Ebola: Kasashen duniya sun gaza in ji Likitoci

Mutane fiye da 1500 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ebola
Bayanan hoto, Mutane fiye da 1500 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ebola

Shugabar kungiyar Likitoci ta MSF ta fadawa Majalisar dinkin duniya cewa ba' a samun nasara a yakin da ake yi da cutar ebola a yammacin Afirka.

Joann Yu tace shugabannin Kasashen duniya na nuna gazawa wajen magance annobar, wacce ita ce mafi muni a tarihi.

Shugabar tace akwai karancin ma'aikata yanzu haka ,abinda yasa tace wasu cibiyoyin da ake bayarda magani a yanzu, suka koma wuraren da marasa lafiyar suke zuwa suna mutuwa.

Mutane fiye da 1,500 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar, kuma kwararru na gargadin cewa wasu dubban mutanen zasu sake kamuwa da kwayar cutar a makonni masu zuwa