Gashaka Gumti: Abin da ba ku sani ba game da Gandun daji mafi girma a Najeriya

Gashaka Gumti
    • Marubuci, Salihu Adamu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Yau ce Ranar Gandun Daji ta Duniya, kuma hakan ne ya sa za mu sake wallafa wannan labari da muka taba wallafawa a baya saboda muhimmancin ranar:

Katafaren gandun daji na Gashaka Gumti da ke jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya ya samu ne a shekarar 1991 bayan hade manyan gandun daji biyu na 'Gashaka Game Reserve' da ke Taraba da kuma 'Gumti' da ke Adamawa.

Dajin ya kasance mafi girma a Najeriya da kuma wasu kasashen nahiyar Afirka kasancewar ya ratsa Najeriya da Kamaru ta jihohin Adamawa da Taraba, sannan ya kasance gandun daji mafi ƙayatarwa a kasar a cewar Adegoke Babatola jami'in cibiyar samar da bayanai ta gandun dajin.

An assasa gandun ne domin kare martabar dabbobi da koguna da kuma muhalli da ke yankin.

Gandun Dajin Gashaka Gumti na da fadi da kuma tsawon murabba'in kilomita 6731 kuma daji ne mai duhun gaske da ke dauke da dabbobi da tsirrai da ciyayi da bishiyoyi daban-daban.

Dabbobi da tsuntsaye da ake samu a Gashaka Gumti

Gandun dajin Gashaka Gumti na kunshe da dabbobi iri-iri da tsuntsaye kala-kala da ake samun jinsin su a kasashen nahiyar Afirka da kuma Turai.

An kiyasta cewa akwai jinsin tsuntsaye akalla 400 kuma gandun ya kasance wuri mai matukar muhimmanci ga tsuntsaye da ake kira Important Bird Area a turance.

A bangaren dabbobi masu kafa hudu kuwa akwai zakuna da giwaye da damisa da kuraye da karkanda da bauna da dorinan ruwa da dai sauransu.

Sannan akwai kananan birrai da gwaggwon biri da gada da kuma barewa.

Akwai jinsin gwaggon biri da ake samu a kasashen Najeriya da kamaru kawai a duk duniya kuma irin wannan gwaggwon na nan a dajin na Gashaka Gumti.

Baya ga irin wadannan manyan dabbobi akwai kanana dangin kadangaru da guza da kada da kulba da kuma sauransu, sannan akwai jinsin macizai daban-daban ciki har da mesa da kububuwa da Gamasheka da sauransu.

Gashaka Gumti

Yadda Turawa ke zuwa yawon Bude Ido da bincike a Gashaka Gumti

Gandun daji na Gashaka Gumti ya na kunshe da kebabbun wurare na musamman da babu abunda ya taba kutsawa cikinsu kuma ana zagayawa da masu zuwa yawon bude ido daga kasashe daban-daban na duniya domin kashe kwarkwatan idanunsu.

A cikin dajin ne ake da wuri da yafi ko ina tudu a Najeriya wanda ake kira "Chabbal Waade" wato Tsaunin mutuwa kenan da harshen Fulfulde.

Tsaunin ya kasance yana da tsawon murabba'in mita 2419 kuma yanada farin jini sosai ga masu zuwa yawon bude ido inda suke tururuwa domin daukar hotuna da bidiyo.

Masu yawon bude ido daga kasashen Turai da kuma sauran kasashen turawa kamar Ingila da Amurka da Sifaniya da sauransu na lekawa Gashaka Gumti.

Sannan akwai masu zuwa daga kasashe kamar New Zealand da Jamus da Sweden da Canada da Faransa da Poland da sauran manyan kasashen duniya.

A nahiyar Afirka kuwa gandun dajin yana samun baki daga kusan dukkan kasashe da ke nahiyar musamman kasashen Kenya da Afirka ta Kudu da Tanzania da jamhuriyar Afirka ta tsakiya da sauransu.

Adegoke Babatola jami'in cibiyar samar da bayanai ta gandun dajin ya ce annobar korona ta shafi gandun dajin a yanzu saboda masu zuwa yawon bude ido daga kasashen ketare sun dakata.

Daga cikin gida Najeriya kuwa ana samun baki daga ko wace jiha kuma suna zuwa yawon bude ido da bincike musamman dalibai daga jami'o'in kasar.

Mr. Babatola yace Turawa na zuwa bincike da nazarce-nazarce kan dabbobi da tsuntsaye iri-iri da ke kunshe a gandun dajin domin karantarwa da kuma tarihi.

Ya kara da cewa akwai jinsin gwaggwan biri da ake samu a gandun dajin kadai a duk duniya kuma Turawan suna sha'awar samun bayanai kan irin wadannan dabbobi da sai a nan kadai ake samun su.

A cewarsa hakan na taimaka musu wajen sanin kyauta da Allah yayi wa Najeriya da kuma Afirka.

Gashaka Gumti

Rawar da dajin ke takawa wajen hana gurgusowar hamada da sauyin yanayi

Kasancewar Gashaka Gumti gandun daji mafi girma a Najeriya, dajin na taka muhimmiyar rawa wajen hana gurgosowar hamada ta hanyar bishiyoyi da ke cikinsa a cewar Mr. Babatola.

Jami'in gandun dajin ya ce da an bar shi kara zube da tuni hamada ta shafi sassan Najeriya domin kuwa da an kusa karar da dukkan bishiyoyi da ke dajin wadanda ke taimakawa muhalli musamman a wannan lokaci da ake safarar dogin bishiyoyi zuwa wasu kasashe domin kere-kere.

Mr Babatola ya ce hakki ne da ya rataya akan jami'an gandun dajin su kare shi daga masu kutse domin lalata shi da kuma farautar dabbobi da ke cikinsa.

Ya kara da cewa anayin hakane domin kare shi da kuma baiwa al'ummar da zata rayu nan gaba a doron kasa damar amfana da dajin.

Koguna da ake samu daga dajin Gumti na gangarawa har zuwa babban kogin Binuwai wanda ya zama jigo wajen samarwa al'umma da dama ruwan sha da kuma sana'o'i kamar kamun kifi da noma da kiwo da sauransu.

Barazanar da Gashaka Gumti ke fuskanta

Gashaka Gumti
Bayanan hoto, Salihu Adamu na BBC a Gandun Dajin Gashaka Gumti

Duk da tarin albarkatu da ke kunshe cikin katafaren gandun dajin na Gashska Gumti, akwai kuma barazana da dajin ke fuskanta.

Jami'in cibiyar samar da bayanai ta gandun dajin Adegoke Babatola ya ce masu kona daji ba gaira ba dalili na cutar da shi ta hanyar cinna wuta wacce ke kashe dabbobi da bishiyoyi.

Bayaga kona daji akwai kuma matsalar masu farauta da kiwo.

Mafarauta na sulalewa su kashe dabbobi dake dajin sannan su kai kasuwa domin saidawa da kuma magani.

Su kuwa makiyaya na kutsawa cikin dajin domin kiwo kuma hakan na kashe tsirrai da bishiyoyi da ake da su.

Har ila yau, Babatola ya ce akwai barazana daga zaizayar kasa da ta kunno kai cikin dajin bayaga dotti da mutane ke zubarwa sannan ruwa ya kwaso ya shigar cikin dajin musamman ledoji da ke makalewa dabbobi idan sun ci su.

Sharhi

Katafaren gandun dajin Gashaka Gumti wuri ne da ke da matukar kayatarwa domin akwai tarin halittun Allah cikinsa.

Wuri ne da ke cikin karamar hukumar Gashaka wacce ke kan hanyar zuwa tsaunin Mambila.

Da zarar mutum ya dumfari mashigar dajin zai ji yanayi ya sauya daga matsakaicin zafi zuwa sanyi sannan zaiji kukan tsuntsaye da dama.

Za kuma a hangi duhun daji mai ban sha'awa da kamshin furanni na tsirrai bila adadin.