'Yan mata 11 aka sace a kauyukan Gwoza

'Yan matan da suka kubuce daga wajen 'yan Boko Haram
Bayanan hoto, 'Yan matan da suka kubuce daga wajen 'yan Boko Haram

Rahotanni daga jihar Borno na cewar adadin 'yan matan da 'yan Boko Haram suka sace a kauyukan Gwoza ya kai goma sha daya.

Mazauna kauyen Warabe sun tabbatarwa BBC cewar an sace 'yan mata takwas a kauyensu a ranar Lahadi.

Sai dai kuma kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar an sace karin wasu 'yan matan uku a kauyen Wala da ke makwabtaka da Warabe.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta sace 'yan mata 276 a garin Chibok a ranar 14 ga watan Afrilu kuma ya yi barazanar 'sayar da su a kasuwa'.

Jihar Borno ta kasance matattarar 'yan Boko Haram kuma yankin Gwoza na yawan fuskantar hare-hare daga wajen 'yan Boko Haram.

Amurka ta ce za ta taimaka wa Nigeria wajen neman 'yan matan Chibok.

Shugaba Obama ya ce za a tura tawaga, da ta kunshi sojoji da jami'an tsaro da kuma jami'an wasu hukomomi wadanda za su yi kokarin gano takamammen wurin da aka ajiye 'yan matan.