Wasika daga Afirka: Yadda sanya hoton 'batsa' a jadawalin 'yan makaranta ya kawo ɓaraka a sabuwar gwamnatin Sudan

Malamai na zanga zanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu malamai sun fito suna nuna rashin amincewarsu da sanya littafin The Creation of Adam a cikin jadawalin karatu a makarantu

A jerin wasiƙunmu daga ƴan jaridar Afrika, wata marubuciya yar Sudan Zeinab Mohammed Salih ta yi waiwaye, wanda masu salon magana ke cewa adon tafiya kan tataɓurzar da ake yi a Sudan, dangane da irin darussan da suka kamata a koyar da yara ɗalibai bayan juyin juya hali.

Short presentational grey line

Bayan kwashe tsawon lokaci ana murna sakamakon hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir, a yanzu an mayar da hankali a kan fatan yin garambawul ga tsarin dimukraɗiyyar ƙasar.

Amma wani rikici a tsakanin manyan malaman addini dangane da sabon tsarin karatu a makarantu na nuna irin haɗarin da gwamnatin riƙon ƙwarya ke fuskanta.

Yayin sallar Juma'a a wani masallaci a babban birnin ƙasar Khartoum a makon da ya gabata, wani limami ya yi ihu cikin tsananin ɓacin rai da murya mai ƙarfi yana faɗin "Allah, Allah, Allah", sannan ya yi kira ga masallata su haɗa kai da gwiwa su yi kukan takaici, a kan yadda aka sanya hoton Michelangelo na Halittar Adam a wani littafin tarihi na rayuwa bayan juyin juya hali.

An bayyana zanen Michelangelo na Halittar Adam a matsayin bidi'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An bayyana zanen Michelangelo na Halittar Adam a matsayin bidi'a

Imam Mohamed al-Amin Isma'il, wanda ya kasance mai goyon bayan Bashir, ya yi imanin cewa hoton ƴan bidi'a ne, wanda za a iya kallo a matsayin na batsa.

Ya kuma caccaki SUNA, wato kamfanin dillacin labarai na gwamnati, saboda ba da wani dandali ga Omer al-Qarray, ɗaya daga cikin mutanen da ke goyon bayan wannan sabon shiri na kawo sauyi a tsarin makarantu, inda ya zarge shi da yaɗa kafirci da aƙidar mulhidanci.

Biyo bayan wannan suka da limamin ya yi, da yawa wasu limamai masu goyon bayan Bashir sun bi sahunsa don fara adawa da sabon tsarin karatun da shi kansa Mr Qarray daga baya danginsa suka ce sun samu saƙonnin barazanar kisa a kai.

Daga baya firaminista Abdalla Hamdok ya hana gabatar da sabon tsarin karatun, sakamakon matsin lamba.

Zeinab
1px transparent line

Mista Qarray, wanda ɗan ƙungiyar ƴan uwa Musulmai ta masu kishin ƙasa ne, ya yi murabus daga aikin tsara manhajar makarantu don nuna fushi da adawa a kan matakin firaministan.

Yana ganin cewa ya watsa masa ƙasa a ido, shi da wasu sauran jam'iyyun siyasa, don saurarar masu tsattsauran ra'ayi da ƙungiyoyin addinin Islama masu goyon bayan Bashir.

Haka kuma an samu saɓani kan yadda za a gabatar da abubuwan da suka shafi tarihin ƙarni na 19 na Sudan.

2px presentational grey line

Yadda juyin juya halin ya gudana:

  • Disamba 2018: Zanga-zangar adawa da farashin burodi da ya tashi bayan da gwamnati ta cire tallafi
  • Fabrairu 2019: Bashir ya ayyana dokar ta ɓaci sannan ya kori majalisar ministoci da gwamnonin yanki a ƙoƙarin kawo karshen zanga-zangar adawa da mulkinsa ta makonni, inda mutane kusan 40 suka mutu
  • Afrilu 2019: Sojoji sun hambarar da Bashir a wani juyin mulki, sun fara tattaunawa da ƴan adawa kan komawa zuwa dimokradiyya
  • Yuni 2019: Jami'an tsaro sun buɗe wuta kan masu zanga-zangar, inda suka kashe akalla 87
  • Satumba 2019: Sabuwar gwamnati ta fara aiki a karkashin Firaminista Abdalla Hamdok a wani ɓangare na yarjejeniyar raba madafun iko na shekaru uku tsakanin sojoji, da wakilan farar hula da kungiyoyin masu zanga-zanga.
2px presentational grey line

Rikici kan abin da al'ummomi na gaba a ƙasar za su koya na daga tarihin abubuwan da suka faru a baya, ya nuna irin jiƙaƙƙiyar da ke akwai tsakanin mutane masu ra'ayoyi daban-daban na siyasa da zamantakewar al'umma waɗanda ke a matsayin tushen siyasa.

Wasu tsoffin ƙungiyoyin ƴan tawaye waɗanda a da suke da alaƙa da gwamnatin Bashir sun yi maraba da matakin firai ministan na dakatar da sabon tsarin karatun.

Misali, Sulieman Sandal, daga ƙungiyar Justice and Equality Movement (Jem), wacce 'ya'yanta ke zaune a kasar Norway, sun goyi bayan Mista Hamdok da Gibril Ibrahim wanda shi ne sabon ministan kuɗi da aka naɗa kwanan nan wanda' ya'yansa ke zaune a Burtaniya kuma duk suna karatun boko.

Kyakkyawan fata game da makomar ƙasar na kan gaba yayin bore a Sudan a cikin 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kyakkyawan fata game da makomar ƙasar na kan gaba yayin bore a Sudan a cikin 2019

An fara gabatar da Shari'a a Sudan a watan Satumbar 1983 lokacin mulkin Shugaba Jaafar Numair. Yana daga cikin dalilan da suka haifar da yaƙin basasa na tsawon lokaci tare da yankin da ke kudancin ƙasar a yanzu kuma yake Kudancin Sudan.

Daga nan aka dakatar da shari'ar Musulunci har tsawon shekaru uku a lokacin zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokiradiyya ta Sadiq el-Mahdi amma an sake farfaɗo da ita lokacin da Bashir ya hau karagar mulki a shekarar 1989 a wani juyin mulkin soja da wata jam'iyyar Islama ta goyi baya.

Tuni dai gwamnatin riƙon ƙwaryar da ta maye gurbin Bashir ta nuna halin ko in kula game da batun na Shari'a da ke da wuyar sha'ani, wanda shi ne asalin rikici da ƴan tawaye a kudancin Kordofan.

Fitacciyar ƙungiyar ƴan tawaye a can, ta SPLM-N, ta buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin da ba ruwanshi da duk wani addini.

A shekarar da ta gabata ta yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiyar da wasu ɓangarori suka amince da ita kuma ta zargi gwamnatin riƙon kwarya da haɗa kai da masu kishin Islama.

Kungiyar ta SPLM-N, wacce ta fi ƙarfi a yankin da kiristoci da dama ke zaune tare da sauran waɗanda ba Musulmi ba, ta yi ƙaurin suna wajen fafutukar ganin an yi wa waɗanda ba a damawa da su adalci.

An dage haramcin giya

Sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya ta ɗauki wasu matakai da suka sawwaƙa musu rayuwa.

Watanni shida kacal da suka gabata, ta yi watsi da dokokin da suka haramta wa waɗanda ba Musulmi ba shan giya, duk da cewa har yanzu an haramtawa Musulman.

Amma a cewar wasu rahotanni, har yanzu ba a daina yi wa mutanen da suka bugu da giya bulala da kuma kame masu siyar da ita ba a wasu wurare a gefen birnin Khartoum.

2px presentational grey line

Wasu labarai da za ku so ku karanta:

2px presentational grey line

Shugabannin SPLM-N sun yi amannar cewa hanya ɗaya tilo da za a tabbatar da ƴancin kowa da kowa musamman waɗanda ba Musulmi ba a Sudan ita ce, ta hanyar samun gwamnatin da ba ta addini ba wacce za ta samar da wani shiri na tattalin arziki da zai tabbatar da an yi adalci wajen rabon arziƙin ƙasa da iko a ƙasar .

Abbakar Ismail, wani marubuci ne kuma ɗan tawaye, ya ce "ta wannan hanya ne kaɗai ba za a cutar da waɗanda ba Musulmi ba''.

Bayanan bidiyo, Wannan mata da aka yi wa laƙabi da 'Kandaka', wanda ke nufin sarauniyar Nubian, ta zama babbar gwarzuwa ga masu zanga-zanga a shekarar 2019

Gwamnatin riƙon ƙwaryar ta ƙunshi ƙawancen ƙungiyoyi, ciki har da janar-janar waɗanda suka taɓa zama makusantan Bashir da wasu ɓangarorin da ke da aƙidar Islama.

Tare da yunƙurin da ake yi a yanzu kan tsarin karatun, gwamnati na nuna cewa ta fi damuwa da samun kyakyawar alaƙa da masu ra'ayin mazan jiya maimakon zama mai nuna ban-bancin ƙasar ta fuskar launin fata, ko addini ko al'ada, matakin da na iya kawo haɗin kai da kawo ƙarshin rikici.

Presentational grey line