Me tasirin hana gwamnatocin jihohi taba kudaden kananan hukumomi

Asalin hoton, Getty Images
Al'ummar Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na hana gwamnatocin jihohi taba kudaden kananan hukumomi a tsarin da suke bi na asusun hadin-gwiwa.
Hukumar da ke tattara bayanai a kan laifukan da suka shafi kudi da ta`addanci ta kasar ce ta sanar da cewa daga watan Yuni mai zuwa za a hana gwamnatocin jihohi amfani da kudaden kananan hukumomi.
Alhaji Tasi'u Muhammad, tsohon shugaban karamar hukuma ne a jihar Bauchi, kuma a tattaunawarsu da BBC ya ce mataki ne mai kyau domin sun gani a kasa lokacin da yake rike da wannan mukamin a baya.
Ya ce ''har ga Allah lokacin da muke rike da wannan mukamin mun yi taruka daban-daban da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan asusun hadin-guiwa kuma suka nuna cewa yin haka ba daidai ba ne''.
''Ya za a yi mutumin da yake karban kudin da ya kai miliyan 130 zuwa 150 sannan ma'aikanta da zai biya albashi ba su fi miliyan 50 ba, amma sai wata ya zo a ce ya gaggara biyan albashi.''
Mayar da wannan asusun na hadin-gwiwa zuwa gwamnati jihar manyan masu laifuka su ne 'yan majalisar jihohi da kuma gwamnoni domin kowanne gwamna na son a yi hakan domin ya ji dadin abin," in ji Alhahi Tasi'u.
Ya kuma kara da cewa rashin barin kudi a kananan hukumomi shi ne ya sa ofisohin kananan hukumomin suka zama kufai "ban da jakuna da dabobbi da akuya babu wani abin da ake samu."
''Wani ofishin idan ka je duk ya yi yana, wata sakatariyar ma idan ka je rabinta a kone take saboda chairmomin ko kantoma babu abin da suke iya yi.''
Alhaji Tasi'u ya ce su a lokacinsu caki ake ba su na kudinsu, su je babban bakin kasa su karba sannan ka sa kudin a asusun ka na karamar hukuma.
Sai dai ya ce duk yadda za ka kasafta kudin ko yanayin kashe su sai ka rubuta wa gwamna domin neman amincewarsa, karfin iko naira dubu dari biyar kawai ya baka damar kashewa.
''Amma yanzu salon ya sauya babu abin da shugaban karamar hukuma ke iya saye, sai dai ya dauka a aljihunsa kuma wannan dalili ne ya sa ba sa iya zaman ofishi.''

An sha zargin shugabanni wasu kananan hukumomin a matsayin 'yan amshin shata wato dai kamar gwamnoni ne ke nada su, dalilan da suka sa ake ganin ba lallai dokar ta yi tasiri ba a yanzu.
Sai dai Alhaji Tasi'u na da ra'ayi na daban inda yake cewa tana iya tasiri indai za a bi ta.
Ya kuma kara da cewa ya kamata a ce shugabannin kananan hukumomi zabensu ake karkashin tsarin hukumar zabe ta kasa ba wai ta jiha ba.
Shimfida
Hukumar da ke tattara bayanan sirri a kan laifukan da suka shafi kudi da ta`addanci a Najeriya, wato Nigeria Financial Intelligence Unit ko NFIU a takaice ta ce ta yi nazarin yadda ake cirar kudi daga asusun hadin-gwiwa tsakanin gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da yadda ake kashe kudaden.
Hukumar ta ce ta fahimci cewa tsari ne da ke bude kofa ga rashawa da halalta kudin haram, tare da kasancewa babbar barazana ga tsaron kasa a yankunan karkara da kasar baki daya.
Wannan ne ya sa hukumar ta dauki matakin bin didddigi tare da tabbatar da cewa gwamnatoci da bankuna da duk wanda abin ya shafa sun yi aiki da tanadin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi game da asusun hadin-guiwar baki dayansa.
A cewar hukumar, bayan kundin tsarin mulkin ya ba wa gwamnatocin jihohi damar shigar da kudadensu da na kananan hukumomi a cikin asusu guda, dokar ta ce a ba wa kowace majalisar karamar hukuma kudinta ba tare da an kashe mata ko da sisin kwabo a kan wata hidimar da ta ta ba.
Hukumar cikin wata sanarwa wadda jami`inta na yada labarai Ahmed Dikko ya sanya wa hannu ta bayyana cewa lokaci ya yi da za a bi tanadin kundin tsarin mulkin sau da kafa.
Kuma daga watan Yuni mai zuwa za ta sa-kafar-wando-guda da wata hukuma ko kamfanin da ya sa hannu wajen karkatar da kudaden kananan hukumomi zuwa wata hidima ko wani aljihun daban.
Hukumar ta kara da cewa wasu hukumomi takwarorinta a bangarorin duniya da dama suna sa ido a kan yadda wasu ke yi wa dokar cirar kudi da kashewa karan-tsaye a Najeriya.
Lamarin da ke nuna gazawar kasar wajen yaki da masu halalta kudin haram da ba da gudummuwar kudi wajen aikata ta`addanci, wanda aka iya tunzura gangamin kasashen duniya da ke sa ido a kan harkokin kudi daukar mataki a kan Najeriya ta hanyar mai da ita saniyar-ware.
Me dokar ta ce?
NFIU dai ta fito baro-baro tana jan-kunnen bankuna da su guji ba da damar cirar kudaden majalisun kananan hukumomi ba tare da tabbatar da cewa za su shiga hannun kananan hukumomin ba.
Duk bankin da ta kama da saba wa wannan ka`idar, to za ta bata masa suna a gida da wajen Najeriya.
NFIU ta jaddada cewa doka ba ta amince da cire tsabar kudi lakadan na karamar hukuma da ya wuce naira dubu 500 ba a kowace rana, tana karawa da cewa wajibi ne a yi amfani da cak ko tsarin laturoni na tura kudi daga wani asusu zuwa wani.
A Najeriyar dai ana zargin gwamnatocin jihohi da dama da yi wa majalisan kananan hukumomi kisan-mummuke, inda suke amfani da asusun hadin-gwiwa suna yi wa kananan hukumomin kashen-dankali, har ta kai ga babu wata walwala ta a-zo-a-gani a yankunan karkara.
Wannan dai lamarin a bangare guda masana na cewa ya tilasta wa wasu shiga aikata miyagun laifuka, ciki har da matsalar satar mutane da ake yi don karbar kudin fansa, musamman ma a arewacin kasar.










