Nahiyar Afrika ba ta buƙatar wani darasi daga Amurka

Joe Biden speaking in Kenya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden a 2010 ya shaida wa mutanen Kenya ba darasi ya je bayarwa ba.

A jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, Waihiga Mwaura ya yi nazari kan abubuwan da kasashen nahiyar za su sa ran gani daga sabon shugaban Amurka Joe Biden.

Short presentational grey line

An shimfida jar darduma a dakin taron da ya cika makil da jama'a inda aka tsaurara tsaro sannan Joe Biden ya soma gabatar da jawabi.

Wannan lamari ya faru ne a birnin Nairobi a shekarar 2010 kuma 'yan kasar Kenya sun je wurin domin sauraren mataimakin shugaban Amurka na wancan lokacin.

"Ina fatan abin da nake fada ba zai zama kamar wani jan kunne ba," ya ce a wani yanayi da ya saba yi kafin ya soma gabatar da jawabi.

"Ba jan kunne ba ne," in ji shi. "Amma kun yi asarar albarkatun kasarku da dama ta hanyar cin hanci kuma ba a hukunta ko da babban jami'i daya ba bisa wadannan laifuka."

Shugaban Amurka Trump da na Najeriya Muhammadu Buhari yayin wani taron manema labarai.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Trump da ake gani tare da Shugaban Najeriya Buhari a nan, ya sauya kallon da ake yi wa Amurka a kasashen waje

Ina daya daga cikin mutanen da ke kallon jawabin, kuma a lokacin Amurka ce kan gaba a dimokradiyya da tabbatar da bin doka, haka kuma kasa ce da kowa ke da 'yanci da jarumta, wadda ta kasance abar koyi.

Shekaru goma bayan wannan jawabi kenan amma abubuwa da dama sun sauya.

Shin yanzu Mr Biden zai iya yin wannan jan kunne - ba tare da an yi masa raddi ba - idan ya yanke shawarar kai ziyara Kenya?

Shugaba Donald Trump, ta hanyar shirinsa na fifita Amurka a kowanne fanni, ya sauya fasalin huldar kasar da kasashen waje.

Kazalika irin kalaman da ya rika yi sun sauya dangantakar kasarsa da sauran kasashe - daya daaga cikinsu shi ne rahotannin da suka ambato shi yana yin munanan kalamai kan kasashen Afirka.

Kodayake akwai bambanci tsakanin shugaban kasa da kuma ofiahin shugaban kasa, idan aka yi la'akari da abin da ya faru shekaru hudu da suka wuce, ya wajaba ga Shugaba Biden ya sauya kalamansa da kuma salon aikewa da sakonsa idan zai yi jawabi ga Kenya da sauran kasashen nahiyar Afirka.

'Zubar da ƙima'

Akwai misalai masu dimbin yawa da ke nuna yadda Mr Trump ya yi fancakali da al'adun Amurka lamarin da ya zubar da kimar kasar a idanun duniya.

Baya ga kin bayyana harajinsa, da yin kafar-ungulu ka tsaron kasar da kuma yin maganganu da suka ci karo da na masana kimiyya game da annobar korona, har gitsirin da magoya bayan Turpm suka tayar a majalisar dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairu ya zubar da dukkan wata martaba da ake kallonsa da ita.

Shugaba Biden na sanya hannu kan wasu takardu mataimakiyarsa Kamala Haris na tsaye a gefensa

Asalin hoton, Jim Lo Scalzo / Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Biden ya kama aiki nan take ana kammala randar da shi a ranar Laraba

Hakan ya tsinka Amurka inda ba a kallonta da mutuncin da a baya ake ganinta da shi.

Mutum biyar ne suka mutu a yayin da masu tarzoma suka yi yunkurin tarwatsa zaman hadin gwiwa na majalisun dokokin tarayyar kasar wanda zai tabbatar da nasarar Mr Biden a zaben shugaban kasar, lamarin da ya sa aka zargi Mr Trump da yunkurin juyin mulki.

Kasashen duniya sun kalli abin da ya faru a Amurka cike da mamaki - domin kuwa irin wannan tarzoma tana faruwa ne a kasashen da ba su ci gaba ba.

Ba editocin jaridun Kenya ne kadai ba suka bayyana lamarin da cewa "mai cike da hargitsi" kuma "abin kunya" ba - sannan suka bayyana Mr Trump a matsayin "kaskantacce".

Kazalika an rika jifan Amurka da kalamai irin su "kasar masu kama-karya", "kasar da ta durkushe" da kuma "wadda dimokradiyyarta ba ta nuna" ba.

Karin labarai da za ku so ku karanta:

Mr Biden ya shiga fadar White House ne yana mai sane cewa duniya ba ta martaba Amurka kamar yadda ake yi a baya.

Kuma hakan zai yi mummunan tasiri a kan yadda ake tafiyar da mulki a nahiyar Afirka.

Yanzu shugabannin kasashe ba sa girmama Amurka kuma cikin sauki za su rika yin watsi da kiraye-kirayenta kan bin tsarin dimokradiyya.

Gabanin gudanar da zaben shugaban kasa a Uganda, Shugaba Yoweri Museveni ya gaya wa wani dan jaridar Channel 4 cewa gwamnatinsa ta yi dirar mikiya kan masu zanga-zanga ne domin hana maimaita abin da ya faru a Washington.

1px transparent line

A yaren sojoji, tsahon shekaru ana yi wa Amurka kallon kasar 'yan sanda saboda tsaro, idan kuma ana maganar dimokradiyya ana kiranta makura a duniya.

Tambayar a nan ita ce shin kungiyoyin 'yan hamayya da na fararen hula a kasashe irins u Kenya za su dogara da Amurka wajen neman taimako a lokacin zabe?

Shugaban 'yan hamayya a Uganda Bobi Wine, ya yi kira ga Amurka kan ta ja wa gwamnatin kasar kunne kafin da kuma bayan zabe, amma wasu na tunanin ita ma ta kanta take yi a lokacin.

Bayan tsaron da aka sanya mai tsanani, an mika mulki a Amurka kuma majalisa ta koma aikinta wanda hakan ke nuna karfin da hukumomi ke da shi sama da daidaikun mutane.

Yanzu kuma Shugaba Biden zai ji irin yadda ake ji a kasashen da shugabanninsu ke yin fatali da al'adu da kuma yarjejeniyar da aka cimma.

Kazalika, zai bukaci karin nutsuwa wajen kulla yarjejeniya da kasashen Afrika, kuma zai rika kiyaye kalamansa wajen ba su shawarwari.