Boko Haram: Shin ƙungiyar ta ɓulla a jihar Neja ne?

Asalin hoton, Getty Images
Wani mai bincike kan ƙungiyoyin 'yan ta-da-ƙayar-baya a cibiyar Tony Blair Institute da ke Burtaniya ya ce saƙon da Boko Haram ta fitar inda aka ga wani mayaƙin ƙungiyar na bayyana kansa a matsayin kakakinta a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya babbar barazana ce ga tsaron ƙasar.
An dai san ƙungiyar ta fi ƙarfi ne a arewa-maso-gabashin ƙasar, tun bayan da tasirinta a wasu jihohin ƙasar ya ragu.
Amma Barista Bulama Bukarti, mai bincike kan ƙungiyoyi masu ta da ƙayar baya a cibiyar ta Tony Blair, ya bayyana wa BBC cewa idan ta tabbata ƙungiyar na da sansani a jihar Neja, za ta iya kai hari a Abuja da wasu jihohin da ke maƙwabtaka da ita.
A saƙon na bidiyo mai tsawon minti shida, wasu mayaƙan Boko Haram bakwai sun yi jawabai inda suke iƙirarin cewa suna aiko da saƙon ne daga sassa daban-daban.
Wasunsu sun ce suna magana ne daga Kamaru da dajin Sambisa da kuma yankin tafkin Chadi.
Amma saƙon da ya fi jan hankali shi ne na mayaƙin da ya yi iƙirari cewa shi ne kakakin kungiyar kuma yana magana be ne daga jihar ta Neja.

Asalin hoton, Getty Images
Sahihancin wannan saƙon bidiyon
Dukkan mayaƙan sun fara da miƙa sakon gaisuwa ga shugabansu Abubakar Shekau, kuma sun yi barazanar kai wasu munanan hare-hare a kwanaki masu zuwa.
Bulama Bukarti na ganin saƙon daga kungiyar Boko Haram yake:
"Tabbas wannan faifan bidiyo daga Boko Haram yake, wato bangaren Abubakar Shekau. Sai dai ba mu tabbatar ko daga jihar Neja yake aiko da saƙon ba, ko kuwa a wani wuri na daban aka dauki bidiyon amma yake barazana, yana ƙarya cewa yana jihar Neja ne."
"A gaskiya idan ta tabbata cewa akwai mayaƙan Boko Haram a jihar Neja, to akwai hatsari mai matuƙar girma," in ji Bulama Bukarti.
"Jihar Neja ita ce jiha ta biyu a girma ta ɓangaren fadin kasa a Najeriya, kuma tana da daji mai duhu da duwatsu masu yawa. Dajin ya shiga jihar Kaduna kuma ya haɗa da dazuzukan da ke jihohin Katsina da Zamfara har zuwa Sokoto."
Barista Bukarti ta ce: "Idan mayaƙan Boko Haram suka yi karfi a dazukanta, to ba abu ne mai wuya ba su kai hare-hare babban birnin tarayyar Najeriya ba."

Asalin hoton, Getty Images
Wani batu kuma shi ne na sabon salon da ƙungiyar ke amfani da shi wajen mika saƙonninta.
A shekarun baya, shugabanta ne kawai aka sani yana magana da yawunta, amma sai yanzu aka ga wasu mayaƙanta na mika saƙonni a madadinta.
Bulama Bukarti ya ce: "Ina ganin matasa sun gane cewa shi Abubakar Shekau mutum ne wanda ba shi da tausayi, maras imani wanda ke da ƙishin kashe bayin Allah wadanda ba su ji ba, ba su gani ba."
Ya kuma ce wannan sabuwar dabara ce da ƙungiyar ta fito da ita ta amfani da wasu muryoyi da fuskokin da matasa ba su saba da su ba - domin sun dawo daga rakiyar Abubakar Shekau.
Ya kuma ce fatan Boko Haram shi ne ta yaudari matasa domin su shiga ƙungiyar.











