Mutane da dama sun rasa rayukansu a Wukarin Taraba

Tsaro a Najeriya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Jami'an tsaro a Nigeria

Rahotanni daga jihar Taraba a arewa maso gabashin Nijeriya na cewa akalla mutane goma sha biyar sun rasa rayukansu a wani tashin hankali a karamar hukumar Wukari.

Bayanai na nuna cewa kimanin mutane takwas ne suka rasa rayukansu a wani kauye da ake kira Nwunkyo-Kura, yayin da a cikin garin Wukari kuma mutane bakwai suka rasa rayukansu a wani lamari mai kama da martani ga harin da aka kai tun farko a kauyen.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce tuni aka tura jami’an tsaro domin maido da doka da oda.