Nigeria: Wasu fursunoni sun shiga hannu

Asalin hoton, Getty
Kwanaki uku da wasu 'yan bindiga suka balle gidan kurkuku na Tunga a Minna, jihar Niger, a Najeriya, an sake cafke 108 daga cikin fursunonin da suka tsere.
Shugaban hukumar gidajen yari a kasar, Dr. Peter Ekpendu ya ce an cafke fursunonin ne da taimakon jami'an soji da na leken asiri da kuma makwaftan al'ummomi.
Ya ce har yanzu ba a kai ga samun sauran 166 daga cikin su 207 da suka tsere ba.
Dokta Ekpendu ya ce daman wasu 49 da ke gidan yarin ba su tsere ba.
Kawo yanzu ba kungiyar da ta dauki alhakin fasa gidan sarkar na Tunga a Minna, kuma an kawar da yuwuwar hannun 'yan Boko Haram a aikin.
Amma an dora alhakin fasa gidajen yarin Ekiti da na Koton Karfe a jihar Kogi akan 'yan Boko Haram din.






