Fina-finan Kannywood mafiya shahara a 2020
Daga Muhsin Ibrahim na Jami'ar Cologne; [email protected]

Asalin hoton, Rahama Sadau facebook
Shekarar 2020 ta zo da abin da ba a taɓa gani a baya-bayan nan ba, saboda sauyin da cutar coronavirus ta kawo a duniya. An sassaka dokar kulle a ƙasashe daban-daban.
An sa sai mutane sun ba da tazara tsakaninsu, sai kuma sun saka takunkumi a fuska, da sauran tsare-tsare.
Ga shi cutar ta kawo naƙasu wa masana'antun fim, kama daga Los Angeles zuwa Lagos, daga Mumbai zuwa Mombasa, daga Alƙahira zuwa Kano, wanda hakan ya tilasta wa sinimomi da dama rufewa.
Saboda haka, ta sa dole an daina ɗaukar fim tare da nuna shi. Amma duk da haka an sami ci gaba ta fannin talabijin da kuma manhajar kallon bidiyo kai-tsaye (wato Video on Demand, VoD).
Sannan hakan ya sa an sami cigaba wajen samar da hanyoyin nuna shirye-shiryen fim ta manhajar YouTube.
A arewacin Najeriya, an sami shirye-shirye irin su Kwana Casa'in, Gidan Badamasi, Labarina, Izzar So, A Duniya, Na Ladidi, da sauransu.
Kannywood ta fara wannan shekarar da ƙafar dama bayan shirin Mati A Zazzau ya sami karɓuwa.
Saboda haka, masu kallo sun yi tsammanin fitowar fina-finai kamarsa ko ma waɗanda suka fi shi.
Duk da cewa fina-finai kaɗan furodusoshin suka sami damar yi, amma a cikinsu akwai masu kyau da kuma akasin haka.
Abu ne a fili cewa wannan cutar ta kawo tsaiko wa abubuwa da dama a Kannywood. A taƙaice dai, waɗannan su ne fina-finan da nake ganin sun yi zarra.
A kuma lura cewa yadda aka jera su ba yana nuna wani ya fi wani daraja ba ne.

Mati a Zazzau

Asalin hoton, Rahama Sadau facebook
A matsayinsa na ci gaban Mati da Lado, wannan fim ɗin ya fara ne a wajen da Mati (Sadiq Sani Sadiq) yake ta gararamba a wani ƙauye bayan tserewar da ya yi daga Rimau.
Shi da ɗan'uwansa Lado (Tahir I. Tahir) sun jima suna damfarar mutanen Rimau da sunan cewa su malaman addini ne.
Daga baya kuma sai mutanen garin suka fatattake su bayan sun gano su waye su. Mati sai ya tsinci kansa a Zazzau, inda ya ci sa'a nan ne mahaifinsa ya yi rayuwa har ya bar dukiya mai tarin yawa a hannun wani amininsa.
Sauran fim ɗin kuma duk ya ginu ne a kan yadda Mati yake ta ƙoƙarin samun wannan dukiyar ta kowace hanya. Yaseen Auwal ne ya ba da umarni, yayin da Rahama Sadau da kuma Sadiq Sani Sadiq suka shirya shi.
Ba shakka wannan shiri ya sami karɓuwa saboda yadda Rahama Sadau da sauran abokan aikinta suka yi ruwa da tsaki wajen ganin ya karaɗe ko'ina.

Dafin So

Asalin hoton, Dafiin So
A fim ɗin, Bashir (Adam A. Zango) ya taso a hannun mahaifiyar da take sakalta shi har ya lalace, wanda daga baya ya koma shaye-shaye. Bayan ya gudu daga gida, sai ya dawo kamar wani mahaukaci.
Wata rana, Nabila (Aisha Tsamiya), wacce ƴar manyan mutane ce, ta kawo gyaran mota a kusa da bolar da Bashir da abokansa suke shaye-shayensu.
Shi kuwa sai ya zo garejin ya roƙi makaniken da su taimaka masa da abinci kamar yadda ya saba. Sai suka kore shi, saboda ba wa kwastomarsu kariya. Ita kuma sai ta tausaya masa.
Ta yi ƙoƙari wajen nemo shi tare da dawo da shi yanayi mai kyau kamar yadda yake kafin ya fara shaye-shaye. Daga baya sai ta fara sonsa, har ta ce masa ya aure ta—mahaifinta kuwa ya yi fatali da wannan batu.
Bayan ta yi hatsari ta koma tafiya a keken guragu, sai wanda za ta aura ya guje ta. A nan ne fa mahaifinta ya fahimci cewa ba mai auren ƴarsa sai mai sonta tsakani da Allah—wannan kuwa ba kowa ba ne illa Bashir.
Duk da cewa labarin ba wani sabon abu ba ne da ba a taɓa yinsa ba, amma yadda aka shirya shi ya cancanci yabo. Sadiq N. Mafia ne darakta. Abdul Smart kuma shi ne furodusa.
Alaƙar fim mai gamsarwa tsakanin Zango da Tsamiya a fili take, sannan yadda suka nuna ƙwarewa a cikin shirin abin a jinjina musu ne.

Kazamin Shiri

Asalin hoton, Kazamin Shiri
Alhaji Sammani (Rabi'u Rikadawa) wani attajiri ne wanda ke zaune lafiya da iyalansa. Ba zato ba tsammani sai ya faɗa son wata matar aure, Karima (Balkisu Shema), wacce ta yi haƙuri take zaune da mijinta, Badamasi (Ali Nuhu), wanda ba kuɗi ne da shi ba.
Ta ƙi amincewa da soyayyar Sammani. Bayan aminiyarta (Fati Washa) da mahaifiyarta da mijinta sun matsa mata lamba, sai kawai ta miƙa wuya.
Fim ɗin a cike yake da cakwakiya, amma kuma ya haɗu. Ƙarshensa zai iya sa mutane su koyi irin wannan ɗabi'a duk da cewa Kannywood na cikin al'umma da ke taka-tsantsan da tarbiyyar al'ada da kuma ta addini.
Sunusi Oscar 442 ne y aba da umarni. Alhaji Sheshe kuma ya shirya fin ɗin. Aminu Sharif da Fati Washa sun taka rawar gani. Rabiu Rikadawa ma ya nuna bajintarsa a wannan shirin.

Fati

Asalin hoton, Fati
Wannan shirin ya fita daban daga sauran fina-finan da ake yi a Kannywood. Labari ne a kan wani mai matsalar ƙwaƙwalwa, wato Umar (Umar M. Sharif), wanda ake masa gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa.
A farkon fim ɗin an nuno shi yana soyayya da Fati (Fati Kinal), wadda daga baya ta rasu. Da abin ya dame shi, sai kawai ya yi ta-maza ya mance da ita, ya koma makaranta har ya kammala.
Bayan ya tafi bautar ƙasa (wato NYSC) a Jigawa, sai ya ga waccar Fatin dai, amma kuma ta nuna ba ta ma san shi ba. Ya yi iya ƙoƙarinsa don tunatar da ita rayuwar da suka yi a baya.
Sai dai da yawa daga cikin masu kallon fim ɗin sun ƙalubalanci yadda aka tafiyar da shirin.
Nuna al'amura mabanbanta guda biyu da aka yi—duk da cewa suna da alaƙa—a ɓangare guda, za a iya cewa ma'ana ba ta fito ba, a ɗaya ɓangaren kuma, za a iya cewa bai kama hankali ba.
Hakanan wasu wurare a fim ɗin sun yi kama da wani fim mai suna Hafeez wanda duk furodusa ɗaya ne ya yi su, sannan ƴan wasan da suka yi wannan su suka yi wancan.
Kamal S. Alkali shi ne darakta. Bashir Maishadda kuma shi ne furodusa.

Voiceless

Asalin hoton, Voiceless
Voiceless fim ne da yake magana game da ta'addancin Boko Haram na sace ƴan matan Chibok.
Labari ne a kan wani mai suna Goni (Adam Garba) da kuma Salma (Asabe Madaki)—waɗanda "Sojojin Aljanna" suka yi garkuwa da su.
Duk da cewa soyayyarsu ta taimaka wajen gina labarin, amma ba ita ce ginshiƙi ba. Abin da dai shirin ya ta'allaƙa a kai shi ne, ta'addanci da abubuwan da yake haddasawa.
Fim ɗin ya sha yabo daga waɗanda suka kalle shi—Musulmi da Kirista—saboda yadda ya fito da irin wannan maudu'i mai cike da sarƙaƙiya.
Duk da cewa sunan fim ɗin da Turanci ya fito, zantukan cikinsa da Hausa aka yi su. Da yawan jaruman fim ɗin Hausawa ne, amma waɗanda suka shirya shi ba Hausawa ba ne: daraktan shi ne Robert O. Peters, furodusa kuma Rogers Ofime.
A taƙaice dai, wannan kamar ƙalubale ne ga mutanen Kannywood da yawanci suke satar fasaha daga Bollywood duk da cewa ga abubuwa da dama a kusa da su da ya kamata su yi fim a kai.

The Milkmaid
The Milkmaid shi ma dalilin Boko Haram da kuma wani hoton matan Fulani masu sayar da nono a bayan naira 10 aka shirya shi.
Najeriya ta miƙa shi ga Oscars (2021) a matsayin wanda ta zaɓa don shiga gasar ƙasa da ƙasa inda za a zaɓi fim ɗin da ya fi kowanne zarra.
Wannan fim shi ne na biyu da ya taɓa zuwa wannan matakin, bayan Lionheart na Genevieve Nnaji, amma kash, bai samu karɓuwa ba.
The Milkmaid, wanda aka shirya shi a Jihar Taraba, yana ba da labarin wata mata mai sayar da nono ne, wato Maryam Booth, wacce ƴan Boko Haram suka sace mata ƴar'uwa.
Duk da ban kalle shi ba, amma miƙa shi da Najeriya ta yi don ya shiga gasa ya nuna cewa ya dace na ƙirgo shi a nan. Ba Hausawa ba ne suka yi shi, amma zantukan ciki da Hausa aka yi su.
Sannan tallen fim ɗin kawai ya nuna cewa zai ƙayatar.
Wataƙila wannan zai iya zama wani ƙalubale ga masu shirya fim a Kannywood, domin wannan ma Desmond Ovbiagele ne ya rubuta shi, sannan shi ne daraktan kuma furodusa a lokaci guda.

Jalil

Asalin hoton, Jalil
Wannan kuma labarin wasu ma'aurata ne, Yusuf (Yakubu Mohammed) da kuma Zahra (Maryam Booth), waɗanda ɗansu, wato Jalil, ya kamu da rashin lafiya har aka buƙaci naira miliyan 33 domin yi masa aiki.
Su kuma ba su da wannan kuɗin duk da sun nemi taimako ta intanet. Shi kuwa Yusuf ya ƙi bin haramtacciyar hanya don nemo wannan kuɗi.
Ashe hakan bai yi wa mahaifiyarsa daɗi ba. Zahra ma'aikaciyar gidan talabijin ce sannan tana da aboki, Jazzy (Sadi Sawaba), wanda yake neman kuɗi ido-a-rufe don ya biya bashi.
Saboda haka sai Jazzy da surukar Zahra suka yi ƙaryar an yi garkuwa da ita surukar saboda kawai su sami kuɗi a wajen Yusuf da Zahra da kuma wan Yusuf (attajiri) wanda a farko ya ƙi taimakonsu saboda rikicin cikin gida.
Fim ɗin yana da wasu ƴan matsaloli, kamar su ƙawance da ke tsakanin Zahra da Jazzy, rashin bayyana dalilin da ya sa Jazzy ke maitar kuɗi, rashin cigaban wasu wurare, da sauransu.
Duk da haka, shirin ya yi kyau. Sannan kuma wannan ma ba Hausawa ne suka yi shi ba amma cikin harshen Hausa aka yi shi.
Yawanci jaruman fim ɗin Hausawa ne. Leslie Dapwatda ne daraktan yayin da Kelly D. Lenka ne furodusa.











