Gwamnati za ta kara tsaro a makarantu

Hukumomi a Najeriya sun ce za su kara daukar matakan kare makarantun kasar daga hare-hare.
Ministan ilimin kasar Malam Ibrahim Shekarau ne ya bayyana haka a ziyarar jaje da ya jogaranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Kano.
Ziyarar ta biyo bayan hare-haren da aka kai ranar Larabar da ta wuce, a kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya da ke Kano.
Wasu dalibai a jihar sun bayyana cewa akwai bukatar a dauki kwararan matakan kariya ga makarantu.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da aka kai hari a kan wata makaranta a jihar ta Kano.







