Katsina: 'Yan bindiga sun kashe sojoji a jihar

..

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 1

'Yan bindiga sun hallaka sojoji uku yayin wata arangama a wani daji da ke ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina a Najeriya.

A wata sanarwa da hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar a ranar Lahadi, ta ce lamarin ya faru ne yayin da Rundunar Sahel Sanity tare da haɗin gwiwar sojojin sama suka kutsa cikin dajin Jibiya domin hallaka 'yan bindigar.

Sojojin sun bayyana nasarar kashe 'yan bindiga 17 inda kuma da dama suka tsere da harbin bindiga a jikinsu.

Sai dai ɗaya daga cikin masu sharhi kan tsaro a Najeriya wato Barrister Bulama Bukarti, ya bayyana cewa sojojin da aka kashe a arangamar sun kai 20.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twiiter, ya ce yana da hotunan irin mummunan kisan da aka yi wa sojojin.

A Najeriya dai ana yawan zargin sojojin ƙasar da taƙaita adadin ɓarnar da ake yi musu, amma sau da dama sojojin kan musanta wannan zargi.

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da 'yan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a arewacin Najeriya.

Rahotanni daga wasu ƙauyuka na jihar irin su Batsari da Dutsinma da Jibiya da Faskari na cewa kaso mai yawa na manoman yankin ba su yi sharar gona ba a wannan shekara ballantana niyyar fara noma sakamakon matsi da suke fuskanta daga 'yan bindiga.