Joe Biden: Abin da ya sa shugaban Amurka ya dakatar da sayar da makamai ga Saudiyya da UAE

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Amurka ta dakatar da sayar wa Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa makamai yayin da take nazari kan yarjejeniyoyin biliyoyin daloli da aka ƙulla lokacin tsohon shugaba Trump.
Matakin zai shafi sayar da jiragen yaƙi ƙirar F-35 ga Hadaddiyar Daular Larabawa da makamai ga Saudiyya.
Sakaataren harkokin wajen Amurka, Antony John Blinken, ya bayyana cewa matakin ba sabon abu ba ne ga sabuwar gwamnati, amma hakan ya biyo bayan kiran da Shugaba Biden ya yi na kawo ƙarshen goyon bayan Amurka ga yaƙin Saudiyya a Yemen.
Ya ce an dakatar da shirin sayar da jirgin da kuma makaman ne da nufin "bai wa sabuwar gwamnati damar bibiyar wadannan yarjeniyoyi."
"Wannan ba wani bakon abu ba ne ga sabon shugabanci, wanda zai nuna mayar da hankali da kuma yin abubuwa a bude da tabbatar da gwamnati mai kyau," in ji Mr Blinken.

Asalin hoton, Reuters
Yayin da gwamnatin Trump ta goyi bayan yakin da Saudiyya take yi a Yemen, shi kuwa Shugaba Biden ya fito ƙarara ya bayyana cewa yana son kawo ƙarshen goyon bayan da sojin Amurka suke ba da wa a yaƙin.
Gwamnatin Biden da ba tafi mako guda ba da karbar mulki, ta nuna karara cewa tana son kawo karshen wannan rikici da Saudiyya ke jagoranta a Yemen wanda kuma wata mafita ce ga mutane.
Wani ciniki da za a yi wanda ya fi ko wane riba mai tsoka shi ne, na sayarwa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa jiragen yaƙi ƙirar F-35 kan kudi dala biliyan 23.

Asalin hoton, Reuters
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ne ya amince da wannan ciniki na jirgi mai layar-zana irin sa na farko da wata kasar Larabawa za ta mallaka - kuma hakan ya zo ne bayan amincewar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi da sabunta alakarta da Isra'ila.
Dakatar da cinikin za ta iya haifar da tambaya kan ko Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta yarda da sabunta yarjejeniyarta da Isra'ila, wadda gwamnatin Trump ke dauka a matsayin wanni abu mai muhimmanci da aka cimma.
'Yan majalisa a Jam'iyyar Democrat sun nuna shakku game da yarjejeniyar, suna nuna fargabar samun rige-rigen mallakar makamai, amma majalisar dattawa a lokacin Trump ta gaza dakatar da hakan.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi Allah-wadai da wannan ciniki, suna cewa hakan zai iya haifar da bazuwar makamai a yankin musamman a Libya da Yemen, inda Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Saudiyya suka sanya karfinsu kan yaki da 'yan tawayen Houthi.










