Gwamna Matawalle: Ko matakin musayar shanu da AK47 a Zamfara ya yi daidai?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce za ta ba ɓarayin daji saniya biyu kan kowace bindiga ɗaya da suka miƙa, a wani mataki na yunkurin kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.
Gwamnan jihar Bello Matawale ya bayyana shirin ne yayin da ya karɓi baƙuncin Babban Sifeto na 'ƴan sandan Najeriya Mohammed Adamu da Shugaban hukumar tsaron farin kaya DSS Yusuf Bichi waɗanda Shugaban Najeriya ya tura jihar saboda tabarbarewar tsaro.
To sai dai gwamnatin na ci gaba da jan hankulan mutane a ciki da wajen Najeriya, yayin da masana ke cewa a yi hattara.
Kwamishinan tsaro na jihar Zamfaran Abubakar ya tabbatar wa da BBC cewa gwamnan ya bujiro da wannan mataki ne don rage yawaitar makamai a hannun mutane.
A cewar gwamnan, za su bai wa ɓarayin shanun biyu-biyu ne sakamakon Fulani sun fi buƙatar su a kan tsabar kuɗi.
'Wanne irin shanu ne guda biyu za su yi dai-dai da kuɗin AK-47?'
Tun bayan da gwamnan ya bayyana wannan mataki al'ummar jihar ta Zamfara, har ma da na wajenta suke tofa albarkacin bakinsu a kan matakin.
A shafinmu na BBC Hausa Facebook wani mai suna Mubarak A. Suleiman ya nemi sanin abin da hukumomi za su yi wa waɗanda barayin dajin suka afka wa.
"Talakawan da aka kashe masu ƴan uwa da iyayensu kuma me zaku basu? Sannan wadanda aka kore ma shanu da ƙone dukiyoyinsu su kuma fa?"
Ya kuma nemi sanin abin da gwamnatin Zamfara ta tanadar musu, kuma ya ce yin sasanci da ɓarayin dajin ba shi ne zai kawo zaman lafiya ba.
Safiyyat Abdulhamid daga Kumasi Ghana ta yi tambayoyi ne ga hukumomin jihar, "Wai shin ba a iya fatattakar su ne? Ko dai gwamnati ba ta da kayan yaki ne sosai?" I
Shi kuwa Aminu Yaro Na-abba yana kallon batun ne daga fuskar musayar makamai da shanu.
"Nawa ake sayar da AK-47? Sannan wanne irin shanu ne guda biyu za su yi dai-dai da kuɗin AK-47?"
Aliyu Sarkin Gidan Aliyu kuwa ya soki matakin ne gaba dayansa: "A gaskiya wannan ba mafita ba ce a ce wai gwamnati taki cewa za ta ba wa ƴan ta'ada wani abu. Amma ba su damar cigaba da yin ta'addanci ke nan."
Ya ce gwamnati na da ƙarfin da za ta ga bayan duk wani ɗan ta'ada a ƙasar nan muddin suka tsaya tsakaninsu da Allah.
To sai dai wasu kuwa na ganin matakin na Gwamna Matawalle abin a yaba ne, domin abinda zai iya ke nan.
Da yake bayyana ra'ayinsa kan batun Suleiman Sani Aliyu Maisango cewa ya yi bai ga laifin shi ba. "Ba shi da iko akan jami'an tsaro a matsayin shi na governor. Buhari kawai yake da su... don haka ya zama dole ya neme ko wace hanya da yake gani zai kawo wa jaharshi saukin wanan bala'in.

Ba lallai ba ne sulhu yayi tasiri
Baya ga jama'a batun ya kuma dauki hankulan masu fashin baki kan al'amurn tsaro da aikata miyagun laifuka.
Malam Abdullahi Yelwa, malami ne a Sashen Nazarin Muggan Ɗabi'u da Daƙile Yaɗuwarsu a Makarantar Kimiyya da Ƙere-ƙere ta Abubakar Tatari Ali da ke Bauchi, kuma masanin harkar tsaro ne.
Ya ce matakin gwamnatin abu ne mai kyau, amma ba lallai ba ne kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
"Wannan ƙoƙari abin a yaba ne. Amma ba lallai ba ne a sami abin da ake so," in ji Malam Abdullahi Yelwa.
Ya ce kamata ya yi a duba darajar dabbobin da za a yi musayarsu da darajar bindigogin na AK-47, "idan aka kamanta su da kuɗin da 'ƴan ta'adda ke kashewa wajen sayen bindigogin".
A ganinsa ɓarayin dajin sun mayar da hare-haren da suke yi harkar neman kudi.
"Abu ne mai wuya wanda ya saba da samun kuɗin banza ta hanyar yin fashi ya haƙura da saniya biyu. Bindigar nan na iya kawo musu shanu 100."
Wasu masharhanta kuwa na da ra'ayin cewa matakin ba zai kawo karshen hare-haren ba.
A cewar wani lauya mai zaman kansa dake bincike kan kungiyoyin 'yan ta'adda Audu Bulam Bukarti, idan har gwamnati ta bai wa mahara tukwici saboda mika bindiga, to me za a yi wa mutanen da ake kashewa 'yan uwansu?

"Shin riba suka ci ko faɗuwa suka yi?"
Batu na biyu kuma da ke tasowa shi ne ko akwai wata hanya da gwamnati za ta iya bi domin warware matsalar in ba ta lalama ba?
A tsarin mulkin Najeriya, dukkan jami'an tsaro kamar sojoji da ƴan sanda na ƙarkashin ikon gwamnatin tarayya ne.
Mallam Yelwa na ganin, "wannan na nufin gwamnatocin jihohi ba su da zaɓi kan batun, saboda ba su da iko kan jami'an tsaro."
Su ma jami'an tsaro ba su samu wata nasarar a zo a gani ba, duk da cewa sun shiga yankin da kayan yaƙi. Amma ya ce duk da haka akwai wasu matsalolin da suke fuskanta na rashin isassun kayan aiki da bayanan sirri da za su taimaka musu.

Gwamnatocin da suka shuɗe a jihar sun riƙa kama wasu fitattun mutane, ciki har da masu riƙe da sarautun gargajiya.
"Tunanin da ya kamata a yi shi ne, su waɗannan ɓarayin sun san mutane idan mutane ba su san su ba. A wasu lokuta kuma hukumomi sun san su, jama'a ma sun san su."
Ya ce kuskure ne irin waɗannan da suka ja daga da hukumomi, a koma ana ba su hakuri kuma hakan yana nuna gazawar gwamnati ne.
"Amma waɗanda ke boye, kuma suka miƙa kansu har suka tuba - babu laifi a yi sulhu da su. Matakin sulhu na iya taimakawa ganin cewa jami'an tsaro ma ba su iya kare kansu ba, ballantana su kare al'umma."

Ina bambancin Katsina da Zamfara?
Wata jihar da ta gwada yin sullhu gabanin Zamfara ita ce jihar Katsina, inda a baya gwamnatin ta shiga yarjejeniya da masu kai hare-hare da satar shanu da garkuwa da mutane da nufin kawo karshen matsalar.
To sai dai haka ba ta kai ga cimma ruwa ba.
Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ma ya ɗauki irin wannan matakin na yin sulhu da ɓarayin daji da suka addabi jiharsa, amma daga baya ya ce ya yi nadama saboda "ɓarayin dajin sun ci amanar mu".

Asalin hoton, @GOVERNORMASARI
A wata hira da ya yi da BBC Hausa Gwamna Masari ce waɗanda ba su yarda da sulhun ba ne suka dawo suna kai hare-hare, kuma yanzu a cewar gwamnan jami'an tsaro ne ya kamata su yi sulhu da ɓarayi.
"Mun bi hanyar sulhu don samun zaman lafiya kuma mun yi iya bakin kokarinmu amma zaman lafiya ya gagara," in ji gwamnan Masari.
Wasu gwamnatocin ma sun bi wannan hanyar, ciki har da tsohon Gwamna Abdulaziz Yari na jihar ta Zamfara amma duk da haka matsalar tsaron ta ki ƙarewa.
Me ya sa gwamnan na Zamfara zai bi wannan hanyar duk da sakamako maras daɗin ji da aka samu a makwabciyar jihar Katsina?
Malam Abdullahi Yelwa na ganin rashin mafita ce ke tilasta wa gwamnatoci ɗaukar irin wannan matakin.
"Ya tabbata cewa salon amfani da ƙarfi da yaji bai biya buƙata ba a Zamfara har ma da wasu jihohi kamar Katsina, sakamakon ɓata lokaci da aka yi gabanin ɗaukan matakin soji kan ɓarayin har ta kai ga sun yi ƙarfi."
"Abu ne mai kyau a yi sulhu, amma sai an bi hanyar da za ta biya buƙata, ganin cewa irin wannan tsarin na sulhu tsakanin gwamnatoci da ɓarayin a wasu jihohi kamar Katsina bai biya bukata ba," in ji shi.

Saboda haka ina mafita?
Malam Yelwa na ganin an bar gyara a baya:
"Ya kamata a nemi hanyar magance matsalar tun daga tushe, domin hana aukuwarsa shi ne abin da yafi kyau, a maimakon neman yin sulhu ko yaƙar wadannan miyagun."
Ya ƙara da cewa, "Babban yaƙi shi ne samar wa mutane ayyukan yi, da inganta rayuwarsu da samar da yanayin da mutane za su yi rayuwa cikin walwala amma bisa doka da oda."
Yana ganin idan aka tabbatar da adalci, yawancin matsalolin tsaro za su kau da kawunansu daga yankin gaba ɗaya.
"Uwa-uba tilas a samar da hanyoyin da gwamnatoci za su yi tasiri a rayuwar mutane, ƙananan hukumomi na neman a tallafa mu su domin kawar da fitintunu tsakanin al'umomin yankin."
Yana ganin duk ƙoƙarin da ake yi kamar an kashe maciji ne ba a sare kansa ba.
"Sulhu da ƴan bindiga da ɓarayin shanu da ma waɗanda ke satar mutane domin karbar kuɗin fansa mataki ne da muke kira na fargar jaji."
Yana kuma kallon yunƙurin yin sulhu da gwamantin Zamfara ke yi cewa ba lallai ba ne ya yi tasiri, ai dai yana nuna himma da damuwa da ƙokarin gwamnan jihar wajen kawar da matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin ƙasar.












