Abin da Musulunci ya tanada kan riga-kafin cutar korona ga mai azumi - - Sheikh Maraya

Bayanan bidiyo, Musulmi da dama na fargabar yin allurar rigakafin cutar korona bisa wasu dalilai

Latsa wannan alamar hoto da ke sama domin kallo da sauraron Sheikh Halliru Maraya

Malaman addinin Musulunci na yin kiraye-kiraye ga Musulmi da su amince a yi musu allurar rigakafin cutar korona ko da kuwa a lokacin da suke yin azumi ne.

Sheikh Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Kaduna ya ce yin allura a jijiya domin neman lafiya da kandagarki ga yaduwar annoba ba ya karya azumi.

Ya kara da jan hankalin Musulmi da ka da su saurari wadanda suke cewa allurar ba ta kamaci dan adam ba, inda ya ja hankalin Musulmi kan irin mutanen da ya kamata a saurara.

"A wannan batu majibinta al'amura su ne likitocin da suke da ilimin kwayoyin cuta saboda su za a saurara.

"Allah Ubangiji a cikin littafinsa mai girma na cewa Ku bi Allah ku bi manzonsa sannan ku bi majibunta al'amuranku."

Bisa dogaro ga wannan aya ne Sheikh Halliru ya ce likitoci a wannan fage su ne ma'abota al'amura ba malamai ba.