Harin Katsina: 'Yadda bam ya kashe 'ya'yana huɗu a Yammama'

Mahaifin yaran ya ce ya dangana

Asalin hoton, Muhammad Garba

Bayanan hoto, Mahaifin yaran ya ce ya dangana

Mahaifin wasu daga cikin yaran da suka mutu sakamakon tashin wani abu da ake zargin bam ne a jihar Katsina ya bayyana matukar takaicinsa kan abin da ya faru.

A hirarsa da BBC, Iliya Adamu, ya ce "yaran guda bakwai ne...lamarin ya rutsa da su. Huɗu sun rasu, uku suna asibiti."

Mahaifin yaran Iliya Adamu ya ce an aiki yaran ne su je su yiwo ciyawa amma sai labarin mutuwarsu suka ji.

"Abin da ya faru dai shi ne an kira ni an ce ga gawarwakinsu...amma daga gida mun bari a kan cewa sun tafi yin ciyawa. An wayi gari da safe sun zo sun ce min 'za a tafi gona?', na ce a'a su je su samo dan abin da za su kashe. Abin da muka yi da su kenan."

Ya kara da cewa babban dansa ne kawai zai yi wa gidansu ciyawa, amma sauran "ba kuma a tura su ciyawa haka kurum suka bi shi saboda karar kwana."

A cewarsa, ya dangana saboda yana sa ran yaran suna Aljanna kuma za su cece shi ranar Al-qiyama.

Ya kara da cewar mai dakinsa ta fi shi dauriya kan rasuwar 'ya'yan nasu, yana mai cewa "ni da na zo ma sai da na yi kuka, amma ita ba ta yi kuka ba. Ta mika al'amarinta ga Allah."

Short presentational grey line

Lamarin da ya faru

Abin ya fashe ne ranar Asabar lokacin da yaran suka dauke shi a hannunsu a ƙauyen Yammama da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Mai magana da yawun 'yan sanda reshen jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar wa BBC da cewa yara biyar suka mutu sai kuma wasu yaran shida suka raunata.

Da misalin ƙarfe 11:30 na safe, DPO na 'yan sanda da ke Malumfashi ya ce sun ji "ƙarar wani abu a gonar wani Alhaji Hussaini Mai Ƙwai".

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce, " abin da ya fashe din ya kashe yara biyar na wani mai suna Alhaji Adamu Yammama, kuma yara shida da ke zaune a ƙarƙashin wata bishiya sun ji rauni".

Gambo Isah ya shaida wa BBC cewa yaran sun je gona ne domin ɗebo ciyawa da za su bai wa dabbobi sai wannan lamari ya faru, ya ce abin da ya fashe zai iya yiwuwa gurneti ce ko kuma wani abin fashewa.

Lamarin ya tayar da hankalin al'ummar garin

Asalin hoton, Muhammad Garba

Bayanan hoto, Lamarin ya tayar da hankalin al'ummar garin