Boko Haram: Yara na mutuwa a iyakar Kamaru

Tuni dai wasu da suka yi gudun hijira zuwa cikin Kamaru suka shiga makamancin wannan halin.

Asalin hoton, NEMA

Bayanan hoto, Tuni dai wasu da suka yi gudun hijira zuwa cikin Kamaru suka shiga makamancin wannan halin.

Mutanen da ke zaune a yankunan jihar Borno inda kungiyar Boko Haram tafi kai hare-hare sun ce yara na can na mutuwa sakamakon rashin abinci da ruwan sha da kuma magunguna.

Mazauna yankin Kala-Balge da kusa da kan iyaka da Kamaru sun ce akalla jarirai fiye da 20 sun mutu, saboda matsalar da suka shiga ta rashin abinci da magunguna.

''Mata ba ruwan nono, ba ruwa sha a wajen ba komai, babu abinci, abin da ke sa yaran suna mutuwa kenan,'' In ji wani da ke zaune a yankin.

Daruruwan iyalai ne suka shiga gudun hijira zuwa cikin kasar Kamaru, bayan da mayakan Boko Haram suka kona kauyukan da suke zaune a kudancin jihar Borno.