Covid vaccine: Camfe-camfen alaƙanta riga-kafin cutar korona da hana haihuwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Rachel Schraer
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Har yanzu ƙarairayin da ake yaɗawa a shafukan intanet cewa allurar riga-kafin cutar korona na haddasa ɓari ko rashin haihuwa, duk kuwa da shaidun da aka bayar.
Likitoci sun yi tsananin taka-tsantsan game da abubuwan da za su amince da su a lokacin juna biyu, don haka shawarar farko ita ce a kauce wa yin allurar riga-kafi.
Amma a yanzu, an samu cikakkun bayanan kariya cewa wannan shawara ta sauya, kana yanzu ana ƙarfafa gwuiwa kan amincewa da wannan allurar riga-kafi (a yayin da kamuwa da ita kanta ƙwayar cutar ta korona na mummunar barazana ga ɗaukar ciki).
Mun duba wasu daga cikin camfe-camfen da aka fi yaɗawa - da kuma dalilan da suka nuna cewa ba gaskiya ba ne.
Wani bincike ya nuna batun da ake cewa allurar riga-kafin na taruwa a cikin jakar ƙwayayen mahaifa - Ba gaskiya bane
Wadannan bayanai sun samo asali ne daga kuskuren karanta binciken da wata hukuma mai lura da al'amura ta ƙasar Japan ya gudanar ne.
Binciken ya ƙunshi ɗura wa ɓeraye allurar riga-kafin mai yawa - adadin riga-kafin da ya fi wanda ake bai wa mutane wato yawan da ya ninka har sau 1,333.
Kashi 0.1% bisa 100 kacal na adadin ruwan riga-kafin ne ya kasance a cikin jakunkunan ƙwayayen mahaifar ɓerayen, sa'a 48 bayan yi musu allurar.
Har ila yau - kashi hamsin da uku bisa dari (53%) bayan sa'a daya kana kashi 25 bisa dari bayan sa'oi 48 - aka gano a wuraren (da aka yi wa mutane allurar akasari a kafadunsu).
Daya wurin da aka fi samu shi ne hanta - kashi sha shida bisa dari (16%) bayan sa'o'i 48, wannda zai taimaka wajen tace duk wani datti daga cikin jini.
An samar da ruwan allurar riga-kafin ta hanyar amfani da kumfar mai da ke ƙunshe da abubuwan ƙwayoyin halittar ƙwayar cutar, wanda ke zaburar da garkuwar jiki.
Kana wadanda ke wannan shaci-fadi game da wannan, a gaskiyar magana tattaruwar wannan kumfar maiƙon ce da aka gano a cikin jakunkunan ƙwayayen mahaifar.
Adadin yawan maiƙon a cikin jakunkunan ƙwayoyin mahaifar sun ƙaru a cikin sa'o'i 48 bayan yin allurar, a yayin da abubuwan da ke ƙunshe cikin ruwan riga-kafin ke kan zagayawa daga da wurin da aka yi allurar zuwa fadin jiki.
Amma abu mafi muhimmanci shi ne babu wata shaida da har yanzu ke nuna cewa suna kunshe da abubuwan kwayoyin halittar kwayar cutar.
An kuma yi wallafe-wallafen da ke ikirarin cewa an ''kwarmata'' binciken ne, duk kuwa da a zahiri an wallafa shi ne don jama'a a shafin intanet.

Wasu labaran da za ku so

Bayanan da aka tattara da suka nuna cewa riga-kafin na haddasa wa masu ciki yin ɓari- Ba gaskiya bane
Wasu wallafe-wallafen sun nuna rahoton yawan ɓarin da ake dangantawa da tsare-tsaren bayar da riga-kafin da suka haɗa da magunguna, da tsarin Yellow Card na Hukumar Lura da Magunguna da Kayyakin Kiwon Lafiya (MHRA) a Birtaniya, da kuma Shirin Samar da Bayanai Kan Tasirin Ruwan Rigakafi (VAERS) a Amurka.
Kowa zai iya bayar da rahoton wasu alamu ko rashin lafiya da suka fuskanta bayan da aka yi musu allurar riga-kafin. Ba kowa ne kuma zai zaɓi rahoton ba, don haka zaɓaɓɓun bayanai ne da aka tattara.
Amma tabbas akwai batun yin bari da aka bayar da rahoto a cikin kundin tattara bayanan - kuma abin takaici shine aka fi bayar da rahoto a kai - amma hakan ba yana nufin cewa allurar rigakafin ce ta haddasa ba.
Wani bincike ya gano bayanan da ke nuna cewa adadin masu yin barin a cikin matan da aka yi wa riga-kafin ya yi daidai ne da adadin da aka yi tsammani a cikin - kashi sha biyu da rabi bisa dari (12.5%) na adadin yawan al'umma.
Dakta Victoria Male, wata ƙwararriya a fannin garkuwar jiki da kuma abubuwan da suka shafi haihuwa a Kwalejin Imperial da ke birnin London, ta ce waɗannan tsare-tsare na bayar da rahotanni na da matuƙar amfani wajen gano sakamako masu illa daga riga-kafin da akasari ba a ciki samu daga yawancin al'umma ba.
Ta hakan ne aka danganta matsalar daskarewar jini da aka samu jefi-jefi da nau'in ruwan riga-kafi na
Da zarar ka fara ganin wasu alamu da ba a saba gani ba daga mutanen da aka yi wa allurar riga-kafin, za ka alamun jan rubutu na gargadi.
Ba su da sahihanci sosai wajen lura da alamu ko sakamako masu illa da aka saba gani a tsakanin al'umma ba - kamar sauyi a jinin al'ada, ko ɓari, ko kuma matsaloli na zafi.
Ganinsu a cikin kudin tattara bayanai ba yana nufin nuna alamun gargadi ba saboda ka saba gainsu, walau da da allurar riga-kafi ko babu.
Har sai mun fara samun karin masu yin bari fiye da yadda aka saba gani a tsakanin mutanen da ba a yi wa riga-kafin ba ne wannan kundin tattara bayanai zai zabura wajen gudanar da bincike - amma a yanzu babu wannan.
Har ila yau wasu mutane sun yi ta yada wasu taswirori da ken una matukar karuwar yawan adadin mutanen da ke bayar da rahoton matsalolin da suka fuskanta ga wadannan tsare-tsare idan aka kwatanta da na shekarun baya, na wasu allurorin riga-kafin da magunguna.
An yi amfani da wannan wajen nuna cewa ruwan rigakafin korona yana da hadari kadan.
Amma karuwar ba ta nuna mana hakan ba, abinda ta unua shi ne cewa an yi wa adadin mutane masu yawa allurar riga-kafin.

Ruwan riga-kafin zai iya yi wa mahaifa - Babu wata shaida
A wasu ƙorafe-ƙorafe da Michael Yeadon, wani mai binciken kimiyya wanda ya wallafa bayananan shaci-fadi kan cutar korona ya yaɗa, ya yi ikirarin cewa wasu sinadaran protein da aka zuba a cikin ruwan riga-kafin korona na kamfanonin hada magunguna na Pfizer da Moderna na da yanayi iri daya da na sinadarin protein da ake kira syncytin-1.
Ya yada jita-jitar cewa wannan ka iya sa garkuwar jikin da ke kai wa ƙwayar cutar farmaki har ila yau ta kai wa dan tayin da ke ciki hari.
Wasu ƙwararru sun yi amanna cewa asalin duka wannan hasashe cewa ruwan riga-kafin korona ka iya yin illa wajen ɗaukar ciki ko kuma haihuwa.
Ko shakka babu sinadarin protein nau'in syncytin-1 da na wanda aka sana a cikin ruwan riga-kafin korona suna da kamanni ɗaya kamar sauran nau'ukan sinadaran protein - idan jikin mutum na da saurin rikicewa, zai iya jurewa kai wa kan sa da kan sa hari a koda yaushe ya kamu da ƙwayar cuta da kuma garkuwar jikin.
Amma a yanzu an tattara shaidun da za su taimaka wajen ƙin amincewa da waɗannan bayanai.
Wani ƙwararre a fannin ɗaukar ciki a Amurka Dakta Randy Morris, wanda yake son ya mayar da martani kai tsaye game da abubuwan damuwar da ya ji.
Ya fara sa ido kan marasa lafiyar da ke karkashin kulawarsa da ake yi wa aikin neman haihuwa don ganin ko allurar riga-kafin ta haifar da wani sauyi a bangaren damar da suke da it ana samun nasarar daukar ciki.

Ƙarin labarai masu alaƙa

Cikin mata 143 da ke cikin Binciken Dakta Morris, wadanda aka yi wa rigakafo, da wadanda ba a yi wa ba, da kuma wadanda suka kamu da ƙwayar cutar na kusan daidai-wa-daida a irin damar samun nasarar dashen ɗan tayi da kuma yadda juna biyun zai cigaba da girma.
Binciken gajartacce ne, amma an ƙaru da shi a cikin saura tarin sauran shaidun - kuma suna tabbatar da gaskiya.
Dakta Morris ya yi nuni da cewa mutanen da suke cusa tsoro a tsakanin al'umma ba su bayyana dalilan da suka saka suka yi amanna garkuwar jikin da ke kai farmaki saboda ruwan riga-kafin ka iya yin illa ga damar daukar ciki, amma irin wannan garkuwar jiki daga wadanda suka kamu da kwayar cuta ba za su yi hakan ba.
Matsalar ita ce, a yayin da masana kimiyya ke ruguguwar samar da shaida don bai wa mutane tabbaci, a daidai lokacin da za su iya bayar da rahoton sakamakon binciken nasu mutane da ke kan shafin intanet sun riga sun ƙara yin gaba zuwa kan wani abu daban.
Kamar yadda Dakta Morris ya bayyana: "Alamun bayanan shaci-fadi da jita-jita su ne da zarar an nuna rashin amincewa, sai ka kara matsa ƙaimi zuwa gaba.''














