Coronavirus: Abba Kyari ya rasu a Jihar Lagos

Aba Kyari

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, Abba Kyari ya mutu ne da tsakar daren Juma'a a Jihar Legas
Lokacin karatu: Minti 2

Allah ya yi wa Mallam Abba Kyari Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaba Shugaban Kasa rasuwa a ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu sakamakon cutar korona.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari Femi Adesina ne ya sanar da mutuwar Abba Kyari a tsakar daren Juma'a da misalin 12.50 a shafinsa na Twitter.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Abba Kyari ya rasu ne a Legas, inda ya koma can bayan ya kamu da cutar korona domin ci gaba da jinya.

An yi jana'izarsa a Makabartar Gudu da ke Abuja a ranar Asabar bisa tsarin hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya, a cewar fadar shugaban kasa.

Kazalika fadar ta ce ba za a yi zaman makoki ba.

Da ma rahotanni sun ce Abba Kyari yana fama da wata rashin lafiya kafin ya kamu da cutar korona, kuma masana harkar lafiya sun ce masu fama da wata cutar na daga cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin mutuwa daga cutar ta korona.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

A ranar 24 ga watan Maris ne aka tabbatar da cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriyar ya kamu da cutar korona bayan komawarsa kasar daga Jamus.

Labarin ya ja hankalin 'yan kasar sosai saboda girman mukaminsa.

Abba Kyari shi ne babban jami'in gwamnatin kasar na farko da ya harbu da covid-19.

A ranar 29 ga watan Maris ne Abba Kyari ya rubuta wata wasika, inda yake cewa ya tafi Legas domin ci gaba da jinya a kashin kansa don ya dauke wa gwamnati nauyin kula da shi.

Tuni maudu'in mai sunan Abba Kyari ya rika tashe a shafin Twitter, inda 'yan Najeriya ke ta jajantawa tare da bayyana ra'ayoyinsu kan mutuwar tasa.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Abba Kyari a takaice

Abba Kyari ya kasance mutum mai karfin fada a ji a gwamnatin Shugaba Buhari.

Dan asali jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin kasar. Kyari tsohon dan jarida ne, kuma tsohon ma'aikacin banki, inda ya rike manya-manyan mukamai a wasu bankunan kasar.