Rufewa
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 09/01/2026
Daga Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage
Karshen rahotannin kenan a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Jami'an diflomasiyya na Amurka sun tafi Caracas, babban birnin Venezuela, domin duba yiwuwar sake buɗe ofishin jakadancinsu, a dai dai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan kama Shugaba Maduro da Amurka ta yi a karshen makon da ya gabata.
Mista Maduro ya yanke alaƙa da Amurka a 2019.
Sabuwar gwamnatin riƙo a Venezuela ta ce ta soma tattaunawa kan yiwuwar sabunta alaƙar.
A gefe guda kuma Amurka ta sake ƙwace wani jirgin ruwan dakon mai a yankin Carribean da ake zargin na ɗauke da mai daga Venezuela.
Jirgin mai suna the Olina, shi ne jirgi na biyar da Amurka ta ƙwace cikin makonnin baya bayan-nan.

Asalin hoton, Reuters
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane fiye da miliyan 21 na tsananin buƙatar abinci a faɗin Sudan.
A yayin da aka cika kwana dubu ana gwabza yaƙi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF, ƙungiyoyin agaji na gargaɗin cewa miliyoyin ƴara na cikin barazanar faɗawa tsananin yanayi na rashin abinci mai gina jiki.
A wasu yankunan, ana bai wa yaro ɗaya da ke fama da tsananin yunwa kulawa duk miniti shida.
Baya ga rashin isasshen abinci, ana kuma yawaitar samun cin zarafi ta hanyar lalata, da musgunawa musamman kan mata da ƴanmata a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.

Asalin hoton, Handout
Dakarun juyin-juya hali na Iran sun shaida wa masu zanga zanga a kasar cewa ba za su lamunci tashin hankalin da ake samu a yanzu ba.
Ana ganin wannan gargaɗin zai iya alamta cewa za a ɗauki tsauraran matakai kan zanga-zangar da aka shafe kusan makonni biyu ana yi.
Katse intanet da aka yi a ƙasar na nufin ba a samun labarai sosai da suka fito a yau, duk da dai wasu labaran da aka samu sun nuna ana ci gaba da zanga-zangar.
Kafar yaɗa labaran ƙasar ta gargaɗi iyaye kan su daina barin ƴaƴansu na shiga zanga-zangar, wadda dubun dubatar mutane ke yi.
Jagoran addini na ƙasar Ayatollah Ali Khamenei ya ce masu zanga-zangar kawai ɓata gari ne, kuma hukumomi ba za su zura musu ido ba.

Asalin hoton, Peter Obi/X
Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a karkashin jam'iyyar Labour, Datti Baba-Ahmed, ya ce za su sake tarbar Peter Obi idan ya koma jam'iyyar bayan rasa tikitin taƙarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC.
Datti ya bayyyana haka ne ranar Juma'a yayin tattaunawa a shirin The Morning Brief na gidan talabijin na Channels, inda ya ce zai fi kyau Obi ya koma jam'iyyar da ya yi wa taƙarar shugaban ƙasa a 2023.
"Na faɗa cewa idan Obi bai samu tikiti a ADC ba, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake maraɓtarsa idan ya dawo Labour Party," in ji Datti.
"Zan tsaya tsayin daka wajen ganin babu wanda zai yi wa Obi abu mara kyau.
Kalamansa na zuwa ne bayan Obi ya sanar da komawa haɗakar African Democratic Congress, shekara uku bayan sun yi taƙarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar Labour.
Datti ya ce yana alfahari kan abin da suka cimma tare da Obi.
Ya kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa yana shirin fita daga Labour Party, inda ya ce labarin kanzon ƙurege ne.

Asalin hoton, Reuters
Rasha ta harba wani makami mai linzami mai karfin gaske birnin Lviv da ke yammacin Ukraine, a cikin jerin hare-hare ta sama da ta yi a ƙasar cikin daren jiya.
An kai hare-haren a birane da dama, duk da dai an kaƙƙaɓo wasu makaman bayan samun gargaɗin ana shirya kai harin.
Ukraine ta ce hare-haren da aka kai kusa da yankunan Tarayyar Turai da ƙungiyar NATO babbar barazana ce ga tsaron ƙasashen Turai.
Jamus ta yi Alla-wadai da hare-haren, yayin da babbar jami'ar diflomasiyya ta Tarayyar Turai, Kaja Kallas ta ce hare-haren na nuna lamarin na ci gaba da ta'azzara, kuma ya kasance kamar wani gargaɗi ne.
Aƙalla mutum huɗu ne suka mutu a Kyiv, kuma hare-haren sun shafi ofishin jakadancin Qatar.
Sojojin Siriya sun yi gargaɗin cewa za su sake ƙaddamar da sabbin hare-hare a birnin Aleppo, sa'o'i bayan mayaƙan Ƙurɗawa sun yi watsi da sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
An umarci fararen hula su fice daga yankin Sheikh Maksoud da ke birnin.
An riƙa samun arangama mai zafi cikin makon nan tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan Ƙurɗawa ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar SDF.
Ƙungiyar ta masu tayar da ƙayar baya ta ƙi janyewa daga wuraren da ta mamaye, kamar yadda sharuɗan yarjejeniyar suka tanada.
Ɓangarorin biyu na samun saɓani kan haɗe ƙungiyar mayaƙan cikin dakarun gwamnati.

Asalin hoton, Getty Images/NMDPRA website
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kai ƙarar tsohon shugaban hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da kuma sufurin man fetur ta Najeriya, NMDPR, Farouk Ahmed, gaban EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa.
Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito wata sanarwa daga kamfanin Dangoten, cewa shugaban kamfanin ya shigar da ƙarar Farouk a shalkwatar hukumar ta EFCC.
A baya Dangote ya shigar da ƙarar Forouk gaban hukumar ICPC mai yaƙi da almundahana a Najeriya, domin bincikarsa kan zargin kashe dala miliyan biyar wajen karatun sakandiren ƴaƴansa a ƙasar Switzerland.
Wani abu da ake ganin ya sa Shugaban ƙasar Bola Tinubu sauke shi daga muƙamain nasa.
Sai dai a kwanakin da suka gabata ne Dangote ya janye ƙorafin nasa daga hukumar ICPC, kodayake hukumar ta ce za ta ci gaba da binciken nata.
Sanarwar Dangoten ta ce ta janye ƙorafin daga ICPC ne domin samun damar shigar da sabon ƙorafi gaban hukumar EFCC.
A ƙorafin nasa Dangote ya buƙaci EFCC ta binciki Farouk bisa zargin tafka almundana da amfani da ofis ba bisa ƙa'ida ba, tare da gurfanar da shi a gaban kotu idan aka same shi da laifi.
Za a soma wani gagarumin atisayen sojojin ruwa a Afrika ta kudu a yau Juma'a.
Atisayen - wanda China za ta jagoranta - zai ƙunshin hain gwiwar sojojin ruwan Rasha da Iran.
Afirka ta Kudu na karɓar baƙuncin shirin ne a wani ɓangare na haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙungiyar ƙasashen da tattalin arzikinsu ke bunƙasa wato Brics.
Sun ce za a horar da sojojin ne kan yadda za su kare muhimman hanyoyin sufurin jiragen ruwa da kuma taimaka wa masu tsaron teku.
Masu sharhi na ganin wannan atisayen na iya ƙara raunana alaƙar da ke tsakanin Afirka ta Kudu da Amurka, bayan Trump ya zargi ƙungiyar Brics da yin adawa da manufofin Amurka.

Asalin hoton, Wike Nyesom
Ƙungiyar matasan al'ummar ƙabilar Ijaw ta yi kira da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sauke Nyesom Wike daga ministan Abuja.
Shugaban ƙungiyar, Alaye Theophilus ne ya bayyana kiran yayin wani jawabi da yake yi wa manema labarai a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Mista Theophilus ya kuma yi allah wadai game da yunƙurin ƴan majalisar dokokin jihar na tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
Shugaban ƙungiyar ya ce matakin ya saɓa wa muradun al'ummar jihar mai dimbin razikin man fetur.
A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar ta sake ƙaddamar da yunkurin tsige gwamnan.
Ba wannan ne karo na farko da ake kiran sauke Wike daga muƙaminsa ba.
Ko a yan kwanakin nan ma sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, ya yi kira ga ministan da ya ajiye muƙaminsa, sakamakon zarginsa da yin katsalandan a harkokin jam'iyyar APC a jihar Rivers
Rahotonni sun ce dakarun Amurka sun sake kama wani jirgin ruwan dakon mai a kusa da gabar tekun Venezuela.
Wani kamfanin kula da sufurin ruwa ya ce jirgin ya yi yunƙurin bi ta wani wuri da rundunar sojin ruwan Amurka ta killace a yankin Venezuela.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Rasha ta bayar da rahoton cewa Amurka ta saki ma'aikatan jirgin manta biyu da ta kama ranar Laraba a gaɓar Tekun Atalantika.
A baya Amurka ta ce ma'aikatan jirgin za su fuskanci tuhuma.
Kawo yanzu ba a san adadin sauran ma'aikatan jirgin da kuma ƙasashensu ba.

Asalin hoton, EPA
Jagoran addinin Iran, Ayatolla Ali Khamenei, ya ce gwamnatin ƙasar ba za ta faɗi ba sakamakon zanga-zanga mafi muni da ake gani a ƙasar cikin shekara 15.
Yayin da yake jawabi a bainar jama'a karon farko tun bayan ɓarkewar zanga-zangar kusan mako biyu da suka gabata, Khamenei ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci mutane su riƙa aiki a matsayin sojojin hayar ƴan ƙasashen waje ba.
Dubban mutanen ne ke kiraye-kirayen tumɓuke gwamnatinsa.
Tuni hukumomin ƙasar suka katse hanyoyin sadarwa a kusan duka faɗin ƙasar.
Shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar kai mummunan hari kan jagororin ƙasar idan suka kashe masu zanga-zanga.
A nata ɓangare ƙasar Faransa ta yi kira ga hukumomin Iran su kauce wa cuzguna wa masu zanga-zangar.
Zanga-zangar ta janyo an soke jirage daga Turkiya da Dubai zuwa Tehran.

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar LP a Najeriya, Datti Baba-Ahmed ya ce lokaci ya yi da za a bai wa sabbin jini dama a siyasar Najeriya.
Cikin wani bidiyon hirarsa da gidan Talbijin na Channels a ƙasar, Datti ya ce tun lokacin da yake yi wa ƙasa hidima (NYSC) Atiku Abubakar ke faman tsayawa takarar shugabancin ƙasa.
''Haka aka zo shekarar 2018 muka shiga zaɓen fitar da gwani tare da shi, haka ma a 2023 muka sake tsayawa takara da shi lokacin ni a matsayin mataimakin shugaban ƙasa'', in ji shi.
''Kuma saboda Allah a sake yin haka a 2027?, akwai buƙatar bai wa sabbin jini damar gwada tasu sa'ar'', kamar yadda ya bayyana.
Datti Baba-Ahmed ya ce akwai matasa sabbin jini masu zummar kawo gyara a siyasar ƙasar, amma yadda aka sanya tsarin zama mai wahala da tsauri na yi musu tarnaƙi.

Shugaban Ƙasar Colombia, Gustavo Petro, ya shaida wa BBC cewa ya yi ammanar cewa Ƙasarsa na fuskantar barazanar harin soji daga Amurka.
Kalaman nasa na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da shugaba Trump ya ce kai wa Columbiya farmakin sojoji abu ne da zai haifar da kyakyawan sakamako.
A baya dai shugabannin biyu sun yi ta musayar kalaman ɓatanci tsakaninsu.
Sai dai sun yi magana a ranar Larabar data gabat inda suka shirya wani taro a Fadar White House.
A makon da ya gabata ne Amurkan ta kai wa Venezuela hari tare kuma da kama shugaban ƙasar Nicolas Maduro da mai ɗakinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Za a yi gumurzun wasan hamayyar ƙungiyoyin Sifaniya da ake yi wa laƙabi da El-Clasico tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙasar biyu, Real Madrid da Barcelona ranar Lahadi mai zuwa a ƙasar Saudiyya.
Ƙungiyoyin za su kara ne a wasan ƙarshe na Spanish Super Cup a filin wasa na King Abdullah da ke birnin Riyadh.
Madrid ta kai matakin ne bayan doke abokiyar hamayyarta a birnin Madrid, Atletico Madrid da ci 2-1 a ranar Alhamis da maraice.
Yayin da ita kuwa Barcelona ta kai matakain bayan doke Athletic Bilbao 5-0 a ranar Laraba.
Wannan ce karawar hamayya ta farko tsakanin manyan ƙungiyoyin na Sifaniya a shekarar 2026.

Asalin hoton, Siminalayi Fubara/X
Jam'iyyar APC reshen jihar Rivers ta yi fatali da yunƙurin tsige gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar ke shirin yi.
Cikin wata sanarwa da APC ta fitar ta ce duk da cewa tana girmama cin gashin kan majalaisar dokoki, amma ba za ta amince da yunƙurin tsige gwamnan ba.
A ranar Alhamis ne majalisar dokokin jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ƙaddamar da yunƙurin sake tsige gwamnan da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, saboda zarginsu da laifukan da suka saɓa ƙa'idar aiki.
Jam'iyyar APC da ke mulkin jihar ta bayyana shirin da yunƙurin ''tayar da hargisti'' a jihar.
APC ta kuma yi kira ga mambobin majalisar dokokin jihar su kauce wa duk wani yunƙuri da zai jefa jihar cikin rikicin siyasa.
A watan da ya gabata ne dai Gwamna Fubara ya koma APC bayan ficewarsa daga PDP.
Tun bayan zaɓen 2023, jihar - mai arzikin man fetur - ta faɗa rikicin siyasa sakamakon saɓanin da gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya samu da ministan Abuja, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Nysome Wike.
Ricikin ya ci gaba da ƙamari, lamarin da ya kai ga shugaban ƙasar, Bola Tinubu ayyana dokar ta-ɓaci a jihar tare da dakatar da Gwamnan Fubara har na tsawon wata shida a shekarar da ta gabata.
Guguwar tarzoma na ci gaba da ƙamari a ƙasar Iran , yayin da aka shiga kwana na 13 a jere.
Yanzu ana kallon tarzomar a matsayin tashin hankali mafi girma tun bayan tashe-tashen hankula 2009.
Hukumomin ƙasar sun katse intanet tare da yanke hanyoyin sadarwa ta wayar tarho.
Haka kuma Jami’an tsaro sun harba bindiga da kuma hayaƙi mai sa hawaye a kan wasu zanga-zangar.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar riƙe da kwallaye da ke ɗauke da saƙon nuna goyon baya ga tsohon Yerima mai jiran gado da ke gudun hijira, Reza Pahlavi.

Asalin hoton, EPA
Ƙasar Rasha ta sake yi wa Ukraine luguden hare-haren da manyan makamai a ciki dare.
Magajin garin Kyiv, Vitali Klitschko ya ce an kai wa gundumomi da dama na birnin hare-haren bama-bamai.
Mista Klitschko ya kuma ce harin ya shafi gidaje da wata cibiyar kasuwanci da kuma wani asibiti.
Magajin garin ya ƙara da cewa an kashe mutum huɗu, sannan wasu 19 suka jikkata.
A halin da ake ciki, hukumomi a yankin Lviv da ke yamacin ƙasar sun ce an lalata muhimman ababen more rayuwa a can.
Sai dai ba su fayyace ko mene ne ba.
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.
Ku kasance tare da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa