An kashe mutane 40 a kauyukan Borno

Rahotanni daga yankin Ngala na Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya sun ce akalla mutane 40 sun rasa rayukansu a hare-haren da 'yan bindiga suka kai wasu kauyuka uku.

Mazauna yankin sun bada rahoton cewa maharan, a motoci da babura, sun kuma kone daukacin gidajen kauyukan, sun kuma kora dabbobinsu.

Sun kuma ce tun daga misalin karfe uku na asuba aka fara kaddamar da hare-haren.

Wani mazaunin yankin ya gaywa Sashen Hausa na BBC cewa an samu fiye da gawawwakin mutane 40 a kauyukan da aka kaima hari.

Yace: "Muna cikin mummunan hali; ba ruwa, ba abinci, ga kuma gawawwaki."

Har zuwa yanzu dai ba wanda ya dauki alhakin kai hare-haren, amma sun yi shigen irin wadanda 'yan kungiyar Boko Haram su ka kai a sassa dabam dabam na yankin.

A jiya ma an kai wani hari a jihar inda aka kashe Sarkin Gwoza Alhaji Shehu Idriss Timta.

Sarkin ya rasa ransa ne a harin da aka kai wa tawagar sarakunan Askira da Uba da na Gwozan a kan hanyarsu ta zuwa jihar Gombe, domin yin ta'aziyyar Sarkin Gombe.

Jihar Bornon dai -- makwabtanta jihohin Adamawa da Yobe -- na karkashin dokar ta-baci wadda aka saka tun bara domin neman shawo kan matsalar tsaro a yankin.