Abin da ya sa Amurka ta kai hare-hare kan ƴan a waren da Iran ke goyon baya a Iraki

Amurka ta ce ta kai hare-haren sama ne kan mayaƙan sa kai da Iran ke goyon baya a kusa da kan iyakar Iraƙi da Syria a matsayin martani kan hare-haren da suka kai kan dakarunta a Iraƙi da jirage marasa matuƙa.

Wani mai magana da yawun fadar Amurka ya ce an kai hare-haren ne kan "wasu cibiyoyin adana makamai" a wasu wurare uku.

Ya ƙara da cewa Shugaba Biden ya bayyana aniyarsa cewa zai kare jami'an Amurka.

Wani ƙawancen sojojin sa kai mai ƙarfi na Iraƙi, Popular Mobilisation Forces (PMF), ya ce kashe mambobinsa huɗu da aka yi ne ya janyo barazanar mayar da martani.

Kusan dakarun Amurka 2,500 ne a Iraki a wani ɓangare na ƙawancen ƙasashen duniya da ke goyon bayan dakarun tsaron ƙasashen a yaƙin da suke yi da ƙungiyar IS da ke da'awar kafa Daular Musulunci.

A ƙalla an kai hare-hare biyar da jirage marasa matuƙa kan cibiyoyin da Amurka da gamayyar ƙawancen ke amfani da su tun a watan Afrilu, a cewar jami'an Amurka.

An kuma harba rokoki sannan an kai wa jerin gwanon motoci hare-haren bama-bamai.

Shin mayaƙan sa kan sun mayar da martani?

An kafa ƙungiyar PMF - wata gamayyar ƙawancen da Iran ke goyon baya a shekarar 2014 ne don yaƙar IS, kuma an haɗe ta da Dakarun Tsaron Iraƙi shekara uku da suka gabata.

Ta kuma ce hare-haren saman sun kashe mayaƙanta huɗu a yayin da suke wani aiki na fatattakar mayaƙan IS daga kutsawa Iraƙi.

Ta ƙara da cewa mayaƙan ba su aikata komai da ke nuna adawa da dakarun ƙasashen waje da ke Iraƙi ba, kuma wuraren da aka kai hare-haren ba wurare ne da ake ajiye makamai ko wani abu makamancinsu ba, ba kamar yadda Amurkan ta faɗa ba.

"Don haka mun yi Allah-wadai da kuma tur kan wannan hari kan dakarunmu... kuma muna sake jaddada cewa muna da damar da za mu mayar da martani kan hare-haren nan."

Mai magana da yawun sojin Iraƙi Manjo Janar Yehia Rasool shi ma ya yi Allah-wadai da hare-haren, inda ya rubuta a Tuwita cewa suna nuna "wata halayya mai muni da ba za a yarda da ita ba kan tsaron Iraƙi."

Ya kuma jaddada matakin Iraki na watsi da shiga tsakanin rikicin wasu, ya kuma yi kira ga kwantar da hankali da gujewa dagulewar lamura ta kowane fanni".

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh, ya ce Amurka na "lalata harkokin tsaro" a Gabas Ta Tsakiya, kuma ya kamata ta guji ɗaukar matakan son rai, da jawo tashin hankali, da jawo ƙarin matsaloli a yankin."

Kafar yaɗa labaran gwamnatin Syria ta ruwaito cewa an kashe wani yaro a wani hari a kusa da garin Albu Kamal a kan iyakar Syria ranar Litinin, inda ta zargi Amurka da son daƙile ƙoƙarinta na ƙarfafa zaman lafiya mai ɗorawa a yankin.

Gwamnatin Syria ta dogara sosai kan goyon bayan da Rundunar Tsaro Ta Musamman ta Iran da kuma mayaƙan sa kai na Shia a lokacin yaƙin basasar ƙasar, kuma suna da tasiri sosai a yankin iyakar ƙasar.

Ƙungiyar da ke sa ido kan haƙƙin ɗan adam ta Syria da ke Birtaniya, ta ce mayaƙan sa kai bakwai aka kashe a hare-haren saman a kusa da Albu Kamal.

Ina Amurka ta yi nufin kai harin?

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka John Kirby ya ce "hare-haren saman da aka kai da niyyar kariya" a ranar Litinin da safe, an kai su ne da niyyar "lalata da daƙile" hare-haren jirage marasa matuƙa da aka kai sansanin Amurka a Iraƙi.

Sun kai harin ne kan wasu wurare biyu a Syria da kuma wani ɗaya a Iraƙi da mayaƙan da Iran ke goyon baya ke amfani da su, da suka haɗa da Kataib Hezbollah da Kataib Sayyid al-Shuhada, kamar yadda ya ƙara da cewa.

Kafafen yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa hare-haren saman - zagaye na biyu da aka kai kan mayaƙan da ke samun goyon bayan Iran bisa umarnin Shugaba Biden tun bayan hawansa mulki a Janairu - rundunar sojin saman Amurka ce ta kai su.

"Mun ɗauki matakan ganin an rage barazanar rura wutar lamarin, amma kuma mun aika saƙo," a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken kamar yadda ya shaida wa manema labarai a Rome.