An kashe sojojin Amurka a Afghanistan

Asalin hoton, Reuters
Dakarun sojin Amurka sun hallaka wasu takwarorinsu bisa kuskure a kudancin Afghanistan.
Wata majiyar soji ta ce lamarin ya faru ne ranar Litinin lokacin da dakarun Amurka da na Afghanistan ke aikin hadin guiwa a lardin Arghandab da ke Zabul a kokarinsu na fatattakar 'yan Taliban.
Wasu jami'an Afghanistan sun ce an hallaka sojojin Amurka biyar ne da kuma wasu sojojin Afghanistan biyu lokacin da jirgin yakin Amurka ya kai hare-hare a lardin.
Rahotanni sun ce fiye da sojojin kungiyar kawance ta NATO 30 ne suka halaka a Afghanistan a wannan shekarar.






