An kashe mutane 11 a yankin Wukari

Asalin hoton, AFP

An kashe kimanin mutane 11 a wani sabon rikicin da ya barke a Jihar Taraba dake arewacin Najeriya.

Rahotanni sun ce rikicin, mai nasaba da kabilanci da addini, ya tashi ne a garin Gindin-Dorawa dake karamar hukumar Wukari a cikin dare Asabar.

Mazauna yankin sun ce ana fada ne tsakanin Jukunawa a bangare guda da kuma Hausawa da Fulani da wasu kabilun a dayan bangaren.

Sun ce rikicin ya raba dimbin mutane da muhallansu -- abinda ya tilasta masu neman mafaka a wasu wuraren cikin jihar, wadanda su hada da Jalingo, babban birnin jihar, da kuma Gassol.

Wani mazaunin garin, Hassan Yakubu, ya ce an yi asara matuka a tashin hankalin.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Joseph Kwaji, ya tabbatar da barkewar rikicin, amma ya ce ba ya da cikakken bayani kan musabbabinsa da kuma ta'adin da aka yi.

Bisa dukkan alamu dai tashin hankalin na Jihar Taraba, wanda rahotanni ke cewa ya samo asali ne daga rikicin makiyaya da manoma a Jihar Benue mai makotaka, na ci gaba da bazuwa.

An dai dade ana rikici a yankin na Wukari, inda aka samu asarar rayuka da dama da dukiyar jama'a.