Za a yi bincike a Damascus

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kiran a gudanar da kwakkwaran bincike game da zargin yin amfani da makamai masu guba a wajen garin babban birnin Syria wato Damascus a jiya laraba.
Gwamnatin Syria da mayakan 'yan tawaye sun zargi juna kan harin.
Wakilin BBC ya ce Rasha da China sun kankane batun kalaman da kwamitin sulhu na majalisar Dinkin Duniya ya yi.
Na kiran Damascus ta ba wa masu binciken makamai masu guba da suke kasar damar shiga ko'ina dan gudanar da bincike.







