Hirar Buhari da Arise TV: Abu bakwai da shugaban Najeriya ya faɗa kan halin da ƙasar ke ciki

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargaɗi matasan ƙasar da su "gyara halayensu" idan suna son su samu aikin yi.
Buhari ya yi gargaɗin ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise TV da safiyar Alhamis, yana mai cewa "mutum zai iya samun kyakkyawar shaidar digiri amma ya mutu bai samu aikin yi ba".
Ya ce zanga-zangar EndSARS da aka yi a ƙarshen 2020 ta tsorata masu zuba jari a Najeriya yayin da kuma aikin gwamnati yake wuya.
"Ka je wajen duk wani gwamna yanzu ka ce ya ba ka kwangila ko aikin yi, zai ce maka babu," in ji Buhari. "Haka ma ƙananan hukumomi. Saboda haka, za ka iya samun digiri mai kyau amma sai ka mutu ba tare da ka samu aikin yi ba.
"Me ya sa? Saboda babu wanda zai zuba jari a ƙasar da babu zaman lafiya. Saboda haka, na faɗa musu su faɗa wa matasa cewa idan suna son aikin yi su sauya ɗabi'unsu, su tabbata Najeriya ta zauna lafiya domin mutane su zo su zuba jari.
"Ka duba sabbin motocin bas 200 da tsohon gwamnan Legas ya sayo, wasu daga cikin irin waɗannan yaran ne suka ƙona su. Wane ne zai je ya zuba kuɗinsa a wurin da babu zaman lafiya? Babu wanda zai yi haka.
"Saboda haka, abu ne mai sauƙi. Ku kama kanku, ku zauna lafiya, sai mutane su kawo kudinsu."
Sauran abu bakwai da Buhari ya faɗa a hirar

Asalin hoton, ARISETV
Matsalar tsaro
Shugaban ya yi tsokaci kan batun da ya fi addabar kasar wato matsalar tsaro, inda ya ce daga bayanan da yake samu daga hukumomin tsaro akwai kwararan dalilai da ke nuna cewa an samu ci gaba, musamman bayan sauya shugabannin hukumomin.
"A arewa maso yamma, ba shakka mun tura karin sojoji zuwa jihohin da suka fi fama da wannan matsalar, kamar a Zamfara, mun hana hakar ma'adanai, su kansu yan kasashen waje mun hana su yin aiki a wannan waje, sannan ana ci gaba da kokarin ganin an kawo karshen matsalar", in ji shi.
A cewarsa: "Matsalar arewa maso yamma ita ce ta mutanen da ke da al'adu iri daya suna kashe juna. Za mu tafiyar da su ta hanyar da suka fi fahimta. Mun bai wa 'yan sanda da sojoji umarni da kada su raga musu. Idan aka kori mutane daga gonakinsu, za mu shiga cikin yunwa."
Ya kara da cewa "A arewa maso gabashin Najeriya muna samun nasara a kan Boko Haram, kuma alamu na kara bayyana da ke nuna cewa an kusa murkushe su."
Hare-haren makiyaya
Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna damuwa a kan yadda ake ci gaba da samun karuwar hare-haren 'yan bindigar da ake zargin makiyaya ne, inda ya ce dole kowa ya yi mamaki a kan yadda makiyayan da a baya ake ganinsu rike da sanduna a ce su ne a yanzu suke dauke da manyan makamai suna kashe mutane.
Ya ce rungumar shirin da gwamnatinsa ta bullo da shi na samar da matsuguni ga makiyaya zai taimaka wajen kawo karshen matsalar da ake fama da ita.
''A cewarsa, a halin da ake ciki an cinye kusan dukkanin hanyoyin da makiyaya ke amfani da su wajen zirga-zirga daga jihohi zuwa jihohi, don haka shima wannan ya taimaka wajen kara ta'azzara matsalar tsaro.
An kashe kananan hukumomi
Buhari ya ce a halin da ake ciki an kashe kananan hukumomi baki daya, ba su da wani tsari, ba sa iya yin komai a kashin kansu, hatta kudin da ake ba su a halin da ake ciki ba su da ikon sarrafa da su.
''Idan da ana bai wa karmar hukuma Naira miliyan 300 domin ta yi wani aiki, a yanzu ba a ba ta abin da ya kai miliyan 100 ma, wannan fa shi ne halin da kananan hukumomin ke ciki", in ji shi.
Ko da yake bai fadi shirin da gwamnatinsa ke yi na ganin kananan hukumomin sun rabauta da yancin tafiyar da harkokinsu ba, sai dai ya ce idan aka ci gaba da tafiya a haka fatan da ake da shi na ganin an samar da ci gaba tun daga kasa na iya gamuwa da cikas.
Hare-haren IPOB
Batun kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra na IPOB, na cikin abubuwan da suka fi jan hankali a halin da ake ciki a Najeriya, musamman bayan kalaman da shugaban ya yi a baya bayan nan, inda ya ce "za mu yi musu magana da irin yaren da suke ji."
Sai dai shugaban ya sake nanata batun da ya yi, har ma ya kara da cewa "za mu shirya 'yan sanda da sojoji domin su yi musu magana da irin yaren da suke ji."
Akwai bukatar a zuba ido don ganin ko me nanata maganar da shugaban ya yi zai haifar, musamman ganin yadda kasashen duniya suka yi masa rubdugu a kan batun a baya.
Yaushe zai yi sulhu da Twitter?
Da aka tambaye shi kan lokacin da za a kawo karshen haramcin da gwamnatinsa ta yi na amfani da Twitter a kasar, Shugaba Buhari ya ce ba zai ce komai ba a kan batun, ko da yake ya amsa da cewa: "Twitter? Na bar wa kaina sanin hakan." Daga nan ya yi murmushi ya ja bakinsa ya yi gum.
Masu zanga-zangar #EndSARS sun so su cire ni daga mulki
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tsokaci kan masu zanga-zangar #EndSARS wadda ta janyo hankalin kasashen duniya. Ya yi zargin cewa babban burin masu zanga-zangar shi ne su cire shi daga kan mulki.
'Abin da zan mayar da hankali bayan na sauka'
Wata tambaya da aka yi wa shugaba Muhammadu Buhari ita ce ko me zai mayar da hankali a kansa da zarar ya sauka daga kan mulki.
Shugaban ya amsa da cewa: "Kamar yadda ka sani ina da gonata ina da shanuna, don haka zan rika zuwa can wajensu a kullum, sannan zan sama wa kaina abubuwa da yawa da za su dauke hankalina."
Sai dai ya ce kafin nan zai mayar da hankali wajen inganta batutuwa uku da suka shafi tsaro da tattalin arziki da kuma manyan ayyuka.











