Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Dr Jabir Sani Maihula
Wani fitaccen malamin Islama a jihar Sokoton Najeriya Sheikh Dr Jabir Sani Maihula ya ce zamansa a Ingila a lokacin da yake karatun digirin-digirgir ya taimaka masa ƙwarai wajen ƙwarewa a harkar amfani da shafukan sada zumunta wajen gabatar da da'awarsa.
Malamin ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a shirinta na Ku San Malamanku.
Ya ce a shekarar 2016 ne ya fara amfani da shafukan sada zumunta wajen yin tafsiri kai tsaye a bidiyo a shafin Facebook.
"Kuma na samu ƙwarewa wajen amfani da intanet ne yayin zamana a Ingila. saboda yawanci ta intanet ɗin ake gudanar da abubuwa a can.
"To na shiga harkar da yawa kuma tana taimaka mana wajen da'awa.
Malam ya ce ko a lokacin kullen taƙaita yaɗuwar annobar cutar korona ya fara wani karatu mai take "Mu Fara Daga Tushe" inda yake yi wa matasa karatu tun daga kan matakan farko na abubuwa masu muhimmanci da suka shafi addini.
Dr Maihula ya ce ya ji dadin zama a Ingila sosai musamman a lokacin karatun digirin-digirgir ɗinsa, musamman ganin yadda ya yi fice ta fannin addini a garin da yake wato Nottingham.
"Na shahara sosai a can don ni kadai na taba karatu a Madina a Nottingham, don haka sai damarmakin al'amuran da'awa suka ƙaru.
"A lokacin zamana a masallacin da ke cikin Jami'ar Nottingham an ba ni limanci. Babban masallaci ne na jami'a a Ingila. A baya kafin na je hayar liman ake amma da na zo sai aka ba ni.
A zaman malam na birnin Nottingham ya yi wani abin a zo a yaba sosai na sasanta saɓanin bambancin shugabancin Musulmai tsakanin masu sassaucin ra'ayi da masu ra'ayin ƴan mazan jiya.
"Yawanci masu ra'ayin ƴan mazan jiya ƴan Saudiyya da Masar da Sudan da Libiya ne. Masu sassaucin ra'ayi kuma su ne kamar ƴan Pakistan da Bangladesh da Indiya da aka haifa a can.
"To su masu ra'ayin ƴan mazan jiyan sai suka roƙe ni na tsaya takara don sun ga ina da irin fahimtarsu to sai daya ɓangaren ma suka karbe ni.
"Na zama shugaban al'ummar Musulmai a wannan yankin, na kan je na yi muhadara kuma ana min tambayoyi sosai, sun ɗauke ni uba," a cewar Sheikh Jabir.
Wane ne Sheikh Jabir Maihula?
An haife shi ranar Juma'a 3 ga watan Yulin shekarar 1981 a garin Sifawa da ke jihar Sokoto.
Ya fara karatun addini wajen mahaifi da mahaifiyarsa a gida na Fiƙihun Malikiyya da Iziyya da Ahalari, sannan ya halarci makarantar addini da ke cikin gidansu inda ya karanci Ƙur'ani da Hadisi.
Ya kuma halarci makarantar soro wajen Malam Ibrahim Auro. Ya yi makarantar firamare a Sokoto sai sakandare ta Kwalejin Fasaha ta Rinjin Sokoto.
Bayan nan sai ya samu gurbin yin digiri A Madina a shekarar 1999, amma sai da ya fara koyon Larabci na tsawon shekara ɗaya. A lokacin shi ne ɗalibi mafi ƙarancin shekaru Najeriya.
Ya fara karatun digiri a fannin Hadisi a shekarar 2000 inda ya gama a 2004. Sai ya zarce da karatun share fagen digiri na biyu wato Post Graduate Diploma a Harkokin Siyasa a Musulunci da Alkalanci duk a Madinan inda ya gama 2005.
Ya koma Najeriya ya yi hidimar ƙasa tsakanin shekarar 2005 zuwa 2006. Ya fara aikin koyarwa a makaranatr koyon shari'a ta Legal a Sokoto.
A 2010 ya samu damar zuwa Birtaniya yin digiri na biyu a Jami'ar East London kan Ilimin Musulunci da na Gabas Ta Tsakiya. Ya koma Najeriya a 2012 inda ya fara aiki a Jami'ar Usman Ɗanfodio a shekarar 2012.
Ya koma Birtaniya a shekarar 2013 don karatun digirin-dirgir a Jami'ar Nottingham. A yanzu haka shi ne shugaban sashen Ilimin Addinin Musulunci a Jami'ar jihar Sokoto.
Yaushe ya fara Da'awa?
Ya fara harkar da'awa tun yana hidimar ƙasa a Abuja a shekarar 2005, yana koyar da mutane karatu da kuma yin wa'azi a Abuja.
A 2006 ya fara koyar da yaran unguwa a Sakwwato. A 2009 kuma ya fara babban majalisi a Sokoton.
"Daga lokacin abu ya kankama na sa ɗambar karatun Sinani Abu Daudu har yanzu ana yi ba a kammala ba," in ji shi.
Malam ya ce duk ranakun Alhamis da Juma'a ana karance karance a gidansa.
Ya zama limamin Juma'a sannan akwai masallatan Juma'a uku a Sokoto da ke ƙarƙashinsa.
Tambayoyi
Malam ya ce masu yi masa tambayoyi sun kasu kashi uku.
Na farko masu fahimta
"Za su yi ta kiranka a waya ko ba ka daga ba za su ci gaba da kira kamar sau biyu ko uku, kuma suna maka uzuri.
"Kai tsaye suke maka tambaya. Mafi yawansu tambaya ce kan wani abu na zamani da ya shafi addini."
Na biyu gama-garin mutane
"Suna iya kiranka a waya sau 30, ba su damu da lokacin da suke kiran ba ko tsakiyar dare ko lokacin salla. Mafi yawa mata ne."
Kashi na uku marasa fahimta
"Da ya kira ka sau biyu ko uku ba ka ɗauka ba sai su fara zagi. Yawancinsu masu neman alfarma ne ta son a yi musu iso wajen wani babban mutum," in ji malam.
Babban abin da ya ƙi jini shi ne ba ya son ana haifar da fada tsakanin malamai.
"Akwai masu kiran malamai su kira ka su yi wata tambaya su naɗi muryarka, sai su aika wa wani malami su ce ga malam wane na soke karatunka.
"An taba hada ni fada da wani malami a irin wannan lamarin, abin ba daɗi.
Malam yana da mata biyu da ƴaƴa biyu.
A fannin abinci ya fi son kaza da tuwon semobita da miyar kubewa.
A baya ya yi wasan ƙwallo har ana ce masa Jabiru Coach. A lokacin a yankinsu babu mai tawagar ƙwallo irin tasa kuma ya buga lamba 7.