'Matasa sun kashe 'yan Boko Haram 200'

Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga Najeriya na cewa an kashe wasu da ake zargin 'yan Kungiyar Boko Haram su 200, a garin Rann da ke jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a Karamar hukumar Kala Balge, yayin da 'yan kungiyar kimanin 300 suka kai hari garin da wasu kauyuka da ke kusa a ranar Talata.
Samarin garin da ke taimaka wa jami'an tsaro da ma wasu dakaru sun yiwa maharan kwanton bauna, inda suka kashe 'yan Boko Haram kusan 200 wasu kuma suka samu raunuka.
Rahotanni sun ce matasan sun kwace babura 70 na 'yan Boko Haram kuma sun kwace motoci biyu kirar Hilux an kuma kama wasu daga cikin maharan.
A makon jiya ne 'yan Boko Haram suka kai farmaki Gamboru Ngala makwabciyar Kala Balge, inda suka kashe mutane sama da 300.






