Zaɓen Edo: Abin da ya kamata ku sani kan zaɓen na 19 ga Satumbar 2020

A ranar 19 ga watan Satumban 2020 ne za a fara zaɓen gwamna a jihar Edo da ke kudancin Najeriya, inda a ranar ne duk wanda ya kai shekarun zaɓe zai fito domin jefa ƙuri'arsa ga wanda yake so ya jagoranci jihar a matsayin gwamna na shekara huɗu masu zuwa.
Tafiya har zuwa wannan lokaci a jihar ta Edo ba ta kasance mai sauƙi ba, domin Edo da Jihar Bayelsa ne kaɗai jihohin kudu maso kudancin Najeriya da ba a yi zaɓen gwamna ba a lokacin da sauran jihohin ƙasar ke yi.
Za a gudanar da zaɓen ne a ranar 19 ga watan Satumban 2020.
Mutum 2,210,534 - waɗanda suka kai ko suka haura shekara 18 - ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta tabbatar da sun yi rajistar zaɓe a jihar kuma suna da haƙƙin kaɗa ƙuri'a.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa za a gudanar da zaɓen Edo a yanzu?
A yadda tsarin Najeriya yake, kamata ya yi a ce duka jihohin Najeriya 36 sun gudanar da zaɓensu a rana ɗaya, sai dai ban da jihohin Edo da Ondo da Anambra da Bayelsa da Osun da Kogi.
Matsalolin da suka biyo bayan zaɓen Gwamna Oserheimen Osunbor a 2007 a jihar ta Edo ya sa aka ɗaukaka ƙara zuwa kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta jihar.
Bayan ja-in-ja da aka sha tsakanin Gwamna Osunbor da kuma abokin takararsa Adams Oshiomhole, a ranar 11 ga watan Nuwambar 2008 Kotun Ƙolin Najeriya ta ayyana Oshiomhole a matsayin gwamnan Edo.
Wannan hukuncin da Kotun Ƙolin ta yanke ya ja zaɓen Edo ya rinƙa shan bamban da na sauran jihohin Najeriya.
Manyan 'yan takarar da za su kara a zaɓen Gwamnan Edo
Kamar yadda hukumar INEC ta bayyana, jam'iyyu 15 ne za su kara a zaɓen gwaman jihar ta Edo.
Cikin jam'iyyu 15 ɗin, 'yan takara biyu da su ne kan gaba sun haɗa da Godwin Obaseki na Jam'iyyar PDP, wanda kuma shi ne gwamnan jihar a halin yanzu, sai kuma Fasto Osagie Ize-Iyamu na Jam'iyyar APC.
Rashin jituwa da aka samu tsakanin Obaseki da tsohon shugaban APC kuma tsohon Gwamnan Edo Adams Oshiomhole, ya sa aka hana Obaseki tikitin tsayawa takara a APC sakamakon zarginsa da cewa ba shi da takardun makaranta.
A kwanakin baya ne Godwin Obaseki ya bar APC ya koma PDP bayan hana shi tikitin tsayawa takarar, inda shi kuma Ize-Iyamu ya bar PDP ya koma APC.
Fasto Ize-Iyamu dai na samun goyon baya daga Adams Oshiomhole da kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa zaɓen Edo ke da muhimmanci?
Zaɓen jihar Edo na zagaye da ce-ce-ku-ce da kuma ruɗani irin na siyasa.
Domin fahimtar me ya sa siyasa ta ɗauki zafi a jihar, ya kamata a gane cewa siyasa tamkar wani wasa ne na wa ya fi yawan jama'a. Duk Jam'iyyar da ta kasance ta fi yawan jihohi a Najeriya, to lallai ita ce kan gaba.
Cikin jihohi shida na yankin kudu maso kudancin Najeriya, jihar Edo ce kaɗai ke da gwamna ɗan APC, a kwanakin baya kuma gwamnan ya tsallaka zuwa PDP, hakan na nufin PDP ce ke da kudu maso kudancin Najeriya baki ɗaya.
Hakan kuma ya sa yawan jihohin da APC ke riƙe da su a Najeriya gaba ɗaya sun koma 20 daga 21.

Edo za ta kasance filin daga
Edo ta zama filin daga ga jam'iyyun siyasa biyu mafi ƙarfi a Najeriya.
Yayin da Jam'iyya mai mulki ta APC za ta mayar da hankali wajen ganin cewa ta ƙwato kujerar da ta rasa, PDP kuma za ta yi ƙoƙari ta ga cewa ta ci gaba da riƙe duka kujerun da suka shiga hannunta a jihar.
Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike, a wata hira da ya yi da gidan talabajin na AIT a ƙasar ya bayyana yadda jam'iyyar adawa ke ɗaukar wannan zaɓe mai zuwa.
Wike ya bayyana cewa "zaɓen Edo ba wai na Obaseki bane, zaɓe ne na mutanen kudu maso kudancin Najeriya".

Asalin hoton, Twitter/EUinNigeria
Ba wai PDP kaɗai ke da irin wannan tunanin na Obaseki ba, sakamakon ita kanta APC ta bayyana cewa Obaseki bai kasance wata barazana ba ga nasararsu.
Tsohon Shugaban APC, Adams Oshiomhole, wanda kuma yana daga cikin masu faɗa-a-ji a siyasar Edo ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa Obaseki ba barazana ba ne ga jam'iyyarsa ko kuma zaɓen jihar.
"Ta yaya zai zama barazana? Ta yaya mutumin da bai cancanci ya tsaya takara ba zai zama barazana? Ta yaya dodon koɗi zai zama barazana ga gasar da damisoshi?"
Rikicin zaɓe
Tuni ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama suka fara nuna damuwarsu cewa akwai yiwuwar a samu rikici a zaɓen da za a yi ranar 19 ga watan Satumba.
Tun kafin wannan zaɓen, an yi ta yin rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyun da kuma kalamai masu zafi a tsakaninsu, inda ake kuma samun fargaba sosai a jihar.
Da ma kusan kowane zaɓe a Najeriya ana samun rikice-rikice da asarar rayuka.










