Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Daga ina sabuwar annobar duniya za ta ɓullo?
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Annobar cutar Covid-19 ta rusa rayuwar mutane da dama da ma tattalin arziƙi amma ba wannan ne karo na farko da wata ƙwayar cuta ta yi wa duniya barazana irin haka ba.
A baya an samu ɓarkewar nau'ukan annoba kamar su SARS da muarar aladu da MERS da Ebola tun a farkon ƙarnin da muke ciki.
Akwai yiwuwar ɗaruruwan ƙwayoyin cututtuka a jikin dabbobi da za su shafi mutane kuma masana kimiyya na sa ido sosai da sosai.
Amma tambayar ita ce ko za mu iya kawar da kai ga irin barazanar da muke fuskanta?