EndSars: Zanga-zangar da ake gudanarwa a Najeriya za ta ƙara haifar da yaɗuwar cutar korona

Kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da cutar korona ya yi hasashen cewa za a iya samun ƙaruwar yaɗuwar annobar cutar nan da makonni biyu a ƙasar.

Kwamitin ya ce wannan ya biyo bayan yin watsi da ka'idojin kiyaye yaduwar cutar da dubban masu zanga zangar da ke gudana ta neman a kawo ƙarshen rundunar musamman mai yaƙi da fashi da makami a ƙasar #EndSARS.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, kuma shugaban kwamitin ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Abuja babban birnin tarayyar kasar a wani taron hadin gwiwa na kwamitin na kasa baki daya.

A kwanaki goma da suka gabata ne dubban masu zanga-zanga suka mamaye muhimman tituna a fadin Abuja, da jihohin Lagos da Edo da Anambra da Rivers da sauran jihohi da suka bi sahunsu, don yin gangamin nuna adawa da mugunta, cin zarafi da kisa ba tare da gurfanarwa a gaban kotu ba da suke zargin jami'an ƴan sanda ke yi.

Irin wannnan mugunta dai sun danganta ta ne ga jami'an ƴan sandan rundunar musamman mai yaƙi da fashi da makami (SARS) da tuni gwamnatin Najeriyar ta rushe.

Boss Mustapha ya ce: "Dole a fadi gaskiya, makonni biyu masu zuwa daga yau, idan aka dauki duk mutanen da suka halarci gangamin a dandalin Lekki Toll Plaza aka yi musu gwaji, za a gano yaduwar kwayar cutar da dama.''

"Duk wani taro mai yawan jama'a da ba a kiyaye dokokin da aka shimfida kamar na saka takunkumin fuska, yin nesa da juna, tsaftar jiki, da kaucewa taruwar jama'a, to ya zama babban taron yaɗa cutar ne ko kana so ko ba ka so,'' a cewarsa.

Ya ƙara da cewa; "Don haka zan iya sake faɗa da babbar murya cewa makonni biyu masu zuwa daga yau, duk wani wanda ya halarci gangami a wurare ba kawai a dandalin Lekki Toll Plaza, ko kuma Unity Fountain da ke Abuja ba, har da sauran wurare da dama, tabbas muna sa ran karuwar cutar ta korona makonni biyu daga yau, don haka ne ya zama dole mu kiyaye a lokacin da muke taruwa.''

Ko a ranar Litinin ɗin sai da hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta bayyana cewa adadin mutanen da annobar korona ta harba a ƙasar sun kai 61,558 bayan da aka gano ƙarin mutum 118 da suka kamu da cutar.

A jihar Legas wacce daya daga cikin jihohin kasar ce da zanga-zangar ta fi ƙarfi, an samu ƙarin mutum 51 da suka kamu da cutar sai Ribas mai mutum 26.

A jumlace mutum 61,558 zuwa yanzu cutar korona ta kama a faɗin Najeriya, cikin su mutum 56,697 sun warke yayin da 1,125 suka rasa rayukansu.

Tun dai bayan da aka fara gudanar da zanga-zangar nuna ƙin jinin rundunar musamman din ta SARS a sassa daban-daban na kasar, a cikin dandazon dubban jama'a a wasu manyan biranen kasar wasu jama'a suka fara fargabar cewa hakan zai iya yada cutar ta korona.

Hakan kuma na da nasaba da yadda za ka riƙa ganin jama'a babu takunkumin fuska a yayin da suke cunkushe suna mu'amala cikin annashuwa, ba tare yin la'akari da abubuwan da za su iya biyo baya ba.

Gangamin dai ya ɗauki hankulan masu zanga-zanga da dama, da akasarinsu matasa ne masu jini a jika da suka yi fatali da ƙa'idojin da hukumomi suka shimfiɗa game da yaɗuwar ƙwayar cutar korona take ci gaba da haifar da barazana a ƙasashen duniya.

Waɗannan ƙa'idoji dai sun haɗa da sanya takunkumin fuska, yin nesa da juna, gujewa taruwar jama'a da ya wuce misali, wanke hannaye da sinadarin kashe ƙwayoyin cuta da kuma sabulu akai-akai.

Me ya jawo zanga-zangar?

Zanga-zangar ta EndSars dai wacce ke ci gaba da gudana a wasu biranen Najeriyar, ta tilasta rufe makarantu a fadin jihar Legas ta rufe makarantu a faɗin jihar don kauce wa barazanar da yara ka iya fuskanta.

Tun bayan da zanga-zangar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa inda ta dauki sabon salo, wasu 'yan kasar da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum suka fara nuna fargabar abubuwan da ka iya biyo bayan, tare da yin kira ga shugaban Najeriyar dauki mataki kan lamarin.

Dama dai tun a makon farko na zanga-zangar ne shugaban kasar ya yi magana tare da daukar matakin rusa rundunar ta Sars, wadda ita ce buƙatar masu zanga-zangar.

Sai dai bayan rushe rundunar ta SARS ne masu zanga-zangar suke ce an yi baya babu zane tun da gwamnati ta kafa sabuwar runduna mai suna SWAT don maye gurbinta, inda suka ƙara ƙaimi wajen ci gaba da zanga-zangar kiran da sai an rushe ta ita ma, sai dai har yanzu Shugaba Buhari bai ƙara cewa uffan ba.

Lamarin dai ya jefa mutane cikin halin fargaba a biranen Legas da Abuja inda zanga-zangar ke ci gaba da bazuwa, lamarin da ke saka mazauna biranen cikin tasku na takurawa zirga-zirga da walwalarsu, inda a ranar Litinin da yamma zanga-zangar ta rikiɗe zuwa rikici a wasu unguwannin.

Dubban masu zanga-zanga ne suka halarci gangamin a kawo karsen rundunar ta SARS da aka shafe kusan makonni biyu ana gudanarwa.

An samu tashe-tashen hankula a birane da dama na kasar yayin da wannan gangami na nuna adawa da cin zarafi da mugunta da 'yan sanda da ke ci gaba da haifarwa.

An kuma raunata masu zanga-zanga da dama ne aka jikkata a lokacin taron gangamin, kana kungiyar kare hakkin bil adama ta 'Amnesty International' ta ce an hallaka mutane 15 - duk da cewa hukumomi sun musanta wannan adadi.

Da alamu matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na soke rundunar ta SARS bai gamsar da masu zanga-zangar ba, bayan da suka fadada ta zuwa wasu bukatu game da yanayin tafiyar da shugabanci a kasar.