Ebola: AU na so a cire haramcin tafiye-tafiye

Asalin hoton, AFP
Kungiyar tarayyar Afrika ta yi kira da a cire haramcin da aka sanya game da tafiye-tafiye zuwa kasashen da ke fama da cutar Ebola.
A wani taron gaggawa da kungiyar ta yi a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, kungiyar ta ce haramcin zai iya janyo tsangwama ga masu fama da cutar da kuma kasashensu.
Hakan na zuwa ne yayin da Hukumar Lafiya ta duniya ke nuna fargaba game da yiwuwar samun wasu dubban mutanen da za su iya kamuwa da cutar a makonni masu zuwa a yammacin Afrika.
Kungiyar agajin likitoci ta MSF ta ce yawan masu fama da cutar Ebola a Liberia na son ya fi karfinta.







