Zambar intanet: 'Da na sani ban bai wa saurayin da na haɗu da shi a intanet fan 300,000 ba'

Someone using a dating app

Asalin hoton, Getty Images

An sauya ainihin sunayen mutanen da lamarin ya shafa domin karesu daga fuskantar tsangwama.

A watan Mayu 2019, Sophia ta fara magana da Aaron a dandalin soyayya.

Tana neman wanda za su yi aure. Aaron ya ce shi ma haka. Sun ci gaba da magana, kuma abubuwa sun fara tafiya da sauri.

Sophia ba ta yi tsammanin za ta gano cewa daga baya za a bar ta ba tare da abokin tarayya ba da kuma bashin fam 300,000m bayan ta ba da kuɗi ga mutumin da ta hadu da shi.

Ta yi magana da sashen BBC na Asiya, kuma ta ce ta kasance wadda aka "damfara ta hanyar soyaya", kuma tana son shafukan soyayya su dauki mataki domin kaucewa faruwar hakan nan gaba.

'Takardun mallakar gida na bogi '

Sophia da mutumin da ta yi tunanin abokin zamanta ne, sun fara magana game da sayen gida tare - ba tare da haduwa ba .

Da ta waiwayi baya, Sophia ta ji an gaya mata "karya da yawa" game da makomarsu da saurayin nata.

Ta ce ya ƙirƙiri takardun jinginar kuɗi na ƙarya da saƙon imel da lauyoyi.

Sophia ta aika wa Aaron makudan kudade da ya nema a wani bangare na shirinsu na sayen gida nan gaba.

"Na ciyo bashin dubbai a matsayin lamuni da duk abin da na ajiye, wanda ya kai kusan £50,000-60,000.

"Sai na karbi bashi mai yawa daga 'yan uwa da abokai."

Gaba ɗaya, Sophia ta ce ta aika masa da kusan fam 300,000.

Someone entering bank details

Asalin hoton, Getty Images

Ba ita kaɗai ba ce ta faɗi tarkon zambar soyayya ba. A cewar ma'aikatar Kudi ta Burtaniya, an sami karuwar masu aikata zamba da kashi ashirin cikin dari da ke da alaƙa da zambar soyaya tsakanin 2019 da 2020.

Lokacin da ya nemi ƙarin fam 50,000, Sophia ta yanke shawarar cewa lokaci ya yi da zai fara amsa tambayoyi.

Ta kira bankinta, inda ta yi ittifakin cewa tana da asusun ajiya da Aaron. Suka gaya mata cewa ba sunanta a asusunta.

"Na ji kamar ƙasa ta buɗe a ƙarƙashina. Abin ya ba ni mamaki . Na ji kamar ina cikin mummunan mafarki," in ji ta.

"Kana ganin labarai, kana karanta labarai, kana jin labarin wasu, amma kana jin hakan ba zai taɓa faruwa da kai ba.

"Amma hakan ya faru, saboda kana cikin wani yanayi na damuwa da ba ka ma san kana cikinsa ba ."

Ajiye waya ki kira 'yan sanda'

Sophia ta fara bincikar abokin zamanta, domin ta gano ko yana aiki a inda ya ce ya yi.

"Sun ce babu wani mai wannan sunan da ke aiki a nan.

"A zahiri mutumin da ke aiki a Barclays ne ya ce, 'kina buƙatar ajiye wayar kuma ki kira 'yan sanda nan ta ke'."

Kuma ta yi hakan. 'Yan sandan Thames Valley sun shaida wa BBC cewa suna gudanar da bincike a kan zargin damfarar ta soyayya, wanda aka gabatar wa 'yan sanda a watan Janairun 2020.

Kawo yanzu dai ba a kama wani mutum ba, amma ana ci gaba da gudanar da bincike. 'Yan sandan ba su tabbatar ko musanta sunayen wadanda ake zargi ko wadanda lamarin ya shafa ba.

Shekaru biyu bayan haka, Sophia ta ji cewa tana cikin matsayi mafi kyau.

Wani binciken baya-bayan nan da jami'in kula da harkokin kudi suka yi ya yanke hukuncin da ya goyi bayanta.

Wannan yana nufin a ƙarƙashin wani tsari da ake kira Model Reimbursement Model [CRM] Sophia ta kasance wadda aka damfara, don haka ya kamata bankuna su ba ta kuɗinta bisa doka.