Shin ‘yan Boko Haram ne suka kashe sojoji a Katsina?

Nigerian soldier in Nigeria's north east

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Bayan harin da ƴan fashin daji suka kai kan sojojin Najeriya a jihar Katsina akwai rahotanni masu karo da juna kan artabun da ya janyo mutuwar sojojin.

Mazauna yankin sun ce a kalla sojoji 16 aka kashe da kuma 'yan fashi da ba a san adadinsu ba, yayin da rundunar sojin ƙasar kuwa cewa ta yi dakarunta hudu ne suka mutu.

Artabun ya auku ne a kauyen Shimfida na jihar Katsina da ke arewa maso yammacin kasar.

Tuni wani mai magana da yawun sojan na Najeriya ya ce sojoji hudu ne aka kashe yayin da suka halaka 'yan fashi 17 a artabun da aka yi a karshen mako.

Amma wani mazaunin karkarar da ya shaida artabun ya sanar da BBC cewa, "an kashe soja kamar 15, yayin da wajen 28 da suka sami rauni".

Mutumin ya kuma ce bai tabbatar da yawan ƴan fashin dajin da sojojin suka kashe ba: "An kashe ɓarayin da dama, amma ba mu da bayani kan iya ɓarawon da aka kashe."

Ya ƙara da cewa sauran sojojin da suka tsira da rayukansu na cikin daji inda suka ci gaba da fafatawa da ƴan fashin.

Wadanna alƙaluman da ake yawo da su, sun nuna rashin alƙiblar da ke tsakanin abin da hukumomin tsaro a Najeriya ke cewa da abin da wasu ƴan ƙasar ke cewa rufa-rufa ne hukumomin sojan ƙasar ke son yi.

Wannan layi ne

Ainihin sojojin Najeriya nawa aka kashe?

Barista Bulama Bukarti mai bincike kan ayyukan ta'addanci ne kuma mai sharhi ne kan al'amuran tsaro a yankin arewa maso yammacin Afirka.

Barista Bukarti na cikin waɗanda suka fara wallafa hotunan sojojin da aka kashe da bayanai kan artabun da ya auku tsakanin sojojin da ƴan fashin daji.

BBC ta tambaye shi sahihancin alkaluman yawan sojojin da ya ce yan fashin sun kashe:

"Gaskiya ce na wallafa hotunan gawarwakin sojin da aka kashe tun ma kafin rundunar sojin Najeriya ta wallafa bayanan artabun. Kuma na sami hotunan ne ta hanyar wani ma'aikaci wanda yana cikin wadanda aka kai gawarwakin sojojin bayan an kwashe su daga inda aka kashe su."

Chadian soldiers have been fighting Boko Haram militants since 2015

Asalin hoton, AFP

Bukarti ya ce, "na ga akalla gawarwakin sojoji 15 kuma ya aiko min da jawabi cewa an kashe sojoji tsakanin 16 ne zuwa 20."

"Ka ga kenan a ce mutum uku aka kashe ba haka batun yake ba," in ji shi.

Ga sakon da Bulama Bukarti ya wallafa a shafinsa na tuwita:

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Wannan layi ne

Shin akwai alaƙa tsakanin ƴan fashin daji da Boko Haram?

Bukarti ya shaida wa BBC cewa "A sanarwar da rundunar soji suka fitar da kuma bayanan da na tattara kan batun, an yi wannan artabun ne da masu ɗauke da mukamai daga ɓangaren wani babban kwamanda da ake kira Ɗangote, kuma shi Dangoten nan ba shi da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram."

Ya ce ɓangaren Dogo Giɗe ne ake ganin ke da alaƙa da Boko Haram.

"Saboda haka, kana iya cewa masu ɗauke da makamai ne suka yi wannan ɗauki ba daɗin da sojojin Najeriya," in ji shi.

Ba abin mamaki ba ne cewa akwai alaƙa tsakanin kungiyoyi ƴan fashi da na ƴan ta'adda.

Amma Bulama Bukarti na ganin ƙungiyar masu aikata laifi na iya zama alaƙaƙai ga hukumomin tsaro:

"Idan aka bar ƙungiyar masu aikata laifi ta yi ƙarfi, ta kuma tara kuɗaɗe, har kuma ta daɗe tana yaƙi, to ba shakka tana iya gogewar da za ta yi irin wannan ɗauki ba daɗin da illa kamar yadda aka ruwaito."

Ya bayar da misali ga ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi ta ƙasar Mexico, "kaga sun fi ƙarfin gwamnatin ƙasar, inda ko shugabansu aka kama, sai su je gidan yarin komai girmansa su balle shi su fid da shugabansu."

Ya kara da cewa, "Tilas aka tafi da wani shugaban ƙungiyar Amurka domin ƙasar ta Mexico ta kasa tsare shi a kurkukunta. Kuma a Amurkan ma sun taba zuwa can sun balle gidan yarin da ka tsare shugaban nasu har suka tsere da shi."

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

'An yi sake ɗan zaki ya fara girma'

Chadian soldiers

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyoyin da ke dauke da makamai a yankin arewa maso yammacin Najeriya sun yi karfi sosai har ta kai ga sun kusa fin ƙarfin dakarun sojin ƙasar.

Bulama Bukarti: "Idan mutum ya kasance fashi yake yi ko garkuwa da mutane, to kowane sisi ko kwabo da ka ba shi domin fansho wadanda yayi garkuwa da su, to fa ƙara ƙarfi yake yi."

Ya ce ɗan fashin zai yi amfani da kuɗin ne "ya sayo makamai domin sune jarin shi, motoci zai sayo da kudin domin sune jarin shi."

Ya kuma ce daga nan ƙara gogewa yake yi, "kuma wannan na iya illata ƙasa matuƙar illatawa."

Bukarti ya kuma gargaɗi hukumomin Najeriya da su ɗauki matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma da muhimmanci sosai.

"Yanzu dai ɗan zaki ya fara girma amma ba za a ce an makara ba, lallai ne gwamnati ta tashi ta yi kamar tana yi," in ji shi.

Ya bukaci gwamnati ta ƙaddamar da yaƙi, "kan wadannan ƴan fashin da manyan makamai ta hanyar tara bayanan sirri masu kyau".

Ya kuma nemi hukumomi su riƙa zaburar da sojojinmu ta hanyar girmama sojojin da suka rasa rayukansu maimakon a riƙa boye su, da kuma samar mu su da isassun kayan aiki tare da kula da lafiyarsu da walwalarsu domin a nuna mu su cewa suna da muhimmanci.

Wannan layi ne