Likitoci sun nemi a dage komawa makaranta

Asalin hoton, BBC World Service
A Nijeriya, kungiyar Likitocin Kasar ta yi watsi da matsayin da ma'aikatar ilmi ta kasa ta dauka na sanya ranar 22 ga watan Satumba a matsayin ranar da za'a sake bude makarantu.
Kungiyar ta nemi a dage komawa makarantun a fadin Kasar har zuwa karshen shekara ko ma sabuwar shekara a wani mataki na kaucewa yaduwar cutar ebola a kasar.
Kungiyar Likitocin ta yi zargin cewa an sanya siyasa cikin lamarin domin a ganin ta bai kamata a koma karatu ba har sai an tabbatar da cewa babu sauran mai dauke da kwayar cutar a Nijeriyar.
Dr. Sharfudden Mashi shine shugaban kungiyar Likitocin reshen jihar Kano, kuma a hirar su da BBC ya bayyana cewar manyan jami'an ilimi na jihohi da suka yanke wannan shawarar da Ministan ilimin Nieriya, duka mutane ne da aka nada a kan mukamansu, don haka dole ne su taka rawa yadda ake so.







