Jonathan ya yi jawabi a London

Shugaban Nigeria, wanda rashin lafiya ya kama shi, ya gabatar da jawabi a wajen taron saka jari a Nigeria a London.
Sai dai sabanin yadda shugabannin da suka bude taron ke wuni a wajen taron, Mista Jonathan bai wuce awa da ya rabi a wajen taron ba.
Ministan harkokin wajen kasar, Dr Nuruddin Muhammad, ya shaidawa BBC cewa shugaban kasar ya samu sauki, sai dai abin da ba a rasa ba na murmurewa.
Jami'an gwamnatin Nigeria da suka gabatar da jawabai a wajen taron sun ce suna daukar matakai daban-daban wajen ganin sun inganta harkar zuba jari a kasar.
Shugaban Najeriyar ne, Goodluck Jonathan, dai ya kamata ya bude taron a jiya amma saboda bai ji dadin jikinsa ba, ya kasa halarta. Likitoci a London sun ba shi shawarar ya dan huta tukuna.







