Yaya batun haƙƙin ɗan adam zai kasance a Saudiyya ƙarƙashin mulkin Biden?

Protest against Saudi Arabia's human rights record, Washington (Oct 2019)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu fafutuka sun ce dole Saudiyya ta ɗauki alhakin cin zarafin ɗan adam da take yi
    • Marubuci, Daga Frank Gardner
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Tsaro na BBC

Tawagar yaƙin neman zaɓen Shugaba Biden ta zargi gwamnatin Trump da kawar da kai kan cin zarafin ɗan adam da mummunan yaƙin da aka daɗe ana yi a Yemen, wanda ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar mutane a tsawon shekara shida da aka shafe ana yi.

Sabuwar tawagar ta Fadar White House ta yi alƙawarin sauya dangantakarta da Saudiyya, inda a yanzu za a dinga bai wa kula da haƙƙin ɗan adam muhimmanci sosai da sosai.

Shugaba Biden ya nuna alamar kawo ƙarshen goyon bayan da sojojin Amurka ke bai wa rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta a Yemen.

Tuni bayan da ya yi mako ɗaya a kan karagar mulki, Amurka ta dakatar da sayar da makamai na biliyoyin daloli da take yi ga Saudiyya da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa UAE, har sai an sake nazari.

Amma ko akwai abin da ka iya sauyawa a ƙarshe? Ko gwamnatin Biden za ta iya aiwatar da wani abun kan cin zarafin ɗan adam da aka daɗe ana yi a ƙasar ko kuma yaƙin da Saudiyyar take yi a maƙwabciyarta Yemen?

Koma dai mene ne, Saudiyya babbar ƙawar Amurka ce a fannin tsaro a yankin Larabawa, muhimmiyar ƙawa ce a yankin ta wajen daƙile yawaitar sojojin sa kai da Iran ke goyon baya a yankin Gabas Ta Tsakiya, sannan ita ce babbar abokiyar kasuwancin Amurka wajen sayen makamai.

Saudiyya a idon duniya

A cewar Cibiyar Binciken Zaman Lafiya ta Stockholm (Sipri), Saudiyya ce ƙasar da ta fi yawan sayen makamai a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019, daga hannun Amurka. Ana amfani da makaman da ake saya daga ƙasashen yamma da suka haɗa da Birtaniya ne wajen kai hare-hare wurare irin su Yemen.

Kamar yadda Andrew Smith na Ƙungiyar da ke yaƙi da kasuwancin makamai ta Birtaniya ya nuna, idan har ana son samun sauyi, "Dole sai Biden ya yi abin da ya fi wanda ya yi a lokacin da yana mataimakin shugaban ƙasa a zamanin mulkin Obama."

"A lokacin Obama ne aka fara kasuwancin makamai ka'in da na'in."

Kan batun haƙƙin dan adam a Saudiyya kuwa, jami'an ƙasar sun fitar da bayanai cewa an samu raguwa sosai kan zartar da hukuncin kisa. Manyan na hannun daman Yarima Mai Jiran Gado mai ƙarfin faɗa aji Mohammed Bin Salman, ko MBS kamar yadda aka fi saninsa, sun san illar da labaran da ake yaɗawa na take haƙƙin ɗan adam a ƙasar ke yi musu a idon duniya.

MBS ya ce ɗan majalisar dokokin Birtaniya Crispin Blunt, "yana samun bayanai masu cin karo da juna daga waɗanda ke zagaye da shi amma wannan (batun da Joe Biden ke nanatawa na haƙƙin ɗan adam) ya bayar da wata damar ta taimaka wa na hannun damansa su ba shi shawara cewa yadda ake kallon Saudiyya a duniya na da muhimmanci.

Tun bayan da ya ɗare muƙamin yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya a shekarar 2017, ƙasar ta fara ganin sauye-sauye.

Yariman ya yi ta gabatar da sauye-sauyen da suka shafi zamantakewa, inda ya ɗage haramcin hana mata tuƙin mota, da bayar da damar nishaɗi da cakuɗuwar maza da mata, tare da rage ƙarfin da malaman addini ke da shi.

Saudiyya a yau ta ga sauyi a fannin jin daɗi da walwalar jama'a da ba ta taɓa gani ba a shekara biyar da ta gabata.

A lokaci guda kuma dai yariman - wanda ba kamar sauran manyan ƴan gidan sarautar ba, bai yi rayuwa a ƙasashen yamma ba - ya bayar da ƙaƙƙarfan umarnin tauye ƴancin albarkacin baki. A Saudiyya mutane na iya yin ƙorafi a intanet idan dai har ba za su yi zanga-zanga a kan titi ba.

Amma a yanzu ko ɗaya daga ciki ba za su iya ba. An kama dubban mutane tare da ɗaure su a gidan yari, inda yariman ya yi wa ƙalilan afuwa, wanda ke kallon suka ko da ta gyara ce a matsayin wani ƙoƙarin rushe shirinsa na ci gaba.

Zarge-zarge da cin zarafi

Manyan batutuwan cin zarafin bil adama da suka faru sun sa an mayar da MBS saniyar ware a ƙasashen yamma.

Waɗannan sun haɗa da kisan gillar da aka yi wa fitaccen ɗan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi a cikin ofishin jakadancin ƙasar da ke Santambul a shekarar 2018 (kwanan nan za a fitar da wasu bayanan da ba na sirri ba daga CIA), kama da zargin azabtar da mai rajin kare haƙƙin mata Loujain al-Hathloul.

Ana yawan yin shari'o'i a cikin sirri, inda ake hana waɗanda ake musu shari'a damar gana wa da lauyoyi, sannan ana amfani da kotunan da ke shari'ar yaƙi da ta'addanci wajen yin shari'ar masu yi wa gwamnati boren lumana.

Loujain Al-Hathloul

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mai fafutukar kare haƙƙn mata ta Saudiyya Loujain al-Hathloul tana fuskantar tuhuma

Akwai mutane da dama da aka ɓatar da su a ƙarƙashin mulkin yarima mai jiran gado. Lamarin ya kai har ana taɓa manyan ƴan masarautar inda aka kama Yarima Ahmed bin Abdulaziz mai shekara 79, wanda ɗa ne ga sarkin masarautar na farko, a bara aka kuma tuhume shi da cin amanar ƙasa.

Sannan kuma ana tsare da tsohon yarima mai jiran gado Mohammed bin Nayef, wanda shi ne ya jagoranci samun nasara a kan hare-haren ƙungiyar al-Qaeda a shekarun 2000.

Tsohon shugaban hukumar leƙen asirinsa kuma babban abokin CIA, Saad al-Jabri ya tsere Canada a 2017 sannan ya shigar da ƙarar MBS, inda ya zarge shi da tura wata tawaga don kashe shi a makonnin da suka biyo bayana kisan Khashoggi.

An fitar da ƴaƴan Al-Jabri daga gidansa a Saudiyya sannan aka zargesu da cin arziƙin kuɗin ƙasar "na sata."

Masu gargaɗi

Shugaba Trump bai mayar da hankali sosai kan waɗancan batutuwan ba. Ya zaɓi Saudiyya a matsayain ƙasar da ya fara ziyarta a 2017 bayan hawansa mulki, kuma ya fi mayar da hankali kan cimma yarjejeiya maimakon matsa mata lamba kan batun haƙƙin ɗan adam.

"Ko wane shugaban Amurka yana da nasa nau'in tasirin," a cewar Andrew Smith na Caat. "Suna amfani da hakan ne wajen dimokraɗiyyarsu. Trump bai yi hakan ba."

President Donald Trump joins dancers with swords at a welcome ceremony ahead of a banquet at the Murabba Palace in Riyadh on 20 May 2017

Asalin hoton, MANDEL NGAN/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump, a yayin da ake wata rawar takobi ta al'adar Saudiyya a yayin da ya kai ziyara ƙasar a 2017

Dennis Ross, wanda ya shafe shekaru a matsayin jami'in diflomasiyya a ma'aikatar harkokin wajen Amurka na al'amuran Gabas Ta Tsakiya, ya shaida wa BBC cewa: "Gwamnatin Trump ta yi babban kuskure wajen rashin saka wasu iyakoki kan alaƙarta ta ƙut da ƙut da Saudiyya. Amma ta yaya hakan zai amfane mu wajen cimma muradunmu?"

Duk da aniyar gwamnatin Biden da aka ambata, za a samu masu yin gargaɗin yadda za a yi mu'amala da Saudiyya a cikin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka da CIA da ma'aikatar tsaro ta Pentagon da kuma ƙungiyoyin da ke goyon bayan mallakar makamai na Amurka.

Sannan idan har wani dalili ya sa zuri'ar Al-Saud ta rasa mulkin masarautar, akwai yiwuwar mulkin ya koma hannun masu tsananin kishin Islama da ba sa ga maciji da ƙasashen yamma. Manyan jami'an diflomasiyya irin su Dennis Ross sun san hakan.

"Ba za mu iya gaya wa Saudiyya duk wani abu da za su yi ba. Ba ka dukan mutum a bainar jama'a ko tursasa shi yin abin da bai so ba. Ana buƙatar tattaunawa ne cikin sirri."

Hatice Cengiz at a human rights conference in London

Asalin hoton, Frank Gardner

Bayanan hoto, Matar Jamaal Khashoggi ta yi ƙarar yarima mai jiran gado kan kisan mijinta

To bari mu koma ga tambayar farkon: ko gwamnatin Biden za ta iya inganta haƙƙoƙin ɗan adam a Saudiyya? E za ta iya. Ya danganta da yadda Fadar White House ta jajirce a kan lamarin kuma sai dukkan ƙasashen biyu sun mayar da hakan jigo a abin da suke son cimma.

Rasha da China za su zo su yi harkar kasuwanci sosai da Saudiyya kuma ba za su dinga sa ido kan haƙƙoƙin ɗan adam ba.

Amma har yanzu, Amurka ce babbar ƙawar Saudiyya kuma wani ɗan cikin gida a masarautar ya ce, "gwamnatin Biden za ta haska fitilarta sosai kan haƙƙƙin ɗan adam fiye da a baya. Hakan na cikin jerin abubuwan da ake son yi a yanzu, kuma yana buƙatar aiki ƙarara ba maganar baki kawai ba."