Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cutar Korona a Kenya: Likitan da yake taimaka wa yara farin ciki
Mutuwar Dr Ashraf babban likitan tiyatar fata a kasar Kenya sakamakon cutar korona a watan da ya gabata, ta nuna halin da ma'aikatan kiwon lafiya da ke bukatar kariya ga wadanda ke kan gaba wajen yaƙi da cutar ta korona, kamar yadda rahoton Basillioh Mutahi ya nuna.
Likitan tiyatar, kuma daya daga cikin ƙwararrun likitoci a yammacin Kenya, ya kamu da ƙwayar cutar Korona, inda cutar ta ƙara zafi kuma babu gadaje a ɓangaren gaggawa na lura da marasa lafiyar da ta yi tsanani a asibitin nasa - Asibitin Koyarwa na Moi (MTRH) a yankin Eldoret.
Dr Emarah ya koyar wa da dalibai masu koyon aikin likita a asibitin koyarwar na MTRH, asibitin ƙwararru mafi girma a kasar da ya shafe shekaru da dama.
Iyalan likitan da abokan aikinsa sun yi yunƙurin mayar da shi zuwa Nairobi babban birnin kasar mai nisan daruruwan kilomita daga nan.
Amma kuma kudin da za a kashe wajen hayar jirgi mai saukar ungulu na ɗaukar marasa lafiya na da ''tsadar gaske'', wani likita kuma jami'in kungiyar likitocin ya fada. Hatta muhimmin maganin da yake buƙata a yanayin yadda ya samu kansa cikin mawuyacin hali yana da wuyar samu.
"Sai da likitoci suka yi karo-karo suka sayi maganin'' don farfado da shi, Dr Chibanzi Mwachonda, sakatare janar mai riƙon ƙwarya na kungiyar likitoci da likitocin hakori da masu hada magunguna ta kasar Kenya (KMPDU), ya shaida wa kwamitin majalisar wakilai.
"Abin bakin ciki ne halin da ake ciki,'' Dr Mwachonda ya ce, yana mai nuni da cewa likitoci ba su da wata tsayayyiyar kariya ta kiwon lafiya daga hukumar inshorar lafiya ta kasa.
An kai likitan wani asibiti mai zaman kansa da ke Nakuru garin da ke tsakanin biranen Eldoret da Nairobi, inda ya yi jinya ya samu gadon kwanciya a dakin lura da masu cuta mai tsanani.
Amma kwana daya bayan hakan, a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba ya mutu.
Karancin likitoci
Dr Emarah shi ne ƙwararren likita na hudu da ya mutu cikin wancan makon, a wani kiyasi a kasar da ya nuna cewa akwai likitoci kimanin 7,000 ga yawan al'umma miliyan 48.
Mako guda kafin rasuwarsa, ya yi aikin tiyata da kuma duba dalibai kafin ya soma samun alamun kamuwa da ƙwayar cutar bayan kwana guda, abokinsa Dr Anthony Akoto ya sahida wa BBC.
"Ya mutu yayin yaki da cutar, a bakin aiki,'' in ji Dr Akoto, wanda shi ma jami'in kungiyar ne, yana mai cewa mutuwa ta dauke kwararren likitan tiyatar fata daya tilo da suke da shi a yammacin Kenya.
"Kasar na da karancin lkitocin tiyatar fata. A matsayin da ya kai, shi kadai muke da shi, duk da cewa muna da wasu likitocin tiyatar fata masu tasowa, amma duk da haka har yanzu muna da gibi.''
Hukumar gudanarwar ma'aikatan kiwon lafiya ta kasar Kenya ta jera sunayen kwararun likitocin tiyatar fata hudu ne a kasar tun daga shekara ta 2018.
Haifaffen kasar Masar, Dr Emarah wanda ya zo kasar ta Kenya shekara 30 da ta wuce, abokan aikinsa sun bayyana shi a matsayin gogagge a fannin aikinsa, malami da kuma kasancewa kwararren likitan tiyatar fata da za a yi kewarsa matuka.
'Bana jin zan kai labari'
Likitan sananne ne a fannin tiyatar gyara fata ga dubban yara da aka haifa da barkakken lebe da ake kira noma, hakan kuma ya taimaka musu wajen yin murmushi, tare da kara wa wasu likitocin tiyatar fata a kasashe makwabta kamar su Somalia, Uganda da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo basirarsa.
"Muna matukar jimamin mutuwar abokinmu, abokin aikinmu," Smile Train Africa, daya daga cikin kungiyoyin bayar da agajin da ya yi aiki da su, lokacin da ta wallafa hotunan likitan a shafinta na twitter tare da sauran yaran da ya yi wa aikin tiyata.
"Muna mika ta'aziyyarmu ga matarsa da yaransa, abokai, abokan aiki, da yara masu cutar ɓarkakken lebe ta noma da ya taimaka wa lokacin rayuwarsa, da kuma lkitocin tiyatar fata da ya horar.
Tun lokacin da cutar korona ta shigo kasar a cikin watan Mayu, likitoci a ƙalla 14 ne suka mutu yayin annobar.
A ranar Litinin, asibitin koyarwa na KMPDU ya sanar da mutuwar Dr Stephen Mogusu bayan kamuwa da cutar korona.
Baya ga haka kuma aƙalla ma'aikatan jinya 20 da jami'an asibiti 10 ne suka mutu sakamakon kamuwa da kwayar cutar.
Ƙarin labaran da suka shafi cutar korona
Baki daya akalla ma'aikatan kiwon lafiya 2,000 ne suka kamu da cutar, da suka hada da Dr Mwachonda, jagoran kungiyar likitoci, wanda a baya-bayan nan ya bayyana halin damuwar da ya shiga.
Adadin masu kamuwa da kwayar cutar ta korona a makonnin baya-bayan nan a kasar ta Kenya yana karuwa, a yayin da cikin watan Nuwamba aka samu adadi mafi yawa da kwayar cutar da kuma mutuwa tun bayan barkewar annobar a kasar.
Kasar ta samu fiye da masu kamuwa da cutar fiye da 88,000, da suka hada da mutuwar mutum 1,500.
'Muna bukatar kariya'
Dr Doreen Lugaliki, likitar cututtukan mata da yara, daya daga cikin likitocin da suka mutu da cutar ta korona ce. Shekarunta 39 lokacin da ta mutu a ranar 10 ga watan Yuli.
A makon da Dr Emara ya mutu, Dr Vladimir Schuckin, likitan tiyatar rage kiba da Dr Hudson Inyangala, wani kwararre a fannin kiwon lafiya da kuma Dr Robert Ayisi, likitan yara suka mutu.
Duk da karin mutuwar kwararrun likitocin, gwamnati ba ta iya daukar wani mataki na shawo kan matsalar nan da nan ba, likitocin sun yi kiran yajin aiki daga 7 ga watan Disamba kafin su janye na tsawon mako biyu don bayar da damar zaman tattaunawa..
"Ta yaya za ka samu nasarar yaki idan sojoji na ta mutuwa daya bayan daya? Muna bukatar kariya,'' Dr Mwachonda ya shaida wa kwamitin majalisa.
Yayin da yake magana a kan yanayin wuraren aikin da ma'aikatan kiwon lafiya ke ciki a kasar ta Kenya, wasu daga cikin 'yan majalisar sun shiga damuwa.
Sauran kungiyoyin da suke wakiltar ma'aikatan jinya da jami'an kiwon lafiya da suka ci gaba da yajin aikin, su ma suna nuna rashin jin dadinsu game da rashin samun kariya a wuraren aikinsu, abin da suke dauka a matsayin rashin kulawar gwamnati game da annobar cutar ta korona.
Kungiyoyin sun yi nuni da rashin isassun kayan aiki a asibitocin gwamnati, karancin ma'aikata, rashin isassun matakan kayan aiki na kariya da kuma rashin cikakkiyar inshorar lafiya, da suka yi mummunan tasiri kan ''matsananciyar wahala, hadari, da barazana a wuraren aiki''.
"Muna ganin gwamnati ta yi watsi da ma'aikatan kiwon lafiya, wadanda ba sa samun kulawa. Ba mu da isassun kayayykin kariya, likitoci na yin karo-karon su biya kudin magani idan daya daga cikinsu ya kamu da cutar a yayin gudanar da aikinsa,'' Dr Akoti ya shaida wa BBC.
"Muna ganin kamar gwamnati ba ta daukar batun da muhimmanci sosai.''
'Fuskantar abokan gaba ba tare da kariya ba'
Ma'aikatar kiwon lafiya ta duba wasu daga cikin abtutuwan da kungiyoyin suka fito da su, amma kuma ta musanta cewa ta yi watsi da ma'aikatan, tana cewa za a biya musu bukatunsu.
"Yin watsi da sojojinmu, tamkar fuskantar maƙiya ne ba tare da wata kaiya ba,'' kamar yadda sakatariyar hukumar gudanarwar kiwon lafiyar kasar Mercy Mwangangi ta ce.
Ana danganta wasu daga cikin matsalolin bangaren kiwon lafiyar kasar Kenya da cin hanci da rashawa, kana akwai zarge-zargen cewa ana karkata akalar wasu kudaden da aka ware don yaki da cutar ta Korona zuwa wasu abubuwa na daban.
A cikin watan Satumba ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar ta bayar da damar hukunta manyan jami'an gwamnatin Kenya da ke hukumar samar da kayayyakin kiwon lafiya ta Kenya (Kemsa) da ake zargi da bayar da kwangilolin da suka haifar da kashe kudaden da ba bisa ka'ida ba.
Har yanzu ana kan gudanar da bincike bayan da babban mai gabatar da ƙara ya ƙi amincewa ya amince da tuhumar. Wadanda aka bayyana sunayensu sun musanta aikata ba daidai ba.
"Abin sanyaya gwiwa ne... muna da likitocin da ke yaƙi da annobar cutar ta korona kuma ba a biya su albashinsu na watanni hudu ba, amma duk da haka mu kan ji cewa a ma'aikatar lafiya da kuma Kemsa, mun yi asarar biliyoyin shilling ta hanyar cin hanci da rashawa,'' Dr Akoto ya shaida wa BBC.