Boko Haram: 'Kuskuren da manyan kafofin watsa labaran duniya suka yi kan sace-sacen ɗalibai a Najeriya'

A jerin wasikunmu da marubutan Afirka suke rubutawa, a wannan makon marubuciya 'yar Najeriya Adaobi Tricia Nwaubani ta soki kafofin watsa labaran duniya kan salon da suka bi wajen bayar da rahotanni game da sace ɗalibai a Najeriya - daga sace 'yan matan makarantar Chibok a 2014 zuwa sace yara maza 'yan makarantar Kankara a watan jiya.

Ana iya cewa yadda kafofin watsa labarai suka rika kawo rahotanni bayan da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata 200 daga makarantarsu a Chibok a shekarar 2014, na da manufa mai kyau amma ya haifar da wasu abubuwa marasa dadi.
Kafin sace 'yan matan, shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ba shi da wani kwarjini, illa dai 'yan Najeriya kan ga an nuno shi a talabijin lokaci zuwa lokaci.
A bidiyo daban-daban da yake fitarwa, yakan yi barazana cike da fariya ga kowa - kama daga shugaban Najeriya na wancan lokacin Goodluck Jonathan zuwa shugaban Amurka na wancan lokacin Barack Obama. Da yawanmu kan ce "Wai wannan kazamin mutumin ji yake ya isa da kowa ne?"
Amma bayan sace 'yan matan Chibok, kafofin watsa labarai a fadin duniya sun yi ta nuna duk wani bidiyo da Shekau zai fitar.
Shi kuma abin nema ya samu, sai ya yi ta sakin bidiyo, misali bidiyon 'yan matan da ya sace wadanda ya yi alkawarin sayarwa.

Asalin hoton, AFP
'Yan matan da aka kubuto daga hannunsa sun bayyana yadda Shekau da mutanensa ke farin ciki idan suka ga an yada wani labari dangane da sace 'yan matan.
Yadda aka rika yada labarin Chibok ya kara kambama martabar Shekau a labarai, kuma wannan ya yi masa dadi.
Haka kuma, yadda ake nuna shi ya sauya asalin yadda labarin Chibok yake.
Duk da yadda kafofin yada labarai na kasashen waje suka rika watsa labarin, sace 'yan matan Chibok ba "wani yunkuri na hana karatun 'ya mace ba ne" kawai dai aikin 'yan bindiga ne da ya kwabe.
Bayan kubuto da su daga hannun Boko Haram bayan fiye da shekara biyu a hannunsu, wasu 'yan matan sun bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga makarantarsu ne don kawai su saci kayan abinci.
'Yan bindigar Najeriya sun yi fice a duniya'
Bayan kwashe kayan abincin da ke dakin ajiyar makarantar, sai suka fara gardama kan yadda za su yi da daliban.
Daya daga cikinsu ya bayar da shawarar su sace 'yan matan a dakin kwanansu su cinna wa dakin wuta. Wani kuma ya ce su yi amfani da 'yan matan wajen shiga cikin gari gidan iyayensu don su kara sato kayan abinci.
Daga karshe wani mutum ya kawo shawarar da za ta yi sanadiyyar mummunan labarin da zai karade duniya: "Mu kai su wajen Shekau. Zai san abin da zai yi da su."

Asalin hoton, The Office of First Lady
Wani rahoton kungiyar Human Rights Watch ya bayar da wannan bayanin, bisa hirarraki da aka yi da dalibai 57 da suka tsere a daren da aka yi garkuwa da su ta hanyar dirowa daga motocin a-kori-kura da 'yan kungiyar suka je da su.
Duk da cewa 'yan watanni ne bayan faruwar lamarin aka buga rahoton, ba a mayar da hankali a kansa ba.
Kafofin yada labarai sun kafu a kan bayyana labarin a matsayin na 'yan ta'adda masu adawa da ilimin 'ya mace, don haka sai suka yi watsi da duk wani bayani da ba zai ciyar masu da wannan ajandar gaba ba.
'Yan makonni kafin afkuwar lamarin Chibok, kungiyar Boko Haram ta kai hari wata makaranta a garin Buni Yadi da ke arewa maso gabashin kasar kuma ta bai wa dalibai mata damar tserewa kafin yi wa samari 40 yankan rago a dakunan kwanansu.
Lamarin na Buni Yadi bai dauki hankalin kafofin yada labarai ba sai bayan da aka sace 'yan matan Chibok. Kuma wannan sabon bayanin da aka samu bai sauya yadda suke kawo labaran ba.

A lokuta da yawa, kafofin watsa labarai sun dage kan nuna lamarin Chibok daga mahangar cin zarafin mata, kuma hakan ya bai wa mayakan Boko Haram damar da suke so ta kafa kansu a matsayin wasu gogaggu a idon duniya.
Nan da nan, amfani da mata wajen kunar bakin wake da kungiyar ke yi ya karu ninkin ba ninki bayan sace 'yan matan Chibok, a cewar wani rahoton Cibiyar Yaki da Ta'addanci a 2017 ta jami'ar Yale, wanda ke nuna cewa kungiyar ta ga tasiri yin hakan ne domin kafofin yada labarai su samu kanun labarai masu jan hankali kuma su sanya tsoro a zukatan mutane.
Kungiyar ta zama ta farko a tarihi da ta yi amfani da 'yan kunar-bakin-wake mata fiye da maza, inda ta yi amfani da mata a kalla 80 a shekarar 2017 kawai.
"Duba da yadda aka watsa labarin Chibok, masu tayar da kayar bayan sun fahimci muhimmnacin amfani da mata wajen aika sakonninsu," a cewar Hikary Matfess, wadda ta rubuta rahoton.
'Zakara mai neman suna'
A watan Fabrairun 2018, kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da wasu 'yan matan 110 daga makarantarsu da ke garin Dapchi a arewa maso gabashin Najeriya.
A shekarun baya, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi matukar rage hare-haren Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Hare-hare sun ragu sannan an rage ambato kungiyar a kafofin yada labaran kasashen waje. Amma wani rikicin na ruruwa a wani wurin.
'Yan bindiga ko barayin daji na ci gaba da yin fashi da makami da satar mutane domin kudin fansa a arewa maso yammacin Najeriya.
An sha sace 'yan siyasa da 'yan kasuwa da matafiya har ma da dalibai a lokuta daban-daban kafin a sako su bayan biyan kudin fansa, sai dai ba kamar yadda aka gani a watan Disamba ba lokacin da aka yi awon gaba da dalibai maza 300 daga makarantarsu ta kwana da ke garin Kankara.
Jami'an tsaron Najeriya da jami'ai a garin Kankara sun bayyana cewa 'yan bindiga ne suka sace daliban.
Amma lokacin da kafafen yada labaran kasashen waje suka zuzuta alakar daliban Kankara da na 'yan matan Chibok, sai Shekau ya ga wata dama.
Kwanaki uku bayan sace daliban na Kankara, Boko Haram ta ce ita ce ta kai harin.
Nan da nan kuwa sai kafofin yada labarai na kasashen waje suka bai wa wannan mutum mai son jan hankalin jama'a damar yin kidansa da rawarsa.
Garin yin haka kuwa, suka iza wutar yada labarin da ba haka yake ba, suka yi watsi da bayanai na ainihi.
'Shekau na matukar so ya samu karfin iko'
Labarai da dama da suka alakanta sace daliban Kankara da Boko Haram ba su duba ta wacce hanya kungiyar ta fadada ayyukanta daga arewa maso gabashin kasar zuwa arewa maso yammaci ba, yankuna biyu da ke da tazara mai yawa.
Ko a lokacin da take kan ganiyarta, Boko Haram ba ta kai hare-hare sosai a arewa maso yammacin kasar ba.
Ta dai sa abubuwan fashewa jefi-jefi, duk da cewa an rasa rayuka.
A wani salo mai kama da wannan da Shekau ya aikata a 2014, ya saki wani bidiyo yana nuna daliban na Kankara.


Duk da cewa kafofin yada labarai na gida suna nuna fargaba kan rashin tsaro a Najeriya, sun yi tantama kan alakanta sace daliban Kankara da Boko Haram.
Lokacin da jaridar The Cable ta Najeriya ta nuna wa wasu daga cikin iyayen yaran bidiyon da Shekau ya saki na samarin, sun musanta sahihancinsa.
"Me ya sa suke mana wasa da hankali?", in ji iyayen. "Wannan bidiyon ba gaskiya ba ne. Ba 'ya'yanmu ba ne a ciki."

Asalin hoton, Reuters
Sai dai ba a saurari wadannan iyaye ba saboda kafofin yada labarai sun dage kan alakanta wannan lamari da batun Chibok.
Wasu masana harkokin siyasa sun ce mai yiwuwa ba Boko Haram ce ta sace yaran ba, amma akwai sa hannunta ta fannin horo da karfafa gwiwar wadanda suka sace daliban na Kankara.
'Yan Najeriya da dama na ganin cewa Boko Haram ta tsoma baki ne kawai bayan da kafofin watsa labarai na kasashen waje suka fara yada labarin.
Gwamnati ta ce ba ta biya kudin fansa ba ga wadanda suka sace yaran, wadanda har yanzu ta ce 'yan bindiga ne.
Yadda ake watsa irin wadannan munanan labarai na da muhimmnaci: ya kamata a karfafa wa gwamnati gwiwa ta mayar da hankali, wadanda aka sace kuma ya kamata a rika tunawa da su sannan a gargadi jama'a.
Amma ana iya yin wannan ba tare da an zaburar da masu laifi ba sannan a daina koya musu hanyoyin aikata laifukan.












