Coronavirus: Ba dukkan mace-macen Kano ne suke da alaka da cutar ba - Dr. Gwarzo

Kwamitin da shugaban Najeriya ya aike Kano domin shawo kan yaduwar annobar korona ya musanta rahotannin da ake yadawa a kansa kan mace-macen jihar.
Tun a yammacin Lahadi wasu kafafan yadda labaran kasar ke cewa kwamitin ya danganta karuwar mace-macen jihar da korona.
Sai dai shugaban kwamitin, Dr. Nasir Sanu Gwarzo ya shaida wa BBC cewa ba haka abin yake ba.
Dr. Gwarzo ya ce da alama ba a fahimci bayanansa ba, domin shi maganar da yake ba ta da alaka da wadannan bayanai da ake yadawa.
"Na yi maganar kashi 80 cikin 100 amma ba a kan mace-mace ba, na yi wannan maganar ne kan samfurin da aka karba da kuma yanayin tasirin cutar a jikin dan Adam".

Likitan ya ce har yanzu suna kan bincike don haka babu wannan maganar, ko wani sahihin bayani.
Amma a cewarsa kwamitinsu ya gano akwai wasu mace-mace da alamominsu ake iya dangatawa da cutar korona.
A cewarsa har yanzu suna kan karbar bayanai kuma aikin nasu mataki-mataki ne don haka watakil sai nan da mako guda komai zai kammala.
"Aikin bincikenmu ya yi nisa, amma har yanzu muna kan aiki, mun bai wa ma'aikata horo an turasu har makabartu."
Sai dai ya ce idan aka duba wadanda suka mutu a baya-bayana nan akwai wadanda za a samu alamun korona ce ta yi ajalinsu.

Aikin kwamitin dai ya shafi bincike da kuma tantace ainihin matsalolin karuwar mace-mace da dubawa ko akwai alaka da annoba.
Yawan mace-macen da ake samu a kusan daukacin unguwannin birnin Kano ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin al'ummar jihar da ma makwabtan jihohi musamman na arewaci.
Rashin sanin musabbabin mace-macen shi ne ya fi daga wa al'umma hankali, lokacin da ake tsaka da fama da annobar korona.
Wasu jihohin masu makota da aka samu masu dauke da cutar na cewa daga Kano aka shiga da ita jihar tasu.
Kano dai ita ce babbar cibiyar kasuwanci a arewacin kasar inda har daga yankin Afirka ta Yamma ake zuwa birnin domin kasuwanci, kuma dumbin mutane ne daga fadin Najeriya suke shiga suna fita kullum don harkokin saye da sayarwa.











