Boko Haram: Me zai faru idan 'yan bindigar Zamfara suka amsa gayyatar kungiyar?

Bayanan sautiBarrister Audu Bulama Bukarti

Latsa wannan alamar lasifikar da ke sama domin sauraron Barrister Bulama Bukarti

Masana harkar tsaro a ciki da wajen Najeriya sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da gayyatar da kungiyar Boko Haram ta yi wa barayin daji da ke cin karensu babu babbaka a arewa maso yammacin Najeriya.

Kungiyar Boko Haram dai ta mika wa 'yan bindigar wannan gayyata ne a cikin wani bidiyo mai tsawon minti 13 da kungiyar ta fitar a baya-baya nan.

Bidiyon dai ya nuna wasu mayakan kungiyar ta Boko Haram guda hudu suna yi wa 'yan uwansu da ke jihohin Naija da Zamfara jawabi da harsuna guda hudu wato na Ingilishi da Hausa da Faransanci da kuma Fulatanci da su ci gaba da aiwatar da manufofin kungiyar.

Masana dai na yi wa bidiyon kallon yunkurin kungiyar Boko Haram na neman goyon bayan wasu mutane masu irin akidarta.

Ko 'yan bindigar za su karbi saƙon Boko Haram?

Barrister Audu Bulama Bukarti, wani lauya kuma mai bincike kan ayyukan 'yan ta'adda a yankin Sahel, ya ce " wannan ba shi ne bidiyon farko ba domin na farko an yi shi ne a tun farkon shekara 2020, inda Shekau ya ce wasu sun tura masa sako kan suna son su shiga kungiyar.

Saboda haka idan har ta tabbata cewa su ne suka nemi a yi musu bayanai kan akidun kungiyar to kenan sun karbi kiran kungiyar."

Bulama Bukarti ya kara da cewa " bayanan da suka samu da ba a hikakance ba sun nuna tun ba yanzu ba akwai kawance tsakanin Boko Haram da 'yan bindiga da ke arewa maso yammacin Najeriya ya dade."

Tasirin kawancen Boko Haram da 'yan bindiga

Barrister Bulama Bukarti ya ce idan har ta tabbata bangarorin biyu sun amince su yi aiki tare to babu abun da hakan zai haifar illa sake jefa yankin na arewa maso yammaci cikin halin ha'ula'i.

"Wato akwai mummunan hatsari dama zubar da jini kasancewar an cusa wa mutanen da suke kashe jama'a da sace dukiyoyinsu ba gaira ba dalili, akidar cewa idan suka kashe sun yi jihadi sannan idan suka mutu a kan hanyar sun yi shahada."

Rahotanni dai sun nuna cewa 'yan bindiga dadi a arewacin Najeriya sun kashe mutum kimanin 8000 a tsawon shekaru 10.

Bulama Bukarti ya ce "al'amarin zai kasance mummuna inda kuma ya ja hankalin shugabannin Najeriya da su farka wajen tunkarar wadannan kungiyo.

Mafita

NPF

Asalin hoton, NPF

Bayanan hoto, Rundunar 'yan sandan Najeriya ta sha shan alwashin ganin bayan 'yan ta'adda a arewacin Najeriya

Barrister Audu Bulama Bukarti ya fitar da wasu hanyoyin guda biyu da ya ce idan aka bi su za a shawo kan matsalar tsaro a arewacin kasar:

  • Yin amfani da karfin soji a arewa maso gabashi da maso yammacin Najeriya domin hana bangarorin biyun numfashi ta ko'ina.
  • Lallai ne gwamnati ta fito da hanyoyin dakile sakonnin da kungiyoyin suke aikewa da shi kasancewar hakan ka iya jan hankalin matasa musamman a yanayin da ake ciki na matsalar tsaron da tasa matasa da dama suka yanke kauna da rayuwa.
  • Ya kamata a shigar da malamai cikin al'amarin domin yi wa matasa huduba kan illar shiga kungiyoyin ta'addanci.
Short presentational grey line

Bayanai dai sun nuna akwai kungiyoyin 'yan bindiga fiye da guda biyar da ke karakaina a dazukan arewacin Najeriya, inda aka ce sun yi kawance wajen kai hare-hare masu muni a arewacin kasar, a baya-bayan nan.

A 'yan makonnin da suka gabata ne mahara suka shiga wasu kauyuka a jihar Sokoto inda a tashin farko suka kashe mutum fiye da 70.

A baya dai an ce bangarorin 'yan bindigar ba sa ga maciji da juna.

Yawaitar hare-haren 'yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasar ne ya tayar wa da al'ummar yankin hankali inda suka gudanar da zanga-zanga ciki har da jihar Katsina wadda daga nan Shugaba Muhamamdu Buhari ya fito.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha nanata aniyarsa na samar da tsaro a kasar mai dorewa, wani al'amari da har yanzu 'yan kasar musamman ma na arewaci ke dakon gani.