Hanyoyi huɗu da za ku kare 'ya'yanku daga masu cin zarafi

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
Batun cin zarafin yara ƙanana na daga cikin abubuwan da ke damun al'ummomi da dama na duniya musamman a nahiyar Afrika.
Gwamnatoci da dama sun sha yunƙurin yin dokoki domin kawar da wannan ɗabi'a, da an ɗauko magana tiryan-tiryan, daga baya sai a rasa inda aka kwana.
Cin zarafi da fyaɗe da musguna wa yara su ne abubuwan da aka fi sani waɗanda shekara da shekaru ake yi wa yara, sai dai a yanzu miyagun da ke irin waɗannan abubuwa sun ƙaro sabon wulaƙanci inda suke garkuwa da yara su kuma kashe su.
Duk wanda aka kama da wannan laifi idan ƴan jarida ko kuma jami'an tsaro suna masa tambaya, abu na farko da yake fara cewa shi ne sharrin shaiɗan, sai dai jama'a da dama na ganin cewa akwai sakaci daga wajen gwamnati a wani lokaci kuma daga wurin iyaye.
An fi ganin sakacin gwamnati ne ta ɓangaren rashin hukunci a zahiri ga waɗanda ake kamawa da irin wannan laifi, inda a wasu lokuta za a kama mutum da laifin aikata ɗanyen aiki kuma ya amsa laifinsa, amma bayan ƴan shekaru kaɗan sai a ji an sake shi.
Wasu daga cikin iyaye suna iya bakin ƙoƙarinsu domin killace ƴaƴansu da tarbiyantar da su da kuma sa ido a kansu domin kare su daga mugayen mutane, amma duk da haka wasu mugayen sai sun samu nasarar yin galba a kan yaran.
Shi ya sa ma Bahaushe ya ce idan kana da kyau, to ka ƙara da wanka, ma'ana duk ƙoƙarin da iyaye suke yi a yanzu, akwai buƙatar su ƙara wannan ƙoƙari ganin cewa irin waɗannan miyagu a kullum suna da sabbin dabarun da suke fitowa da su na cutar da yara.
Babban misali na baya-bayan nan shi ne yadda wani malamin makaranta ya yi garkuwa da wata yarinya yar shekara biyar a Kano ya saka mata maganin ɓera ya daddatsa ta ya saka ta a cikin buhu ya binne.

Asalin hoton, FAMILY
Wannan lamari ya tayar da hankalin kusan duk wani mai imani da tausayi sakamakon yadda abin ya yi muni.
Irin wannan lamari ba shi bane na farko sakamakon an sha kawo rahotanni na cin zarafin yara inda ko a kwanakin baya sai da aka samu rahoton yi wa wata jaririya fyaɗe.
Waɗannan mugayen abubuwa suna faruwa a kusan kullum, sai dai ba kowane lokaci bane ake bayar da rahoton faruwarsu sakamakon a wani lokaci iyayen yaran suna gudun tsangwama da sauran abubuwan da ka iya biyo baya.
Dangane da wannan lamari, BBC ta tuntuɓi Dakta Muhammad Hadi Musa, wanda malami ne a tsangayar nazarin laifuka a Jami'ar Open University ta Najeriya kuma ya bayar da shawarwari huɗu muhimmai ga iyaye waɗanda a ganinsa idan aka bi su, za a gudu tare a tsira tare.
Kowane namiji zai iya zama barazana

Dakta Muhammad Hadi Musa ya bayyana cewa ya kamata iyaye su sani ko wane namiji zai iya zama barazana ga yaransu ko da kuwa kawunsu ne, ƙanin uwa ko ƙanin uba.
"Malamin makarantar islamiyya, malamin makarantar allo, malamamin makarantar boko zai iya lalata da ƴarsu, su rinƙa yi wa wannan namijin wannan kallon, wannan shi ne matakin farko wanda zai taimaka musu wurin yi wa ƴayansu katanga.
"Idan ba su kalle shi da wannan zai iya yi ɗin ba, to za su yi sakacin da za ta iya zuwa ta faru ko da ko da kuwa yarinya wanta ne ma domin an sha samun cewa yaya ya yi lalata da ƙanwarsa," in ji Dakta Muhammad
Iyaye su rinƙa tuhuma idan soyayya da ƙauna ta yi yawa
Dakta Muhammad ya bayyana cewa akwai buƙatar iyaye su rinƙa bincike ko tuhuma a duk lokacin da suka ga wani kusanci ko kuma soyayya ta yi yawa tsakanin malami ko wani majiɓincin lamari ko daga aboki ko daga ƙawa, ko daga amarya a makwafta ko wani babban mutum a makwafta.
Dakta Muhammad ya shaida wa BBC cewa akwai wani bincike da suka yi a kwanakin baya inda suka gano yadda wani shugaban makaranta ya rinƙa lalata da wani yaro na makarantarsa ta firamare a Kano wanda har shugaban makarantar ya saya masa waya da agogo.
Ya ce ko da mahaifin yaron ya ga haka sai ya tuntuɓi shugaban makarantar domin jin dalilin da ya sa ya saya wa yaron agogo sai ya ce don yaron yana da ƙoƙari ne amma mahaifin yaron ya san ƙoƙarin ɗansa bai kai har ya rinƙa zuwa na ɗaya a makaranta ba.
Dakta Muhammad ya bayyana cewa ya kamata a kowane lokaci a rinƙa lura da irin wannan soyayya domin gano gaskiyar lamari.
Sakacin ba yara cikakken ƴanci

Dakta Muhammad ya bayyana cewa iyaye sukan ba ƴaƴansu cikakken ƴanci ko su bar su hakanan sakaka inda ya bayar da misalin cewa "mahaifiya za ta iya aiken ƴarta mai shekara takwas ko goma daga Hotoro zuwa Galadanci ko kuma daga Kurna zuwa Rijiyar Zaki ta hau Adaidaita Sahu ta je ta biya mata buƙatunta ta dawo", in ji shi.
"Duk mai yin haka ta san cewa ta sa ƴarta ko ɗanta a cikin target, duk abin da ya faru kada ta yi kuka da kowa kar ta yi kuka da har wanda ya sace mata ɗa ko wanda ya yi mata lalata da ƴa ta yi kuka da kanta," in ji Dakta Muhammad.
Ya kuma yi kira ga mahaifin da bai tsaya ya sa ido ga uwar ƴayansa ba kan irin abubuwan da ke faruwa saboda hidimar neman abin duniya da kada ya kuka da jami'an tsaro ko wanda ya ci zarafin ƴarsa inda ya ce ya kuka da kansa.
Wayar da kan yara
Dakta Muhammad ya bayyana cewa akwai buƙatar iyaye su taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan ƴayansu domin gudun faruwar waɗannan munanan lamura.
Ya bayyana cewa jama'a kan saki jiki ba tare da ɗaukar mataki ba sai wani abin ƙi ya faru tukuna sai a tashi tsaye a yi ta magana a kai.
Ya bayyana cewa wayar da kan yara da gargaɗinsu da tsoratar da su yana taimakawa matuƙa
Ya bayyana cewa yana da kyau a rinƙa kiran yaro ko yarinya ana faɗa musu da cewa "Idan ka ga mutum zai baka alawa kada ka karɓa ka gudu, idan baka san mutum ba ya kiraka kan babur ko Adaidaita Sahu ka gudu ko ka tafi inda manya suke ka tsaya a kusa da su.
"Idan wani ya zo zai riƙe maki hannu kada ki yarda za ki yi ciki, idan kika yi ciki yanka ki za a yi mutuwa za ki yi, kin ga yadda ake yanka rago? ana riƙe maki hannu ciki za ki yi," in ji shi.
Ya ce ya kamata a rinƙa irin wannan tsoratarwa ga yara domin yana taimakawa sosai. Ya ce kuma akwai buƙatar yara su san al'aurar su da sauran sassan jikinsu inda ya ce shi ma hakan yana da matuƙar muhimmanci.











