Ku San Malamanku tare da Sheikh Halliru Maraya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon hirar BBC da Sheikh Halliru Maraya a shirin Ku San Malamanku, sannan kuna iya shiga shafinmu na Youtube don kallon cikakken bidiyon:

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kadunan Najeriya ya ce shi ba ya siyasa, mutane na ganin kamar yana yi ne don kawai ya taɓa riƙe muƙami a gwamnatin farar hula shi ya sa ake ganin kamar shi ɗan siyasa ne.

Malamin ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, inda ya ce tsohon gwamnan Kaduna marigayi Patrick Yakowa ne ya naɗa shi mataimaki na musamman kan harkokin addini da aikin Hajji.

"Duk da cewa ni ba ɗan jam'iyyarsa ba ce ta PDP. Sannan sai da na sa masa sharuɗa sannan ya yarda da hakan," a cewarsa.

Malamin haifaffen Unguwar Tudun Wada ne a garin Kaduna, kuma an haife shi ne a watan Agustan 1968, sai dai yana da shekara biyu mahaifiyarsa ta rasu, dalilin da ya sa ya samo sunan maraya kenan.

Ya fara karatun allo tun yana ɗan shekara bakwai, kuma a yanzu shi ne mai gudanarwa a Gidauniyar Zaman Lafiya Ta Duniya a arewacin Najeriya, wato Global Peace Foundation.

Sheikh Maraya ya ce ya fi ƙwarewa a fannonin Fiƙihun Malikiyya da Luggar Larabci da ilimin Hadisi da ilimin Tafsiri da aka fi saninsa a kai.

Ya ce malamansa da ya fi alfahari da su su ne kamar limamin Masallacin Tudun Wadan Kaduna Sheikh Abdulkarim Hashim da marigayi Malam Abubakar Tureta da marigayi Sheikh Lawal Ƙaura Zariya (wanda nake zuwa Zariya kullum tun daga Kaduna don ɗaukar karatu a wajensa).

Malam Halliru ya ce bayan su akwai babban Malami na Madabo a Kano da ya dinga zuwa ɗaukar karatu a wajensa. A ɓangaren tafsiri kuma malaman da yake ji da su su ne kamar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi "wanda idan wani abu ya ɗaure min na kan je na same shi ya warware min wannan abu," in ji malam.

Yaya batun wallafa littattafai?

Malamin ya ce a yanzu haka yana rubuta littafi na addini amma sai ya kammala za a ji sunan littafin. Ya ce abin da ya sa ba ya samun karsashin rubuta littattafai shi ne don ya ga tuni magabata sun yi rubuce-rubuce a kan duk wani fanni na addini.

A cewarsa: "Babban abin da ya kamata mutane su mayar da hankali a kai musamman matasa shi ne su yi karatun. Waɗanda aka rubutan ma za ku ga mafi yawa ba sa zuwa makarantar."

Mai yawan ce-ce-ku-ce

Ana yi wa Malam Maraya kallon mai yawan jawo ce-ce-ku-ce, sai dai ya ce abin da ya sa ake ganin hakan shi ne saboda a yanzu yawancin malaman ba sa son faɗar gaskiya saboda suna ci a jikin gwamnati.

"Da dama ba su da wata sana'ar yi in ba wa'azi ba, ba kamar yadda Annabawa suka yi rayuwa ba, don duk Annabawa suna da sana'ar yi don samun ƴancin tattalin arziki. Amma da zarar ba ka da sana'a to da wuya ka samu ƙarfin halin gaya wa masu mulki gaskiya.

"Za ka zama ɗan amshin-shata ne kawai. To haka malamai suka zama a yau. Shi ya sa sai ka ji idan ana yi da su a gwamnati sai su ce ai babu gwamnatin da ta kai ta. Idan ta wuce wata ma ta zo sai du faɗi haka.

"Da cin su da shan su da suturarsu duk sun dogara ne ta hanyoyin hukuma, ni kuma ba haka nake ba ina da aikin yi. Don haka da zarar sun yi maganar da na ga cewa ba za ta jawo wa al'umma alheri ba, to sai ka ji na ce ba haka ba ne.

"To hakan ne ya sa muke cin karo da su, kuma na kan tambayi dalilai."

Ya bayar da misali kan yadda wasu malaman ke dagewa cewa dole sai Musulmi ne zai yi mulki, ko dole sai Kirista ne zai yi mulki, inda shi kuma yake soke maganganun nasu da "tarin hujjoji."

Babban abin da nake jan hankalin malaman da ya kamata su karkata shi ne waye zai yi adalci, in ji malamin.

Tambayoyin da aka fi yi masa?

Kamar yadda aka sani duk abin da ya shigewa al'umma duhu to su kan kai maganar ne gaban malamai don a warware musu.

Sheikh Maraya ya ce an fi yi masa tambayoyin da suka shafi aure da gado sai kuma tambayoyin da da suka shafi zamantakewa tsakanin Musulmi da Kirista.

Abincin da ya fi so shi ne ɗan wake da mai da yaji. Kuma ya yi wasanni irin na ƙwallon ƙafa lokacin da yake yaro, har ma sukan yi wasa da su Tijjani Babangida da Garba Lawan.

Abin da Malam ya fi nishaɗantuwa da shi shi ne yin karatu.

Sheikh Maraya yana da mata ɗaya da ƴaƴa biyar.