Ya kamata mu ci irin abincin ƴan Japan don mu yi tsawon rayuwa?

Sushi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wane sirri ne a abincin 'yan Japan?
    • Marubuci, Daga Veronique Greenwood
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future

Japan ta fi ko wace kasa mutane masu shekara 100 zuwa sama a duniya. Mutum arba'in da takwas cikin ko wane mutum 100,000 a kasar na kai wa shekara 100 kafin su mutu. Babu wata kasa da ake samun irin haka. Wannan na iya zama izina ga mutane a sauran kasashen duniya. Shin me suke da shi da mu ba mu da shi? Ko a abincin da suke ci ne?

A irin haka ne aka samar da nau'in abinci na yankin Mediterranean. Shahararsa a wajen yankin na Mediterranean ya samo asali ne daga masanin abin na Amurka Ancel Keys da yadda yake da mayar da hankali kan mutanen Italiya da shekarunsa suka kai 100, wadanda abincinsu ke da karancin kitsen dabba a shekarun 1970.

A shekarun 1990, wani mai bincike kan abinci, Walter Willett ya ambato yadda al'ummar Japan ke da tsawon rai a wata takarda, sannan mutanen da ke gamuwa da ciwon zuciya a kasar 'yan kalilan ne.

Tun a wancan lokacin, bincike da dama sun duba batun cewa ko tsawon ran nasu na da alaka da abinci. Kuma idan haka ne, wane abinci ne ya kamata mu mayar da hankali don samun tsawon rai irin nasu?

seaweed

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Abincin Japan ya kunshi tsirran cikin ruwa da dai sauransu

Abincin Japan ya kunshi abubuwa da dama, a cewar mai bincike Shu Zhang na cibiyar bincike kan tsufa da kula da tsofaffi.

Haka kuma, wata bita da aka yi kwanan nan kan wasu bincike 39 ta duba alakar da ke tsakanin abincin Japan da ingantacciyar lafiya kuma ta gano cewa akwai abubuwa da dama da aka dade da fahimtar suna gyara lafiya: naman ruwa da kayan lambu da waken suya da shinkafa da miyar daddawa.

Miso soup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Miyar daddawa ta Miso na da amfani a jiki sosai

Babu shakka, cin abinci irin wadannan na da alaka da karancin ciwon zuciya, in ji Zhang amma ba da cutuka kamar ciwon daji ba.

Haka kuma, da alama abincin yana da alaka da tsawon rai.

Tsuyoshi Tsuduki, wani farfesa kan abinci a jami'ar Tohoku, ya ce karancin wani sinadari a nau'in abincin Japan din ne ke janyo tsawon rai.

Da farko, shi da abokan aikinsa sun yi amfani da alkaluman kasar don gano abincin da aka fi ci a Japan a shekarun 1990 da kuma abincin da aka fi ci a Amurka a wadannan shekarun.

An sa abincin a na'urar firiza sannan aka ciyar da beraye shi tsawo mako uku, sannan masu bincike suka sa ido kan lafiyarsu.

A girl eating broccoli

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai wani abun mamaki, berayen da aka rika bai wa abincin Japan din ba su tara kitse a cikinsu da jininsu ba, duk da cewa duka nau'ikan abincin na da yawan sinadarai masu maiko da nama da hatsi adadi guda.

Wannan na nuna cewa inda ake samo sinadaran - nama a maimakon kifi, shinkafa a maimakon alkama, misali - na tasiri kan sakamakon binciken.

Haka kuma, berayen da aka bai wa abincin da aka fi ci a Japan daga shekarar 1975 ba su da hadarin kamuwa da ciwon suga da ciwon hanta fiye da sauran berayen, kuma da kwararrun suka duba hantarsu sun gano kwayoyin halittar da ke hana kitse samuwa a jiki.

Abincin ya kunshi tsirran cikin ruwa da naman ruwa da wake da kayan marmari da daddawa ko makamantanta kuma gaba daya ya kunshi abinci da babu sukari mai yawa.

A man making chicken skewers

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An fi turarawa ko tafasa abinci a Japan

A gwaje-gwajen baya-baya nan, an gano cewa abincin na 1975 ya haifar da tsawon rai a berayen, da rashin mantuwa da karkon jiki a lokacin da suka tsufa.

Tsuduki da abokan aikinsa sun gano cewa abincin na da kyakkyawan tasiri kan lafiyar mutane.

Wani gwaji na kwana 28 kan mutane masu kiba masu cin irin abincin Japan ya nuna cewa sun yi saurin rage kiba kuma sinadarin cholesterol a jikinsu ya ragu.

Mene ne sirrin?

Plate of fish

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Japan, ana dafa abin da sinadarai masu kara dandano

Tsuduki ya ce akwai yiwuwar yadda ake girka abincin ne ke tasiri kan lafiya.

Abinci a Japan ya kunshi nau'ikan abinci daban-daban kuma 'yan kadan-kadan.

An fi turara abinci ko a tafasa sama-sama maimakon a soya. Haka kuma, ana zuba wa abincin kayan kara dandano kadan maimakon a zuba gishiri da sukari da yawa.

Daga karshe, ana iya cewa mai yiwuwa alfanun cin abincin Japan na tattare ne da cin abinci kala-kala da aka dafa ta hanyoyin da suka fi inganta lafiya tare da mayar da hankali kan cin ganyayyaki da wake.