Coronavirus: Duniya ka iya tsunduma cikin yunwa saboda annobar - UN

Ma'aikata na jera buhun fulawa a cibiyar raba abinci ta hukumar abinci ta duniya dake Sanaa a Yemen, a ranar 11 ga watan Fabirairu a 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Miliyoyin mutane a fadin duniya sun dogara ne kacokan kan kungiyoyi masu ba da agajin abinci wajen rayuwa

Duniya na cikin hadarin fadawa cikin matsanancin farin abinci saboda annobar korona, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaban shirin raba abinci na Hukumar Abinci Ta Duniya David Beasley, ya ce akwai bukatar daukar matakin gaggawa don kaucewa wannan mummunan yanayi.

Wani rahoto da Hukumar ta fitar ya ce, adadin mutanen da ke fama da yunwa a duniya kan iya karuwa daga miliyan 135 zuwa miliyan 250.

Yawancin wadannan mutanen suna rayuwa ne a kasashen 10 da suka fi fama da rikice-rikice da matsalar tattalin arziki da kuma matsalar gurbatar sauyin yanayi.

Wani rahoto da hukumar ta fitar na watanni hudun karshe na bara kan matsalar abinci a duniya ya yi nuni da cewa, kasashen Yemen da Jamhuriyarar Dimokradiyyar Congo da Afghanistan da Venezuela da Ethiopia da Sudan Ta Kudu da Sudan da Syria da Najeriya da kuma Haiti suna cikin barazanar.

A Sudan Ta Kudu, kaso 61 cikin 100 na adadin 'yan kasar sun yi fama da matsalar abinci a bara, in ji rahoton.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Tun kafin wannan annobar ma, wani bangare na Gabashin Afrika da Kudancin Asiya dama na fama da matsalar karancin abinci da kuma fari wanda matsalar farin dango ke janyo musu na sama da gomman shekaru.

Da yake bayani ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta bidiyo, Mista Beasley ya ce ya kamata duniya ta dauki matakin gaggawa kan wannan annoba".

"Za mu iya fuskantar ninkuwar fari nan da watanni masu zuwa, ya ce. "Kuma gaskiyar magana babu da lokacin shiri."

A wani kiran daukar matakin gaggawa da yayi ya kara da cewa: "Na yi imanin muna da kwararru da kuma abokan huldar da muke aiki tare, za mu iya hada karfi wuri daya domin ganin cutar ba ta haifarwa da duniya da matsalar abinci ba."

Presentational grey line

A reality check

Analysis box by Lyse Doucet, chief international correspondent

Babban jami'in hukumar wanda ya warke daga cutar, ya fara wannan tattaunawar ne da cewa "ku yi min afuwa saboda magana gaba-gadi."

Babu wani boye-baye game da abin da duniya ke fuskanta - tun kafin wannan matsalar lafiya da duniya ta fada - David Beasley ya sha kiran wannan yanayin mummunan halin da dan adam ya fada tun bayan yakin duniya na biyu.

A wata tattaunawa, ya bayyana fargabar kan cewa mutum miliyan 30 ko sama da haka kan iya mutuwa nan da 'yan watanni, matukar Majalisar Dinkin Duniya bata samar da karin kudade ba a bangaren abinci.

Su ma yanzu masu ba da tallafin na fama da matsalar ta su cutar koronan a yankunansu.

Mista Beasley ya ce babu wanda ya ce za su juyawa masu karamin karfi baya. Amma duk sun amince akwai bukatar su ajje kayan abinci a gidajensu farko. Ya kuma yi gargadin cewa za a iya yada jita jita kan hakan.

A gargadin da ya yi: "Ko ta wanne yanayi sai duniya ta biya wannan bashin." Yana da kyau a hada hannu ayi aiki tare akan abin da yake na gaskiya, ba tare da wani jin tsoro ba.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Wani babban masanin tattalin arziki na Hukumar Abincin yace, Matsalar tattalin arzikin da duniya za ta fuskanta za ta shafi miliyoyin mutane "Wadanda dama tuni suna fama da barazanar rayuwa".

"Wannan wani mummunan yanayi ne da zai ritsa miliyoyin mutane wadanda suke rayuwar hannu baka hannu kwarya," Kamar yadda yace.

"Dama tuni dokar hana kulle da tabarbarewar tattalin arziki a duniya ta lallata shirinsu.

''Abu daya da ya kara girgiza yanayin shi ne cutar korona- wadda ke kokarin kai su bango. Don haka dole mu hada hannu don rage bazaranar da tattalin arzikin duniya zai iya fadawa.''

A farkon wannan watan, Shirin abinci na majalisar dinkin duniya ya shirya raba aikin ba da agaji a yankunan da ke fama da yaki a Yemen, inda ke karkashin ikon mayakan Houthi saboda matsalar kudi.

Tuni wasu masu aikin ba da agajin suka dakatar da ayyukansu, bayan nuna damuwa da suka yi kan yadda mayakan ke kawo tsaiko ga ayyukansu.

Shirin na ciyar da mutane miliyan 12 a Yemen a wata, kashi 80 cikin 100 kuma na cikin yankin da mayakan Houthin ke iko da shi.

Yemen ta samu bullar cutar korona ta farko a farkon wannan watan, yayin da kungiyoyin ba da agaji suka yi gargadin cewa cutar za ta iya yaduwa cikin gaggawa saboda raunin da tsarin kiwon lafiya ke da shi a kasar.

Wannan layi ne