Rikici tsakanin Hausawa da Jukun a Taraba

Asalin hoton, BBC World Service
Rahotanni daga Jihar Taraba dake arewacin Nigeria sun nuna cewar an yi tashin hankali tsakanin kabilar Jukun da Hausawa a kauyen Jubu dake karamar hukumar Wukari.
Rahotannin da muka samu sun nuna cewa a safiyar ranar Talata ne, aka samu tashin hankalin amma babu cikakkun bayanai game da rikicin.
Kabilar Jukun da ta Hausawa sun dade suna zaman tankiya a tsakaninsu, inda a wasu lokutan rikici tsakaninsu kan janyo hasarar rayuka.
Kawo yanzu jami'an tsaro ba su yi wani karin haske ba game da rikicin na kauyen Jubu.







