Larry King: Covid-19 ta kashe shahararren ɗan jaridar Amurka

Larry King

Asalin hoton, @kingsthings

Lokacin karatu: Minti 1

Larry King, fitaccen ɗan jarida mai gabatar da shirye-shiryen talabijin da rediyo a Amurka, ya mutu yana da shekara 87.

An sanar da labarin rasuwarsa ne a shafinsa na Twitter inda aka bayyana cewa ya rasu ne a ranar Asabar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Rahotanni sun nuna cewa fitaccen ɗan jaridar, wanda ya lashe lambobin yabo da dama, ya mutu ne sanadin cutar korona.

King ya mutu ne a safiyar Asabar a asibitin Cedars-Sinai da ke birnin Los Angeles, kamar yadda kamfaninsa na watsa shirye-shiryensa ya bayyana a wata sanarwar ta'aziyyar da ya aika ga iyalansa.

A farkon watan nan ne rahotanni suka bayyana cewa King ya kamu da korona, abin da ya sanya aka kwantar da shi a asibiti a sashen da ake sanya wa mutane iskar taimakawa wajen yin numfashi.

A shekaru sittin da ya kwashe da ya kwashe yana aikin jarida, wadanda suka hada da shekaru 25 da ya yi yana gabatar da sirye-shirye a CNN, King ya yi hira da manyan 'yan siyasa da taurarin fina-finai da 'yan wasan kwallo.

King ya soma shahara ne a shekarun 1970 inda ya rika gabatar da shirinsa mai suna The Larry King Show, oa gidan talbijin mai zaman kansa na Mutual Broadcasting System.

Daga bisani ya rika gabatar da shirin Larry King Live a gidan talbijin na CNN, daga shekarar 1985 zuwa 2010, inda ya roka hira da fitattun mutane.

Ya kwashe fiye da shekaru 20 yana wallafa makala da yin sharhi a jaridar USA Today.

Biyu daga cikin 'ya'yansa biyar sun mutu a shekarar da ta wuce - daya sakamakon ciwon zuciya, dayan kuma sanadin cutar daji.

A shekarar 1988 ya kafa gidauniyar Larry King Cardiac Foundation, wadda ke taimaka marasa galihu da ke fama da ciwon zuciya da kudin neman magani.