'Yan arewa sun nuna damuwa kan tsaro

A Najeriya, wasu 'yan arewacin kasar na nuna damuwa a bisa halin tabarbarewar tsaron da yankin ke ciki.
Inda dattawan ke ganin ya kamata a hada kai don ceto yankin daga matsalolin rashin tsaron da ya shiga.
Sun bayyana hakan ne yayin bikin bude wani sabon ofishin gidauniyar Ahmadu Bello a Kaduna.
Kashe-kashen rayukan al'umma da yawaitar hare-haren kungiyar Boko Haram na daga cikin abubuwan da ke ci wa 'yan arewacin Najeriyar tuwo a kwarya.







