Wane ne silar kashe ƙarfin ƙananan hukumomi a Najeriya?

Gwamnoni jihohi a Najeriya

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto, Masana na ganin gwamnoni na yin yadda suka ga dama da ƙananan hukumomi
    • Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist

Batun ƴancin ƙananan hukumomi na ci gaba da haifar da mahawara a Najeriya.

Duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya ayyana ƙananan hukumomi a matsayin mataki na uku a gwamnatance, amma a yau hakan na neman zama tarihi a kasar saboda zargin da ake yi wa gwamnoni na danne su.

Malam Kabiru Sa'id Sufi, wani masanin kimiyyar siyasa ne a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta CAS da ke Kano, ya ce tsarin tarayya da Najeriya ke bi ya ƙara tabbatar da wannan ƴanci na ƙananan hukumomi.

"Tun daga kundin tsarin mulki na 1979 har zuwa yanzu wato na Jamhuriya ta hudu ya tabbatar da kafuwarsu, wanda a sashe na 7 na kundin ya yi bayani daki-daki a kansu.

"Sashe na 8 da ya dauki alhakin tsara dokoki kan kananan hukumomi ya damka a hannun majalisun dokoki na jihohi, wanda wasu ke ganin hakan ne ya bai wa gwamnoni damar su shiga tsarin su yi abin da suka ga dama kamar yadda muke gani a yau," in ji Malam Sufi.

'Matsalar siyasa da danniya'

Karamar hukuma

Asalin hoton, Getty Images

A ganin Malam Kabiru Sufi matsalar da ta haifar da wannan koma-baya ga kananan hukumomi guda biyu ce - matsalar siyasa da kuma tattalin arziki.

A cewarsa a yanzu an koma ana naɗin kantomomi a matsayin shugabannin kananan hukumomi maimakon gudanar da zaɓe.

Dakta Tukur Abdulkadir na Sashen Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Kaduna, na da irin wannan ra'ayin, inda ya ce an koma bautar da kananan hukumomi a Najeriya domin haka babu dalilin da zai sa su iya yin wani aiki da ba shi gwamnatoci suke so ba.

"Ko a lokacin mulkin soji ana ba mutane dama su zabi waɗanda za su wakilce su a mataki na kananan hukumomi, amma a yanzu da ake dimokuradiyya an hana su wannan damar da kundin tsarin mulki ya ba su," in ji shi Dakta Abdulkadir.

Ya ƙara da cewa ƙananan hukumomin sun kasance mataki na farko da ake samar da ƴan siyasa - a cewar masanin, bincike ya nuna yadda siyasar ƙananan hukumomi ta haifar da manyan shugabannin a siyasar jihohi.

Kamar 20 baya an yi manyan 'yan siyasa kamar Barnabas Bala Bantex wanda ya shugabanci karamar hukuma, daga baya kuma ya zama mataimakin gwamnan jihar Kaduna.

Da irin su Salihu Sagir Takai da Lawal Sama'ila Abdullahi wadanda dukaninsu sun samar da manufofi a matakai daban-daban na rayuwar mutanen da suka wakilta a baya.

A ɓagaren kason kuɗin da gwamnatin tarayya ke bayarwa, masanan sun bayyana cewa hadakar asusu tsakanin gwamnatin jiha da ta kananan hukumomi na daga cikin abin da yake hana kuɗaɗe shiga ga kananan hukumomi domin gudanar da ayyukan ci gaba.

"Kuɗaɗen da shugabannin ƙananan hukumomi suka samu a baya sun samar da manufofi masu kyau na ci gaba ga al'umarsu kamar bangaren lafiya a matakin farko da noma da kiwo da sauran ayyukan ci gaba," in ji Dakta Tukur.

Wannan layi ne

'An kashe ƙananan hukumomi'

BuhariSallau

Asalin hoton, BuhariSallau

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wata hirar talbijin da aka yi da shi ya bayyana cewa "an kashe kananan hukumomi".

Buhari ya ce kananan hukumomi a Najeriya ba su da wani tsari, ba sa iya yin komai a kashin kansu, hatta kudin da ake ba su ba su da ikon sarrafa su.

''Idan da ana bai wa karmar hukuma Naira miliyan 300 domin ta yi wani aiki, a yanzu ba a ba ta abin da ya kai miliyan 100 ma, wannan fa shi ne halin da kananan hukumomin ke ciki", in ji shugaban.

Ko da yake bai fadi shirin da gwamnatinsa ke yi na ganin kananan hukumomin sun rabauta da yancin tafiyar da harkokinsu ba, sai dai ya ce idan aka ci gaba da tafiya a haka fatan da ake da shi na ganin an samar da ci gaba tun daga kasa na iya gamuwa da cikas.

Sai dai Malam Kabiru Sufi ya ce wannan magana ta Shugaba Buhari za ta iya zaburar da kanannan hukumomi su nemi haƙƙinsu wurin jihohi.

Amma Dakta Tukur ya ce maganar shugaban kawai ba za ta wadatar ba, domin yana da ikon da zai iya daukar matakin da ya fi haka.

Ganin cewa mafi yawan gwamnonin ƴan jam'iyyarsa ne zai iya samun goyon bayansu wajen tabbatar da ƴancin kananan hukumomi ta bangaren tabbatar da zaɓe mai inganci da kuma isar da kasafin kudin da ake aike musu.

Wannan layi ne

Yaushe aka fara danne ƙananan hukumomi ?

2007

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPEI

Bayanan hoto, .

Mafi yawan tsofaffin shugabannin kananan hukumomin da BBC ta tattauna da su sun bayyana cewa wannan matsala ta fara ne a 2007 amma a wasu johohi kadan kafin daga bisani ta mamaye kasar baki daya.

Alhaji Tasi'u Muhammad, tsohon shugaban karamar hukumar Katagum ta Jihar Bauchi wanda ya shugabanci Katagum sau biyu a 1990 lokacin SDP da NRC da kuma a tsakanin 1999 zuwa 2003 lokacin PDP da ANPP, ya ce zaɓensu aka yi ba naɗi wanda hakan ya ba su ƙarfin kalubalantar gwamnoni idan sun zo da wasu manufofi da za su iya karya kananan hukumomi.

"A yau rubuta shugabanni ake yi a daki su karbi mulki da sahallewar gwamnoni, ta yaya kake zaton wanda aka naɗa zai iya kalubalantar wanda ya naɗa shi?" in ji shi.

Wani shugaban wata karamar hukuma da bai yarda a bayyana sunansa ba, ya shaida wa BBC cewa kudaden da ake bai wa ƙananan hukumomi daga tarayya ba su isarsu biyan albashi.

Ɓangarorin ƙananan hukumomi ke kashe kudinsu sun kunshi:

  • Lafiya (biyan albashin ma'aikatan lafiya na karamar hukuma)
  • Ilimi (Malaman makaranta da ayyukan gyara makarantu)
  • Tsaro ( kudaden da ake bai wa hukumomin tsaro irinsu Hisba a arewacin Najeriya)
  • Tsafta (kwashe shara da ake yi da kuma tsaftar muhalli a ko wanne karshen wata)
  • Masarauta (hakimai da dagatai da kuma masu unguwanni)
  • Ruwa
  • Fansho
  • Horaswa (horaswar da ake bai wa ma'ikata lokaci zuwa lokaci)
  • Siyasa (harkokin siyasa da ake yi a mataki na kananan hukumomi)
Wannan layi ne

Shin asusun hadaka da jihohi ne matsalar kananan hukumomi?

Shekarau

Asalin hoton, IBRAHIM SHEKARAU/FACEBOOK

Malama Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan jihar Kano, ya musanta cewa asusun hadaka ne ya haifar da wannan matsala.

Ya ce a lokacin da yake shugabantar jiharsa, idan aka aiko da kudaden da gwamnatin tarayya a baya ana bayar da bayanin yadda za a raba kudaden baki daya.

"Idan an aiko da kuɗin akwai takarda da ke dauke da bayanan yadda za a bai wa ko wacce jiha kudadenta, kuma idan aiki za a yi da kudaden wata karamar hukuma sai an tambayi izininta sannan a nemi ta bayar da wani abu domin aiwatar da aikin.

"Babu tilastawa cewa sai an yi amfani da wadannan kudade karfi da yaji," in ji Shekarau.

Ya kuma ce bai kamata a dauki kudaden kananan hukumomi ba a zuba aiki a hedikwatar jiha wadda kawai wasu kalilan ne ke amfana.

"Wani mazaunin kauyen har ya gama rayuwarsa ba zai je inda aka zuba kudaden ba."

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai ne kawai zai iya kawo karshen matsalarsu a Najeriya saboda su ne suka fi kusa da jama'a kuma su suka fi sanin matsalolinsu ta yadda za su magance su.

Sai dai wasu na ganin su ma suna da nasu laifukan wadanda ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, ko da yake sun sha musantawa.

Wannan layi ne