Abin da ƴan Najeriya ke cewa kan yawan bashin da ake bin ta

Matsayin Najeriya a jerin ƙasashen da suka fi fama da yawan bashi a duniya ya ja hankalin ƴan ƙasar inda suke ta tsokaci da mahawara musamman a shafukan sada zumunta.
Rahoton da Bankin Duniya ya fitar ya bayyana cewa Najeriya na cikin kasashe 10 da suka zarta sauran kasashe yawan karɓar rance a duniya.
Bankin duniyar ya fitar da wannan bayanin ne a cikin rahoton ƙungiyar da ke kula da ci gaban ƙasashen duniya a ranar Laraba.
Rahoton wanda aka fitar a ranar Litinin, ya ƙunshi jerin kasashe 10 da ke fama da bashi a duniya.
Rahoton ya nuna cewa Najeriya ita ce ƙasa ta biyar a ƙasashen da suka fi fama da bashi, kasancewar ana bin ta kusan dala biliyan 12.
Indiya ce ta sha gaban sauran kasashen da bashin da ake bin ta da ya kai dala biliyan 22, yayin da Bangladesh ta rufa mata baya da ake bi bashin dala biliyn 18 da ɗoriya, sai kuma kuma Pakistan ta zo ta uku da bashin da biliyan 16 da ƴan kai.
Kasar Vietnam ta kasance ta hudu da ake bin bashin dala biliyan 14 da ɗoriya.
Sauran kasashen da ke goman farko daga nahiyar Afirka suke, wadanda suka hada da Habasha wadda ta kasance ta shida da bashin dala biliyan 11 da miliyan 200, da Kenya, wato kasa ta bakwai mai bashin dala biliyan 10 da miliyan 200.
Tanzania ce ta takwas da bashin dala biliyan takwas da miliyan 300, Ghana kuma ta tara bashin dala biliyan biyar da miliyon 600, yayin da Uganda ta kasance ta 10 da bashin dala biliyan huɗu da miliyon 400.
A cewar rahoton, irin wannan yanayi da kasashen suka samu kan su yana iya jefa su cikin haɗari da zai shafi amincinsu a tsakanin masu ba da rance, idan suka gaza cika wani ɓangare na yarjejeniyar da ake ƙullawa da su.
Zuwa yanzu babu wani martani daga ɓangaren mahukuntan Najeriya.
Me ƴan Najeriya ke cewa
Ƴan Najeriya musamman masu bibiyar shafin Facebook na BBC Hausa sun ta yin tsokaci da tafka mahawara game batun yawan bashin da ake bin Najeriya da kuma matsayinta a rahoton Bankin duniya.
Da dama suna ganin kamar yadda duniya ta san da yawan bashin da ke wuyan Najeriya ya kamata a ce "suna gani a ƙasa, wasu kuma na cewa suna ganin ayyukan gwamnati."





Wasu na ganin ci gaba da ba waɗannan ƙasashe rance da bashi ya yi wa katutu zai iya zama kasada, idan aka yi la'akari da irin halin da suke ciki ta fuskar biyan bashin.
Amma a lokuta da dama hukumomin Najeriya sun sha bayyana cewa bashin da ake bin kasar ba shi da wani haɗari, saboda ana kashe shi ne a kan abubuwan da za su bunkasa tatattalin arziki, tare da samar da abin biyan bashin.
Ita ma ƙasar Kenya, wadda ta kasance ta bakwai, kamar yadda shugaban kasar, Uhuru Kenyatta ke cewa bashin ba wani abin ta da hankali ba ne, saboda kamar yadda ƴan magana ke cewa: bashi hanji ne yana cikin kowa. Don haka babu wata kasa a duniya da ba ta cin bashi.
Bayan haka gwamnati na iya sauke wajibcinta nahanyar biyar albashin ma`aikata da kuma samar da abubuwan more rayuwa ga al`umma. Sannan uwa-uba, gwamnatinsa ba ta gaza wajen rage bashin da ake bin ta.











